20

389 30 5
                                    


  Lokacin da su ka isa gidan sun iske Mamma na can side in Alhaji. Saboda haka sai suka zauna kawai abin su suna hdimomin su. Sai da Mamman ta Kira su tace su same ta nan side in nashi sannan su ka wuce.

Areef na hango Alhaji ya fara Mika mishi hannu har da kokarin yin tsalle shi a dole yana son yaje wurin shi. "Kai wannan zakwadin fa Areef" Nabila da ke hannun ta, ta fada tana kokarin Mika ma Alhaji shi.

"Zo nan takwara na kaji, yaro ya San takwaran shi" da sauri ya makale a jikin Alhajin Sai kace wani Wanda za a kwace. Duk dariya su kayi, sannan su ka gaisa ana dan raha.

"Wannan kanin naki dai sai anyi da gaske. Nace an bada yarinya amma Sai roko na yake, ni na rasa me yake nema Kuma. So yake in hana waccan auren Sai kace nine mahaifin ta" Alhaji ke maganan yana kallon Salma. Murmushi tayi domin ita ma dai rigiman da suka gama yi da Bilal in kenan.

"To ko kaine mahaifin ta ai ba a neman cikin nema ko. Haram ne Allah ya hana. Ni na rasa saurin me Bilal yake, duka nawa ma yake" Mamma ta fada ranta a dan bace, daman tunda aka fara maganan ba wai son zancen take ba Sam.

"Aa ni ban ga laifin auren wurin ba. Tunda yaro ya nema ai akwai fa'idan shi nayi hakan. Ba gwara auren ba akan yaje ya fada neman matan banza" Alhaji ya amsa. Ita dai Salma tayi shiru ne kawai. Amma ta San dan uwan ta, abinda duk basu fahimta ba, ba wai auren bane ke shaking in shi. Aa, Layusan ce bai son ya rasa. She understands him shekarun da suka yi suna tare dole rashin shi ya firgita shi.

"Kilan ba alkhairin shi bace Kuma, shiyasa hakan ya faru" Anty Salman ta fada kawai. Alhaji ya amsa da "Tabbas hakane Kam. Ya nemo wata kawai, ko in baida shi mu Sai mu nemo mishi tunda da dai yana son auren, gwara a mishi kawai. Mu rufa ma kanmu asiri" Alhaji ya sake fada.

Anty Salma dai ganin ana Shirin ballo ma kanin ta ruwa yasa tayi saurin bude baki "Alhaji Bilal fa ba wai aure ne yake so ba, daman saboda yarinyar ne sun dade suna tare. Jin an Fara zancen auren ta shiyasa yace a nema mishi itan. Amma tunda hakan bai yiwu ba, Ina ganin kawai a barshi don kanshi zai nemo watan ai, in ya tashi" Hararan ta taga Mamma nayi.

"To Uwar tsari. Laifi ne dan an mishi samo mishi watan? Ko da yake zamanin ma gwara ma kowa ya nemo tashin yafi maka kaima kwanciyar hankali" Salma dai ba tace komai, jin ta hau ta Kuma sauka ita daya dai.

"Allah ya kyauta, na nemi Bilal inji dai. Amma wancan Kam, ki gaya mishi ya hakura ya daina maganan ta. Ya bar yarinya tayi auren ta, don iyayen ma sunce ta tada musu hankali. Allah ya zaba ma kowa mafi alkhairi" duk suka ce Amin.

Sai lokacin Alhaji ya juya ya ga Nabila da ke can gefe tana danne dannen ta, ba ta ma San me suke tattaunawa ba.

"Ni Nabila wani School zata ne?"

Nabilan ta juya. Mamma ce ta bashi amsan yanda su kayi da Abbah. Ba ta ma sani ba ashe ta neme shi akan zancen. "Ni dai gsky nace mishi a bar maganan KASU in nan kawai, wahala kawai za ta Sha. Inma ba ta son wajen ga Universities inmu a nan, ga Nile ga baze gasu Alhikmah duk. Ko Kuma Maryam Abacha na Niger duk ana karatu dai"

"Ke dai kin fi son Private University naga alaman" Alhaji ya fada, tayi nodding kanta "Matsalan strike nake guje mata gsky. Ga sauki gwara kawai a bishi" girgiza Kai yayi "Gskyn ki Kam, kasan mu dai ta zama abinda ta zama. Sai a Fara applying don Ina jin Baze sun bude admission"

Mamma ne ta juya tana kallon Nabila "Kina son baze?" Ta bukata. Nabila kuwa ji tayi kaman ta zuba ihu, gsky tana son komawa gidan su. Tana son zama da mamin ta, duk da dai tasan zasu rabun Amma ba ta son ace ta bar gidan su hakanan. Ga Amina da sauran kannen ta.

"Eh Ina so" ta fada a hankali ba wai don ya Kai har zuciyan ta ba.

"Sai a nema kawai" Alhajin ya fada.

Zuciya Da Gwanin TaWhere stories live. Discover now