S💞: "Thank for the warmth of comfort angel, it better than any blanket i've ever used. I feel pleasured. Ina son ki Nabilata" Even though she is still confuse, Sai lokacin taji wani irin murmushi ya bayyana a fuskan ta. Daya daga cikin abinda ya sa take son Sadeeq, he always confess his feeling for her. Ko dayaushe, kokari yake ya gaya Mata Yana son ta. Hakan na sawa, ko tana cikin rudu ta ji hankalin ta ya kwanta.
Tana cikin mota zata koma gida ne daman ya tura Mata mssg in. Ba dai ta Mai reply ba Amma Kuma ba ta da wani tunani a ranta in ba shi in ba. Ya Mata dumu dumu a zuci, Kai hatta numfashin ta, tana jin da kalman sunan shi a ranta yake tafiya. Komai take, shine a ranta. Murmushin ta kayatacce, tunanin shi je ke sawa. Har wani irin kallo na daban ta ke ma mutane, in dai Sadeeq na ranta. Kai hatta yanayin tafiyan ta canjawa yake. Tana tafiya wani lokacin, tana magana ita kadai. It like she is becoming mad in that love. Bakuwan soyayyan da ke samun katon fage Mai kyau a rayuwan ta. Sadeeq ya fara canja ta, domin yanzu koman ta kawai, shine a ciki.
"Ba kiji nane?" Sai lokacin ta dago kanta ashe driver in nata faman Mata magana.
"Au yi Hakuri Dan Allah"
"Lafiya dai ko?" Ya fada yana kallon yanayin ta. Gyade kai kawai tayi, tana kallon shi tunda tasan magana zai Mata.
"Hajiya tace in kai ki gidan Maman Areef. Sun tafi Lagos da Alhaji, Sai zuwa Jibi ko gata zasu dawo" rasa Mai zata yi, tayi. Amma tabbas tana cikin tsan tsan murna da farin ciki.
"To bara na debi kayana a gida" toh yace Mata ta cigaba da driving, tasan Anty Salman ba ta sani ba. So ita ma bata gaya Mata ba, saboda tana son tayi surprising inta.
Zainab dai ta tura ma text, akan tana nan zuwa gidan su Washegari, tayi Missing Zee in kwana biyu ba ta leko ta ba.
Kaman baza ta tura mishi text ba, Sai Kuma taji ba zata iya share shi inba. Don haka, dole ta daure ta mishi sending.
"Mamma is not in town, I will be in Gwarimpa"
Shiga tayi ta debo kayan nata da dan yawa, don tana son in da hali su roki Mamman ta dan barta tayi ko da one week ne. Tana hanya tafiya Gwarimpan ne, taga Sms in shi ya shigo.
S💞: "Such a good new! Can i see you please?" Tasan daman da wuya in bai bukaci hakan ba. Sai dai kuma ba ta fada mishi bane dan yazo, kawai she is use to telling him things, kusan dukkan abinda ke faruwa presently a rayuwan ta, he knows. Ya dai kwace ma Zainab position inta, don da da ita take yawan messages in nan. Yanzu ma su kanyi, Amma ba Kaman da shi in ba.
"Not today" tayi replying back. Shi inma bai yi complaining ba. At least, he got more than enough da zai yi keeping in shi har gaba da goben ma.
Tana sauka a gidan da Baby areef ta Fara cin karo yana jikin Nanny inshi Sai gwaranci yake yi. Ai kuwa Yana ganin ta ya fara yage baki, dake yawan zuwa gidan dasu ke kwana biyu shi da maman shi yasa ya gane ta. Daukan shi tayi tana fadin "Oyoyo baby na" shima har da dariyan shi, irin Wanda ya ke so ta dauke shi, ta karbe shi in nan.
Tana dosa kanta, taci kamshin girki na tashi. To tasan yau Anty Salma an shiga kitchen kenan. A kullum A ake grading inta in dai wurin abinci ne, hakan kuwa yana ba mutane mamaki duba da cewa gidan su cike yake da cooks. Abinda basu gane ba, zaman shiru ya ke sa Salman shiga kitchen in, duk wani cook da za suyi a gidan nan Sai da suka Saba dashi ta yanda ta samu abinda ta dauka gun kowanne, shiyasa ta zama expert dayawa saboda ta tara experience in mutane dayawa. Tunda tayi aure kuwa, Yan uwa da abokanan mijin ta suka fahimce cewa girkin ta bai da na biyu, shikenan ba Sai suka kulla Mata ba. Kullum cikin baki take, tana kitchen tana faman girki. Tun tana mishi complain, yaba fada Mata mutane rahama ne har shi inma abun ya fara fita kanshi. Don haka kawai, in ka ishe su suna ka dan dauke kafa. Sai ya sata dafa abincin Wanda kwata kwata bai da taste, don in aka ba ka fruit ko wani snacks ma dadi zaka ji ka dawo gobe. Har code gare su, in taji yace "The norm" to tasan yana nufin normal abincin da ta iya kenan. Amma in yace Mata "The unique" tasan yana nufin ayi tsiyar kenan, Kuma abincin ko su basa iya ci sai dai su gyara su bayar. Saukin ta ma wai tafiyan su USA, dake nan aikin shi yake.

YOU ARE READING
Zuciya Da Gwanin Ta
RomanceBurin zuciya a ko yaushe shine ta samu gwanin ta. Ko da kuwa hakan zai zama illa a gare ta. To amma in hakan ne kadai ya rage zabi, ya abin kan kasancewa? Ku biyo ni... Ku fito kuji labari zazzafa Kan zuciya da gwanin ta Tsokar da babu irin ta mai s...