15

272 34 4
                                        

Cool music ke tashi a cikin motan yana driving. As usual fingers in hannun su a hada yake. He told her, he feel safe when he does that.

"Me zamu siya ma Anty Salma?" Dan jim tayi kaman tana tunani. Can Kuma ta q wayan ta tayi dialling inta.

"Hello Anty Salma am on my way back"

"Am about to call you hala hiran da Zainab in ne yayi dadi?" Basar da zancen tayi saboda ba ta son yin karya.

"Anty Salma daman Sadeeq ne..." Juyawa tayi tana kallon shi "Ya ke tambayana me zai kawo miki. Ni Kuma na san you are always changing what you crave for, shiyasa i call to ask"

"Allah yar gidan Sadeeq? Muuga... Get me some fruit salad. Yauwa daman yanzu Zan aiki driver na ya siyo min cereal in Areef, ya Kare. Kinsan Wanda yake Sha" Dan pouting lips inta tayi kafin ta Fara complaining "Kai Anty Salma, your siriki is about to come and greet you, Yana tunanin me zai kawo miki. And all you are thinking is your son, ku daman iyayen nan haka kuke"

"Kaniyan ki Nabila, shi Sadeeq in bai San yaro bane? Oya tell him in Yana so ya siya Uwar yaro to ya so dan ta than anything. So in yana so in zama on his side, I need cereal for my baby" dariya tayi, ta kashe wayan. Hade rai tayi tana fadin "Kaji Anty Salman nan fa"

Dariya yayi yace "To daman waya ce Miki ki kirata, wai ni nan Ina shawaran sirri da budurwata. Gashi kin tona Mana asiri" turo bakin ta tayi, irin tayi fushin nan.

A Sahad su ka tsaya. Ai kuwa taga hauka, domin da ya fara diban cereal Sai da ta saki baki. Ya hada da milk da Kuma milky drink in da yasan za a iya ba yara. Daganan suka je ya dauko fruit salad in. Stall in chocolate suka je, kallon ta yayi tayi saurin mishi nodding Kai. Sai Kuma tace "in nayi kiba, you won't like it" dariya yayi yace "Ai inada kayan Gym, I will force you to do it. Yanzu dai let me spoil my girl friend" tana kallo ya kwashi chocolate in nan, ya dauki orange drink carton, probably saboda Wanda ya ga taji dadin shi sosai. Sai yogurt da ice cream, ita dai kallon shi kawai take. A wurin magreeb ya tare su, don haka ya shiga Sallah ita Kuma ta tsaya a mota tana scooping Ice cream inta, chocolate flavor ne, her favorite. Tsaf ta shanye hankalin ta kwance kafin ya dawo.

A hanya ma Sai da ya tsaya ya musu ordering chicken kebab tukunna su ka tafi. "Ita fa Anty Salma ba a siye ta da shopping" ta fada tana daddana wayan ta. Picture ta musu a snap chat duk da ba iya daurawa zata yi ba. Ba ta jin zata iya daura pic in Sadeeq a media, haka kurum asirin ta rufe a tona mata.

"Au abinda Zaki ce kenan?" Ya fada Yana hararan ta cikin wasa.

"Ai gsky ne, naga Sai wani siye siye kake. Just pray she likes you saboda ita in bata son mutum, nothing that person do will change it" da sauri yaja burki "ke karki fada min da gaba mana"

"I mean it" ta fada tana cigaba da dan danne dannen ta.

Suna isa gidan da ta fita, ta Kira mai aikin Anty Salman da Nanny in Areef su zo su shiga da kayan. Ta window in motan ta leko "I hope you are praying" ta fada sounding serious.

"Nabila ni kike ma haka ko? Zan Kama kine" gwalo ta mishi, sannan ta juya da gudu. Ji yayi kaman ya fita ya kamo ta.

Jim kadan Sai ga Nanny in dauke da Areef, wai ance ya shiga wani parlor. Da dai alamu na guests ne kawai. Amsan Areef yayi ya wuce dashi, don haka kawai yake jin Anty Salma ta bashi Satan amsa. Wasa ya dinga yi ma yaron, har aka kawo mishi refreshment hadda kulan Abinci, da kamshin shi kadai ya sa shi jin cewa dole ya ci abincin nan.

Yana cikin wasa da Areef in, yaron na faman washe mishi hakora Sai ga Anty Salman ta shigo. Da murmushi kan fuskan ta take fadin "Aa su boy an samu abinda ake so" jin Areef in nata faman kwashewa da dariya. Cikin natsuwa da girmamawa ya gaishe ta. Duk da dai yasan ba zata wuce mate in shi ba. 26 years haka kenan.

Zuciya Da Gwanin TaOnde histórias criam vida. Descubra agora