8

284 26 9
                                    

"Su kyau manja, ka jira a yabe ka Mana" ta amsa.

"No, gwara inyi appreciating abinda Allah ya bani. Now tell me, meye sa kike tsoron Ummah ta Kai maganan mu wurin su Abbah" dan jim tayi sannan tace.

"No kawai Ina so in Fara school ne, Abbah Yana son makaranta sosai" dariya yayi yace "Ni dai banyi Kama da Wanda zai hana ki School ba ai ko? Kuma numban Ummah, ko ba a ban ba nasan yanda zan yi in samu" dariya tayi, sun dade suna waya kafin su kayi Sallama. Daganan hiran ya gangara messages, sun dade suna yi. Sai wani irin murmushi take yi na daban, wani lokacin ma ba wai maganan soyyaya yake Mata ba. Aa, kawai hiran ne da suka Saba yi, Sai dai a ciki yana dan jefo words in da zai nuna Mata, mahimmancin ta a gareshi. Wannan inma, ba sabo bane saboda yanzu ta gane tun da yana amfani dasu.

Kaman in ta fadi wani abu Sai yace "keh bari Mana, Kar ki sa in kasa bacci" ko Kuma "kina so na kasa tashi daga inda nake ko?" Ko "Na kasa cin abinci, duk na fara ramewa ma kuma ke kika ja" ire iren maganganun dai dayawa.

A duk lokacin da suke magana, tsintar kanta take a wani yanayi na daban, Wanda take ji cikin kwanciyar hankali da annashuwa. Sai dai duk da haka, ta kanji sautin bugun zuciyan ta na karuwa. Mostly, daga yanayin yanda yake Mata magana. Komin shi na da irin effect in da yake samarwa a jikin ta. One minute za taji kaman tana tsoro the next taji farin ciki ya Mata yawa, ta rasa inda zata sa kanta. In ko basa magana, ta kan kasance ne cikin tunanin previous conversation insu. Haka nan ita kadai Sai ta tsinci kanta, tana murmushi, ko dariya ma wani lokacin. Ko Kuma ta runtse idanuwan ta, tana tuno wani abu da ya fada Mata. Wani lokaci, har tsalle take Sai tayi Sai ta gane abinda tayi. Ko kuma tana cikin tafiya, ta sa gudu duk da ita kadai. Kama wata mai aljannu. Nan ko duk love effect ne ke haka da ita. Without her realizing, a hankali duk wani kankantan takun shi, da salon shi na kara ruruta girman soyyan shi a cikin zuciyan ta. Ita kanta ba wai ta kan gane hakan bane, all she knows is that, he matters a lot to her. Dan ita kanta yanzu, ta riga tayi sabo da magana dashi ta yanayin da bata iya jure lokaci mai tsawo ba tayi magana dashi ba. Ko bai nema ta ba, zata neme shi. A kullum kwanan duniya, shakuwa Mai girma ke kara shiga tsakanin su.

Shi inma ya gane, kullum da irin progress in da ake samu. Saboda wani time, da gangan zai ki kiranta, don dai kawai yayi testing inta. Tabbas, yasan zata Kira. Kawai, yanayin lokacin da take dauka ka fin ta kiran, ya ke aunawa yaga iya cigaban da aka samu.

Kwanan shi biyar a Taraba ya juyo. Sai a safiyyar ranar Kuma ya ke gaya Mata zai biyo ya ganta kafin ya koma Kano. Sosai taji dadin hakan, Sai dai Kuma sabuwan tension in da hakan ke nufi. Aminiyar ta Zainab ce ma ta Kira ta ranar, ta dan kauda Mata tension in. Har lokacin ba wai ta gaya ma Zainab in abinda ke faruwa tsakanin ta da Abakar Sadiq in tayi ba. Hira ce dai suke yi kawai na school suna dariya. Nan Zainab in ke fada mata ta Kira ta, ta gaya mata an saman Mata admission in karatu a Sudan ne, dan daman tana da burin karantar pharmacy. Abun ya zo Mata as surprise ita ma, kwata kwata ba ta San ana Shirin fitar da ita karatu ba. Nabila kuwa, taji Mata dadi sosai, Sai taji kaman ma ta Kira Abbah ta gaya mishi tana son zuwa can in itama, tunda ya riga da ya bata daman zaban ko ina take so.

"To Sadeeq infa? Kiyi ya dashi?" Zuciyar ta ya tunatar da ita. Sai Kuma lokacin ta gane, a yanzu duk wani decision da zata yi dole zai yi involving in shi a ciki. Yanzu haka da yake maganan ganin Abbah, ta ina zata fara zuwa Sudan karatu? Da wannan thought in ta share maganan Sudan, suka cigaba da hiran su da Zainab.

Maganan Mubarka ma suke yi, da kw suna da kusa da Zainab in a cikin Abuja, so sukan hadu. "Ai baki San me Mubarak ya ce min ba" gyara zama Nabila tayi, tace "Ina sauraron ki" tasan tsaf halin Mubarak, yanzu haka wani shiriritar ya fada, at least tunanin ta kenan dai.

"Kinsan zai tafi China karatun Engineering ai"

"Haka ya fada min" Nabilan ta amsa, dake Mubarak in ya kan dan kirata bayan kwana bi biyu. Sun dai fi chatting a WhatsApp, Sai Kuma comments akan post in juna a su Twitter da IG.

Zuciya Da Gwanin TaOù les histoires vivent. Découvrez maintenant