"Heart" ta Kira cikin wani irin raunanniyar murya. Dagowa yayi yana kallon ta, bakin shi Kam ya rasa Mai zai ce Mata Kuma. Shekara Shidda ai ba wasa ba. Tun yana secondary, bai gama sanin kanshi ba suka hadu da Layusa. Daga zuwa gidan wani friend in shi a Abuja ya ganta, sun zo bikine lokacin suka sauka gidan su Abokin nashi dasu ke da dangantaka.Ba wani magana suka yi ba rana, illa dai wani series da ya iske su, suna kallo. He loves the series, so Sai ya zauna har aka gama Episode in da suke kallo. Daganan aka hau hiran film in. Ita Kuma dake tasan film in sosai, tare suka yi dan labarin. Ya tashi ya tafi. Sai ma bayan kusan wata biyu yana scrolling a IG ya ganta. Bai wai gane ita ince ba, ta dai yi looking familiar. Bai Mata magana va a lokacin Sai daga baya bayan ya gama ganin irin poems in da take rubutawa. Har da videos, he likes them sosai. Don har comment watarana ya kan mata.
Sai ranar tasa abu a status inta akan love and it darkness.
"Who is the guy? We will love to know him" ya Mata replying.
Fuskan dariya ta tura mishi. Ta sa "No one but if there is, I will love to know him also"
"How can you write to Nobody then? All these messages, it weightness all for nothing. Girl you are kidding me, i swear"
Dariya tayi tayi, daga ranar duk randa tasa love poem Sai ya tura mata "Even this one? 🙄" Ko Kuma "i still can't believe you" dariya take, har tana posting a status inta. "Please help me tell this guy am not dating anyone, he find that hard to believe."
Shima Sai ya tura Mata fuskan dariya. Sai ranar da ya tmbyn ta to meyesa take posting love poems, when she is not in love. As in what motivate ba.
"They are just thoughts and imaginations" tayi replying,
"Then i wish your imaginations came true oneday" da sauri ta tura mai Ameen and thanks. Daga lokacin haka su cigaba da dan gaisawa. Sai ranar da tasa pic ubta a status, Rana ya Kara tabbatarwa akwai inda ya santa. Don haka ya tura Mata "Do you know you look familiar, like I know you somewhere"
Dariya tayi tace "Okay oh, maybe in your thoughts"
"Girl, am serious"
"Then post my pic in your status, maybe some of your buddies can help you remember" ita tsokanan shi take. Shi kuwa posting in yayi. Friend in nashi na ganin shi ya Kira ya fada Mai. "No wonder" yace, don yasan dole akwai inda ya santa.
Mssg ya tura mata asking ko tasan wane wane, sunan friend in kenan. Tana mishi reply ta San shi. Yace okay can you remember so so guy, da kuka yi hiran so so series dashi a Unguwa kaza a Abuja.
Da sauri tace "You are the guy? I thought you weren't serious fa"
"Now you know"
Shikenan daganan suka Fara chatting, ba ma a IG kadai ba har Twitter da Snapchat Sai da suka zama friends. A hankali suka saba sosai, har suka yi exchanging contact suna chatting tanan. Suka dawo kullum Sai sunyi chatting, musamman a series in da suke da interest. Abinda ya Kara keeping friendship in nasu Kuma, she is a poet shi Kuma yana painting. Don tun kafin ya fara University ma, ya fara paintings. A zama da yake shi kadai a gida, he comes to love art sosai. Don ko Nabila ya taba bata one of zanen shi during one of her birthday. Ita ya zana tana boye fuska, lokacin tana jin kunyan. Sai kuma Wanda take ma Anty Salma shagwaba.
She loves that paintings duk tasan tsokanan ta yayi, har yanzu tana nan ajiye dasu a Kaduna.
Abinda yayi keeping alakan shi da Layusa. Yawancin in kowa yayi piece of art in shi, they motivate each other sosai. Har yazo in yayi painting inshi ya tura Mata, Sai ya zamo kaman inspiration ne a gare ta. Na irin poem in da zata rubuta. He paints and she get a poem for it ko Kuma the other way round. Sai ya dawo kaman suna aiki a tare ne. Saboda ko a net suna posting abubuwan juna. Duk fans insu sun sansu as friends. A haka har suka Fara waya, ba irin hiran da basu yi. Daga waya Sai ya gangara Vidoe call. Watarana har 3 hours suke suna magana. Things became even more than friendship, kowa ya gane hakan Amma ba Wanda ya fito ya bayyana ma dan uwanshi. But they felt the tension between them.

BINABASA MO ANG
Zuciya Da Gwanin Ta
RomanceBurin zuciya a ko yaushe shine ta samu gwanin ta. Ko da kuwa hakan zai zama illa a gare ta. To amma in hakan ne kadai ya rage zabi, ya abin kan kasancewa? Ku biyo ni... Ku fito kuji labari zazzafa Kan zuciya da gwanin ta Tsokar da babu irin ta mai s...