17

312 24 5
                                    

Duke a gaban mutumin da yake a matsayin mahaifin ta, tana sauraron irin fadan da yake mata duk da dai cikin hankali ya ke Mata "Yanzu ya dace mutane su zo tun daga wani gari Kuma basu samu abinda suka zo nema ba? Ko kuwa so kike mu biya musu nasu bukatun mu Kuma mu zama masu magana biyu? Mu koma mutanen banza kenan?" Shiru tayi don ba zata iya maida ma Mahaifin nata komai ba.

Ita Kam jima take kaman numfashi neman gagaran ta yake yi, don yanzu haka struggling dai daituwan shi take. Ga wani irin zufa dake ketowa daga kowani sashe na jikin ta, hijab in da ke a jikin ta duk ta gama hada gumi.

"Ab-ba-h" muryan ta cracking yake, dga haka tasan ba zata iya maganan ba ma. Ko tayin ma ta riga ta fahimci ba wani tasari zai yi ba. Aikin gama ya riga ya gama. Tashi mutumin yayi Yana kaiwa da kawo a falon. Tunanin shi daya, bai San yanda zai yi da mutanen da zai amshi bakuntar su ba. Mutane manya, shahararru Kuma Wanda ba kasafai mutum ke iya duban su, ya sanar dasu ba zasu samu abinda aka zo neman ba. Bai son yi ma yarinyar abinda bashi take so ba, haka Kuma ba ta yanda za ayi ya zama Mai magana biyu. Kafin ya bada auren ta, tun farko Sai da ya tabbatar da kamala da hankalin Wanda ya ba mawa in da kuma iyayen shi. Ya tabbatar daga gidan mutunci da amana ya fito. Yanzu Kuma kwatsam ta zo mishi da wannan zancen. In yayi haka ma ai ace wani abun ya duba, ba mutunci da dacewa ba. Maganan da ake ma har ranar auren sun gama tsaidawa, to ta ina zancen nan Kuma zai koma baya.

"Kinsan ba ki San Ibrahim in kika turo min shi?" Girgiza Kai tayi hade da share wani Uban zufan. "Abba ce min yayi zai zo ya nemi izinin ka, ni Kuma nace ya zo Mana Ina ruwa na. Wlh ban zaton zai zo in ba, Kuma ban yi zaton za a zartar da hukuncin ba a tuntube ni ba. Ni wlh ba shi nake so ba" Rasa abun cewa Wanda take Kira da Abban yayi. Can yace Mata "shin layusah waya ce miki ana wasa da maganar aure? Tun yaushe yar uwarki ke Miki maganan auren, kinsan akwai Wanda kuke tare shine baki fiddo shi ba? Sai yanzu da mai afkuwa ta riga ta afku?" Magana yake Mata Amma ji take kaman tasa hannu akan ta, ta kurma ihu. Ta Ina za ta Fara yi mishi bayanin dalilin da yasa tuntuni Bilal in bai bayyana kanshi ga iyayen ta ba? Tana son Bilal, soyayyan da bata taba sanin na wani ba bayan nashi. Da shi ta bude Kuma ta sha tunanin akan shi zata rufe. To meyesa sai yanzu abun zai juye Mata haka? Shin meyesa Ibrahim in ya zabi ya mata haka, bayan ya San babu wani abu a tsakanin su banda mutunci. Ko yayi zaton wasa ta ke mishi lokacin da take bashi labarin Bilal in. Za ko ta hadu dashi, da kanshi zai janye batun auren nan. Domin a rayuwa ba zata taba hango kanta da wani ba bayan Bilal in.

"Tashi kije zan neme ki" Abbahn ya fada. Ba wai don ta gamsu ba ta tashi tafi in, a Zuciyan ta tana tunanin mafita.

Bayan fitan ta, numban Ibrahim Abba ya kira dashi da kanin shi Usman Wanda yake da tabbacin ta hanyan shi tasan Ibrahim in.

Ba a wani dade ba kuwa Sai gasu dukkansu biyun. Zama su kayi suka gaishe shi ya dago yana kallon su. "Wai ya abun naku hakane?" Dukkan su biyu ya ma tmbyn, saboda yasan duk abun daya to dole dayan ma ya sani.

"Yaya ni fa abun tashin hankali a nan ba. Tunda an riga ansa rana shi wancan in aika ga ba rabon shi bace. Maganan da ake yi ma ba a kasan nan yake da zama ba. To ga Wanda aka sani, aka yarda dashi aka San asalin shi. Wani abun takaicin ma shekarun su daya fa, ta ina yaro karami zai iya rike mate in shi Dan Allah?" Dakatar dashi yayan nashi yayi "Ba wannan bane matsalan yanzu, so nake in San taya kuka bi aka sa auren bayan ba abinda ita take so ba kenan"

"Yaya" Ibrahim inne yayi magana wannan karon, bayan ya share wata muguwan zufa "A lokacin da take housemanship a Zaria muka Saba da ita. Duk lokacin ban sanar mata da manufa ta ba, Sai dai ko a cikin wasa haka. Har ga Allah ni na dauka ta fahimce nine, saboda muna yawan wasan da ita so shiyasa ko da ta ban labarin Saurayin ta na dauka wasan take. Don duk a cikin dariya ta sanar min, har Ina ce Mata Mijin Novel kike jira kenan. Tayi dariya aka bar zancen a wurin. Sai ranar da nake ce Mata Yakamata In zo neman izini wurin haka hakanan, ta min dariya harta ce min mena ke yi daman tuntuni da ban je ba. I thought she mean it. Shiyasa na samu Usman muka zo wurin ka. Ina zuwa kace in turo su Baba, abinda ya faru kenan. Har ga Allah banyi hakan da wani manufa ba"

Zuciya Da Gwanin TaKde žijí příběhy. Začni objevovat