Sai da suka gama sa key in, a tare suka zube kan gadon. Sai Kuma suka kalli juna su ka tuntsire da dariya. "Kai Ummah case ce wlh" Halima ta fada tana kara yin nishin gudun da suka Sha.
"Ina Sabon wayan naki? In gani" Sai da Haliman ta fadi hakan sannan Nabeelarh ta tuno tunda ta iso, ba ta bi takan wayan ba ma baki daya. Jakan ta, ta nuna ma Halima kawai. Don tsoron Kar ta fita Ummah ta titse ta, ruwan toilet ta bude famfo ta dirka tana cigaba da kwasan dariya.
"Keh wa ya Miki irin wannan missed call in wai?" Halima ta fada cike da mamaki. Dam! Taji gaban ta ya fadi. Sai lokacin Cooper Abubakar ya fado Mata, ba ta ko shakka shi inne yayi ta neman ta. Gashi ba ta jin ta fada mishi zata zo Bauchi ma.
"Mu gani" a tsorace ta amshi wayan tana bin shi da kallo. Barin ma da ta tabbatar dashi inne yayi ta neman ta. Ba ta tare da ta sani ba, nan take yanayin ta baki daya ya sauya. Har wani irin dimi take ji na ratsa ta, ga yanda ta kara kura ma wayan idanu kaman zata shige ciki.
"Ke lafiyan ki kuwa?" Jin muryan Haliman ne, ya sa ta juyo ta kalle ta. Kaman za tayi magana Sai Kuma ta rasa abin cewa. Ba su taba maganan saurayi da Haliman ba a rayuwan ta, bar su dai suyi tsokanan su, ayi gulman wance da wane. Shikenan kawance, Sai Kuma yayin da suke zuwa Islamiyya a tare, wannan Kam har malamin su, sun sa ma hawan jini kila.
"Wa ke Kiran ki?" Haliman ta kara tmby.
"Ehmm wan..." Kasa karasa zancen tayi saboda yanda Halima tayi tsalle tana fadin "Your Boyfriend right?" Hararan ta Nabila tayi, Sai dai duk yanda ta so boye abun. Fuskan ta ya riga da ya bayyana komai take kokarin boyewa. Why is she so obvious ne? Meyesa ba ta iya boye abinda ya dangance shi ne wai?
"Iyye ashe munyi saurayi, to ya sunan shi? Come on tell me about him mana" kasa magana tayi, Sai ma tsintan kanta da tayi da wani irin murmushi. Ganin irin kallon da Haliman take Mata Kuma sai tayi saurin boye fuskan ta cikin cinyoyin ta, tana faman dariya kasa kasa.
Duka Halima ta dada Mata a baya "Ke dai banza ce wlh, ni Kuma kike jin kunya? Wai tsaya ma, what so new about this?" Kallon ta Nabilan tayi sosai "Kya jiki, ke kina dashi ne?"
"Ina dasu dai" Nabilan tayi saurin fada. Ganin irin kallon da Nabila tayi Mata yasa ta cigaba da cewa "Kallon fa malama ban Kai bane ba? Kinfa san muna fara University Baba ke mana aure, so gwara inci duniya ta da tsinke kafin lokacin yayi"
"Ba dai kyau yaudara" tsaki Halima taja "Yaudaran me? Ina da dayan da yafi kwanta min ai, zai ma zo gobe, zamu je ki ganshi ai. Now tell me about yours"
So confuse, Nabilan tunanin ta Fara yi kenan is normal every girl her age ace tana da saurayi kenan? Ba ta gama tunani ba Sai ga Karan wayan ta ya kara shigowa. Jiki na rawa ta dauka, a hankali tayi Sallama.
Shi inma a Hankalin ya amsa. "Ignoring me?" Yanda ya fada hakan, Sai da ya sa Mata jin wani iri har ranta, he sounds disappointed sosai. Sam, tana jin ba ta kyauta ba. Gashi shi bai manta da ita ba, Yana ta faman Kiran ta. Amma ita Kam zuwa tayi kawai tana harkokin gaban ta.
"Are you not talking to me again?" Ya Kara fada cikin cool voice in da ke kara ratsawa har cikin jinin ta.
"Ehm Ehm am sorry please Sir na manta da wayan ne a cikin jaka tun dazu" cikin rawan murya ta amsa mishi, he can even sense it.
"Kin manta dani kenan?" Ya Kara fada cikin muryan da ya fara saukan mata da kasala. Gabadaya ma, ji take kaman ba ita ba. Too many feelings to accommodate for three days, straight.
"Aa fa, I travel ne. Munje bauchi da Abbah. Shine na shiga cikin gida na bar wayan muna gaisawa" dan jim yyi zuwa can yace "Kinje Ziyara kenan? Ya kika samu su Umman" An dan sabon da suka yi a school, ya san dayawa daga cikin Yan uwan ta.
YOU ARE READING
Zuciya Da Gwanin Ta
RomanceBurin zuciya a ko yaushe shine ta samu gwanin ta. Ko da kuwa hakan zai zama illa a gare ta. To amma in hakan ne kadai ya rage zabi, ya abin kan kasancewa? Ku biyo ni... Ku fito kuji labari zazzafa Kan zuciya da gwanin ta Tsokar da babu irin ta mai s...