9

248 29 13
                                    

Jiki a sanyaye ta juya rungume da bags in, zata shiga gida. Four eyes, tayi da Yaya Khalipha yana mata wani irin mugun kallon. Ba ta San meyesa taji gaban ta bai fadi, Sai ma ji da tayi she is ready to defend soyayyan Sadeeq gaban kowa ye ma.

Sum sum ta taho zata wuce abun ta, kanta a kasa kaman ba ta ganshi ba.

"Au tafiya Zaki yi?" Har ga Allah ta so ya kyale ta, ta wuce. Ya barta da emotions in da take jin sun Mata yawa. Cak ta tsaya ba tare da ta dago kanta ba.

"Waye wancan?" Ta lura shi ma Yaya Khaliphan cikin zafin rai yake maganan.

"Saurayi nane" ta fada Kai tsaye, ba wani alaman tsoro da take jin ya taso Mata.

"Ni kike fada ma Saurayi Nabila? Mena fada muku ranar eh?" Wani guntu murmushi tayi ta kalle shi "Yaya wannan ba irin samarin da kake magana bane. A shekaru ma nasan zai kaika, Kuma kaima nasan kana da wacce kake burin aura at this age" wani irin kallon ya watsa mata, Sai da ta dan tsorata Amma ba ta motsa ba.

"Au shi ya koya miki ki min rashin kunya ko?" Girgiza Kai tayi tace "lah wlh ba rashin kunya bane, kawai dai..." Sai Kuma ta sa kafa ta ruga da gudu don ganin yanda ya ke matsawo kusa dashi. Sai da tayi nisa ta daga muryan ta "Gaskiya ne" girgiza Kai kawai yayi ya juya.

Washegari bayan sun karya kenan su kaji Sallama. Nabilah Sai da gaban ta ya fadi, saboda gane muryan Wanda ta ke sallaman da tayi, ba wai wani abu take Mata ba, Aa kawai tsaurin tane yasa duk wani Wanda ta girma ke shakkan ta.

"Ah ah Maraba da Maryamu har kin iso kenan" Ummah ta fada tana duban kofan falon, inda mamma ke kokarin shigowa. Daga ita har Halima a tsorace suka kalli kofan, kafin su yi laifi su ka tashi da sauri suna Mata Sannu da zuwa. Kayan da driver inta ke shigowa dasu, suka fara deba suna kaiwa ciki. Sa'annan su ka zo suka zauna suna gaishe ta, ta amsa ba tare da ta wani kalle su ba.

Gudun matsala yasa dukkan su biyu su ka shiga kitchen, ruwa da drinks suka kawo suka ajiye a gaban ta. Ummah dake gefe Sai ta dara "Yau Kuma kune kuke aiki ba tare da an saka ku ba Kuma?" Tsoro ba zai bar su, su tanka ba ko da sun San hakan.

Mamma kuwa cewa tayi "To daman Sai bako yazo su tsaya suna kallon shi? Kuna da abinci kuwa, don ban karya ba" da sauri Halima tace "bara a daura yanzu" Ummah Kam kallon ta ke, duk kiwuyan Halima, ita ke kokarin daura girki ba a sata ba.

"Kai nikam ai gwara da kika zo, Kya min maganin yaran nan" mamma Kam ko murmushi ba tayi ba ta kalli Haliman "Yaushe Kuma na fara cin girkin ki? Baba batanan ne?" Halima na dari dari ta je ta Kira ta. Nabila kuwa, Abincin da suka ci ya rage ne ta zuba ma driver in da suka zo tare da mamman, ta fita Kai mishi.

Baban na fitowa, su kayi waje dukan su biyu. Har zasu fita, Mamman ta kwala ma Nabila kira. Jikin ta har rawa yake, ta zo ta dan durkusa a gaban ta. Daman Nabila ba dai tsoro ba. "Ke Kuma tun yaushe kike garin nan?"

"Sati na uku" ta bata amsa a takaice, kanta ma baki daya kasa yake kallo, dan bata son tsautsayi ya sa su hada idanu da Mamman.

"Shine shi Usman bai San ya Kai min ke hutu ba ko? Zan hadu dashi kuwa, tashi kije" da sauri Nabila ta mike ta wuce, gaban ta har dukan uku uku yake. Fita su kayi daga sashen baki daya su ka tafi wurin mama. Daman Ammi kam Sai tayi kwanaki bata sa Halimatun a idanu ba. To da yake ba Mai magana bace, ba wada ya taba jin tace kala akan hakan.

Ba a son ran Nabila ba Halima ta jata bangaren Innah. Sun same ta tana kallo, suna shiga ta Fara "Ah Ah maraba da dubu dubu" yanda take Kiran Haliman kenan ita Kuma. Ba tama ko kalli Nabila ba, ballantana tasan tana nan ko bata nan. A haka dai Nabila ta gaishe ta, banda amsawan da tayi ba ta kara bi ta kanta ba. Sai ma hiran da ta Fara jan Haliman da shi. "Ke Sumayya tashi ki kawo ma dubu dubu fura da dambun da na ajiye maza, daman dai na ajiye na Mai rabo ne" Sumayyan jikan tane, na wurin ya mace. Hutu tazo Mata.

Zuciya Da Gwanin TaWhere stories live. Discover now