A hankali ya ke moving jikin shi toward kujeran da take zaune. Dan sunkuyar da Kai yayi, ta yanda yake fuskantan ta da kyau "Na- Bee-larh" dagowa tayi tana kallon shi. A hankali ya Kara furta "Ina son ki" taba saitin zuciyan shi yyi "My heart beats for you Nabee" duk tension in da take ciki, ba ta San lokacin da ta daga idanun ta, ta sakan mishi harara ba.
Dariya yayi sosai, duka dimples in shi suka lotsa sosai. One of the captivating thing, she found in him. Abinda ma ta lura, sanin dimples in na mishi kyau ya sa yake yawan yin murmushi.
Kamo hannun ta yayi, ya bude yatsun ta ya hade wuri daya da nashi. Ba ta janye hannun ba Sai wani irin kallo da ta watso Mai. Ai kuwa Sai ji tayi ya sa dayan hannu ya shafo kan idanun ta. "Cute eyes, wai ke ma kin iya tsiwa ko?"
Ba tace komai ba Sai sa hannu ta da tayi, ta rufe idanuwan ta. Dayan hannun nata kuwa Sai faman wasan ya ke dashi.
"Nazo har zan tafi baki ban komai ba"
"Me kake so in baka?"
"Nice words form you. Yanda zan dinga tuna ki ina tuki, in ta murmushi ni daya"
Kanta dai a kasa yake, ya Kara cewa "Ina jiran ki, am getting late kin kuma san hanya ba kyau"
"Thanks for the visit, it nice seeing you again" more like a whisper, zancen nata ya fito.
"Bara na maida ki gida, kafin a Fara neman ki" Yana fadin haka, ya tayar da motan. A kofan gidan ya tsaya, har ta danna kofan tana fadin "Allah ya kiyaye hanya" ta ji kofan a datse ya ke. Juyowa tayi tana kallon shi, ya daga Mata gira.
"Haka zaki tafi? Ba kice min kina so na ba"
"Ya ilahi!" Ta fada a ranta, ta dai lura ya cika neman rigima. Haka Kuma ya rantse Sai ya bi ta yanda yayi, ya cire ta daga comfort zone inta.
Ta dago tana shirin mishi magiya ya barta, ta wuce Kar tayi dare. Kawai sai gani tayi Yaya Khalipha ya fito waje. Yanayin yanda ta bishi da kallo yasa ya gane akwai wani abun. "Ya dai?"
"Ya Khalipha ne, Yayan Halima. Jiya ya mana warning akan Kar ya sake ya ga wata da saurayi a cikin mu"
"Au ashe ni saurayin kine ko?" Yanda ya fadi zancen ya sata darawa. "Shine Kuma ba za ace ana so na ba?"
Shiru tayi kawai tana murmushi. Gani tayi ya murda handle in kofan shi. "bara na fita na tsaida yayan naku, na sanar mishi na zo wurin ki ina neman izinin shi, tunda ba zaki fada ba" ta dauka wasa take amma Sai taga ya bude kofan yana kokarin bin bayan Yaya Khalipha da ya dan Fara nisa" da sauri ta Fara mishi magiya da ido da hannu, gudun ma Kar tayi magana Khaliphan yaji.
"Oya to tell me kafin naje" ta tsaya tana hesistating taji kawai ya bude baki "Bawa..."
"I love you wlh" ta fada da sauri, dariya ya kwashe da. "Yarinya nasan maganin ki" bude motan tayi cike da kunya ta ruga cikin gida.
Ranar gabadaya dinga tuno yanda Shirin su ya kasance a school take. Daga practicing poems, ranar aka basu wani Assignment in chemistry mai ban wahala. Duk son ta da chemistry, Sai da abun ya gagare ta, duk wanda yazo yaji ita ma ta kasa solving zai ce lallai ba kanta kam. Ba ma suyi zasu hadu ba ranar, kawai ya shiga ajin juniors Kai ma wata yarinya sako, dake shine master on duty ranar kawai ya ganta kanta akan littafi Sai faman cizon biro take, tana neman solution.
"Lafiya kuwa?" Ta ji an fada a kanta, murmushi tayi ganin shine. Don ko lokacin ba su wani Saba sosai ba, ba wani abinda ke shiga tsakanin su a lokacin Wanda ba academics bane.
Tsintar kanta tayi da mishi bayanin assignment in duk da tasan shi English teacher ne, Amma she is hoping for solution ko yaye ne. Amsa yayi ya dan duba, to abinda ba ta sani ba shine first degree in shi kan Biochemistry yayi. Don haka yana amsa ya gane matsalan, cikin sauki ya Mata bayani. Sai taga abun ma ashe sune suke maida shi babba, it so simple ma.

YOU ARE READING
Zuciya Da Gwanin Ta
RomanceBurin zuciya a ko yaushe shine ta samu gwanin ta. Ko da kuwa hakan zai zama illa a gare ta. To amma in hakan ne kadai ya rage zabi, ya abin kan kasancewa? Ku biyo ni... Ku fito kuji labari zazzafa Kan zuciya da gwanin ta Tsokar da babu irin ta mai s...