(16)

44 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Wednesday, September 2nd,2020.

(16)

***************

Haka akai ta yada kananun maganganu a tsakar gidan wannan,shi dai Maina yayi kunnen uwar shegu,Kuma jira kawai yake yaji Wanda zece dashi ya rushe katangar sa yaga aiki da cikawa...

Shidai Mallam sa'idu ya kafe akan ba Wanda ze Kara daga katanga a gidan da sunan ya ware kan shi..ya Kara da fadin Duk Wanda yake ganin ba'ai mai adalci ba kuma yayi yadda yake so..

**************

A kwana a tashi ba wuya gurin Allah me kowa me komai.se gashi an shafe kimanin watanni biyu bayan daga katangar su Maina,Kuma bayan daga katangar ma da yayi,se kawai ya yanke shawarar fara yin girki abunsu..dalilin yin hakan kuwa shine,se ya zamana bayan ya daga katangar sa,se aka fara masa kauron abinci,se a zubo abincin kadan Kuma ba kyan gani,wani zubin ma hadda kanzo ake zubo musu.inko akai dambun tsaki,se a zubo musu mai Dan mitsisi ta yadda sedai su ruga ci suna Kora wa da ruwa ,in miyar kadi akai Kuma,se kuga an tsulo musu ruwa aciki Dan azaba da bakin hali,yaga dai shi Allah ya rufa masa asiri,balle ya tsaya ana mai wulakanci,hakan ne yasa ma be wa kowa magana ba ,suka fiddo murhun su da yan tukwanen su guda biyu..

A ran da zasu fara dafa abincin su ,tare ma suka tafi debo ruwa a rafi.cikin kuran tayi shigewar ta,se ta dauke jarkar gun ta kama ta daure a jikin wata jarkar,se ya ruga tura ta Yana mata gudu,tai ta Dariya kuwan,a hakan suka je har Rafi,ba Kuma ruwan su da mutane,gefe ya sata ta zauna shi Kuma ya ruga zubo ruwan sa a jarakunan sa,Yana. Gama wa sukayo wankan su, suna  gama wa Kuma se ta haye gun Turin dama da yar saka a jiki,se suka tsaya sukayo iccen su,Dan Maina yayi alkwarin baya bukatar komai nasu tunda abun ba mutumci a ciki..

Bayan sun zo gidan ya sauke ta ta shigo cikin gidan,shi Kuma ya aje iccen sannan ya wuce sahun farko.

Kai tsaye tayi rumfar Inna Mari,a Nan ta kwanta tana ta bawa Inna Mari Labarin yadda Maina ya daura ta a kan kura Kuma da yadda sukai wankan su a rafi.ita dai Inna Mari abun duk kunya yake Bata,Amman ya ta iya tunda Allah ya hada ta da 'ya me wauta?

Anan Mairon ta karya sannan ta wuce gun Innaji,daga nan ne tayi gurin su.A kofar zauren su ta tarda Hasi ta fito,Dariya sukai wa junan su sannan Hasi tace .."Adda ina kika tafi kika barni ?"

Cewa Mairo tayi .." Rafi mukaje da Hammah Dan kiji yarinya har wanka mukayo.."

Hasin ce tace .."Amman Adda shine Nan kika tafi ke dai,mekon ma kice mu tafi tare?"

Cewa Mairo tayi.."bari gobe maje tare,bakiji ba har kan kura na hau Hammah yayi ta tura ni.."

Rumfar su Mairon suka shige,nan Hasi kece wa Mairo .."Adda nifa yanzu haushi Hammah kama yake ban,gashi banna son abunda yake mun kullun wallahi,na rasa yadda zanyi Adda.."

Cikin hawaye Hasina ke fadin haka..Nan take jikin Mairo yayi sanyi,Sanin cewa Hasina ba komai take wa kuka ba,hakan ne yasa Mairon ta gane cewa Hasinan ba wasa take ba..

Cewa Mairo tayi.."yo ya zakiyi kenan?"

"Ban sani ba nima Adda"

Daga kofa Kamalu da tun fara zancen yake tsaye yake jinsu yace .."Ah ah Addar mu me kikai wa Hasi ta take kuka?" Wato yayi kamar be ma ji su ba

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now