WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Wednesday, 21st October. 2020
(31)
***************
(Yar guntuwar shawara ga maau ganin cewa gaya wa saurayi ana son shi ba komai bane,toh albishirin ku,da wani abu,dan wallahi ba karamin zubda mutumci hakan keyi ba.sannan Kuma in aka ki karban tayin soyayyar taki kisha kunya..anan dai bazan ja da yawa ba,Amman hausawa na cewa .."Duk Wanda ya debo da zafi,bakin sa!")
Isar su Ummi office,kowa ya Kama gun aikin sa,suka cigaba.in kaga Ummi se ka rantse ba abunda yake damun ta,dan ta bala'in iya boye damuwar ta,har na a kasa gane wane yanayi take ciki.har zuwa sanda aka tashi daga aiki,Amal Bata bar rarrashin ta ba,ita kuwa ummin se cewa take kawai.."hmmm" , irin ni na san me nake ji din nan.
Da haka dai har suka tashi,kowa ya kama hanyar gidan su..
***
Maina bayan ya shiga asibitin yayi abunda ya Kai shi,sannan ya fito shima ya kama hanyar gidan sa abunsa.se bayan yaje gidan ne take ta faman jujjuya maganar da sukai da Ummi.
Kai gaba daya ma shi abun mamaki yake bashi,wai kamar Ummi ce ta budi baki tace tana son shi?,shi ya zata a Kauyen su kawai ake haka,Amman da ya tuno zully wadda ta kusan Masa fyade ma se ya ga cewa ai ana yin hakan ma a Birnin,kai har fiye ma da tunanin shi..
Ita dai Mairo taga alamun cewa hankalin Maina Yana wani gu,Amman Daman duk yan kwanankin nan haka yake zama yayi ta sake sake shi kadai.
Abinci ta kawo masu suka ci,seda suka gama ,se Maina ya labarta Mata yadda sukai da Ummi,Nan fa Mairo hankalin ta ya tashi,tuni ta fado jikin shi tana kuka,wai ita bata son yayo mata kishiya.shima a bangaren shi,hakuri yake ta bawa Mairo,tare da tabbatar Mata da cewa baze iya mata ma kishiyar ba.
Lallai hankalin Mairo ya tashi,ta tuno yadda Bakon nan nasu yake Dan gayu,gashi Kuma wai kanwar sa ce ma Ummin,toh indai haka ne ai kenan itan ma Yar gayun ce,Kai inaaa! Wallahi bata yadda ba!
Haka dai tai ta Masa yan daru,har ya samu ya Dora ta bisa jirgin kauna Wanda ya rufe Mata idanu da baki hade da hanci da kunne ta mance da wannan duniyar ..
Bayan lokaci me tsayi,Mairo ta kammala secondary School din ta,Kuma Alhamdulillah an samu abunda ake so..
Toh daga nan dai ta tsaya da karatun,Amman ko ba komai ta kile yanzu,tasan bambancin kauyanci da Kuma gayunci,sannan Kuma tana karanta komai in ta ganshi,Haka Kuma tana gane wa.wanda kuwa Bata gane ba,tuni take zuwa ta bude dictionary din da Uncle Munir ya bata,Nan zata dubo ma'anar kalma Kuma ta gane a wuce gurin..
Idan baku manta ba,sana'ar saida gwanjo Maina da Mairo keyi..shi Maina ba karamar wahala yake Sha ba in Yana yawon neman ciniki,Haka zeyi ta zabga gumi,ga rana,wani lokacin sanyi,ko kura,hazo da ruwan sama.
Amman da yake Yana neman halalin sa ne,se kawai ya manta da wannan wahalhalun ya ci gaba da neman na kan shi.
A wani debo kayan da Maina yayi,ya debo jaka ta Mata guda biyu a cikin kaya.shi a nufin sa ,a ribar su ya sai wa Mairon sa ,ai kuwa su humaira na ganin jakan Nan suka rude a siyar musu a siyar musu.
Da Mairo taga haka se ta dauke jakunkunan ta nuna wa Maina cewa su humaira sun ce se an siyar musu, dole Haka nan suka siyar musu tare da alkawarin siyo Mata wasu ita ma..
![](https://img.wattpad.com/cover/238861444-288-k943635.jpg)
YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomanceLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...