WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Saturday, 29th August. 2020
(15)
***************
A haka Mairo da Hasi suka kasa boye mamakin su,dan sun san Innar su da kunya,har gwamma Baffan su ma ,Amman se gashi Inna ta sake dasu Hammah tana ta Shan Hira..
Sun dade sannan Maina ya tashi ya nufi gida Dan zeje aiki..
Yana fita Inna ta kalli yan diyan ta ,tace musu basu da matsala dai ko ?
Sukace Babu,Amman Kam Nan da Nan Hasi ta hau bawa Inna Labarin rayuwar su a gidan tun daga farko,in banda Inna ta kwabi Hasinan ma da tuni tayi kwaba..
Ita dai Mairo se kallo da ido,tana Kuma sauraren yadda Hasina keta zuba zance,da Duk abunda ake wa Addar ta ta a gidan..se Kuma dukkan masu son su suma a gidan ta fada ..
Cikin hikima Inna ta ruga bin su da tambaya ,Nan ta fahimci cewa Hasina ita lafiya Lau take ,amman ita Mairo tana da matsala ,Amman da yake miskila ce se kawai ta ruga amsa wa da ..."hmm"
Su Talan ne suka dawo ,se Hasi ta tashi suka yi kor gida.a Nan ne Inna ta tisa Mairo da tambaya,ko da taga nuku nukun baze yi Mata ba ,se ta fito fili ta tambayi Mairon ko tana da damuwa ta bangaren kwanciya da me gidan ta..
Nan fa Mairo ta hau kuka tana cewa .."ni Daman na gaji, kullum zafi kullum zafi gashi se an dade Inna ,nidai banni koma wa gidan ,gwamma dai daga nan se I ruga zuwa muna tadi .."
Kallon Mairo Inna tayi ,kallo irin na tausayi,da mamaki .shiyasa tun farko ita bata so auren Mairo ba ,tasan diyar ta Bata da wayo,tasan batada juriya ,sedai batayi tunanin har yanzu akwai rishin wayon ba a tartare da Mairo,ji dai ko daga Labarin da Hasinan ta bawa Inna ita Mairon dai ce kamar wata sokuwa a zaman gidan ma ,ita yanzu tunani ma take yadda Maina yake da Mairon..kallon ta take tana auna yadda tace wai .."ita batta koma wa ,gwamma ta tsaya shi ya ruga zuwa tadi"..Abun ma abun Takaici Kuma abun Dariya ,Amman ya ta iya ,Daman tasan a runa wai an saci zanin me rangwamen hankali..
Da yake daga cikin rumfar su suke ,Baffa baya jiyo maganar mi suke,sedai kukan Mairo kawai ya jiyo,Nan ya kwala Mata Kira ,tana amsawa tana kukan ta ta nufi rumfar shi,a jikin shi ta fadi tana kuka tana cewa .."Baffa Gani"
Shi yayi zaton ko Inna ce take mata fada,shiyasa yace .."Yi shirun ki haka,kyale Innar ki,ita haka Nan ake yo,daga zuwanki yau har ta Sanya man ke kuka?"
Tashi tayi tace .."Ni Hammah ne ba Inna ba ,banni koma wa gidan kaji Baffa,kullun kullun fa se ya ruga hay....."
Kan ta karasa Inna tayo sallama tana cewa .."Oh yau ni Dije naga ta kaina,wai ni kau Mairo se yaushe Zaki hankali ne?"
Da yake Mairo na tsoron Inna ,se tayi shiru,Kuma ta so ta gane tayi wani Abu ba dai dai ba,toh Amman mi tayi?"
In Baku Manta ba Daman kun San Mairo ce yar lelen Baffa,haka Nan Kuma tafi sake wa da Baffan ta akan Innar su,Dan Inna badai fada ba..ita kuwan batta son fada ,yanzu ne ta fara kuka..
Koma wa jikin Baffa tayi tana cigaba da kukan ta,shi Kuma Baffan yaso ya fahimci me zata iya cewa ,Amman be San takamaiman mene ba,kawai dai yasan wauta taso dafka masa tunda yaji Innar ta katse ta,tun da Kuma yaji Innar ta kwabe ta se yayi shiru Yana ta rarrashin ta ..A hankali ya Soma Mata Labari me kamar nasiha dai dai da yadda zata fahimta ..

YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomantizmLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...