(32)

43 4 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Thursday, 22nd October. 2020

(32)

***************

Washegari Maina be fita ba,Yana daki,kamar yadda ya tsammata kuwa se yaji Humaira tazo wuraren daya saura.

Anan take cewa Mairo.."Na Kira kawata fa,zata zo itama,Amman se mu fara kan tazo,nasan zakiji dadi,Dan in kika gwada ma baza ki iya daina wa ba.."

A zuciyar Mairo tace ..(gwaji ma Allah ya tsare Ni da shi,ya haneni da shi,Kuma Allah ya yaye muku ya shiryar daku )

Amma a fili se Mairo tace .."Eh Haka ne kuwa,tsaya na kullo mana gidan,sannan na zagaya bayan gida na fito.."

Cikin fara'ah Humaira tace "Toh.."
A take ta cire hijabin ta,ta rataye a igiyar shanya dake daure a Yar tsakar gidan su Mairon,se gata ta bayyana cikin siket na atamfa da yar top.

A bandaki kuwa bulalai Mairo ta dauko,Daman a Chan Maina ya ajje Mata su,ya Kuma mata bayanin yadda zata zane musu Humaira,ko da Mairo ta debo bulalai ta fito ta fara wani bori tana zubo fillanci,ke kyace me iskar gaske ce,tuni tayi kan Humaira da duka.tayi ta lafta Mata wannan bulalan,shiko Maina Yana daga bayan kyaure Yana leko su,ga Dariya kamar ta kashe shi.Dan Mairo cewa take Mai .."karfa ka bari ta buge Ni,ka tsaya kusa da tayo kaina kazo ka tare min.."

A fillanci take wannan maganganun,ta kuwa yiwa Humaira mugun dukan tsiya,seda ta Mata lis lis sannan ta koma ta fadi.

Humaira kuwa ta bude kofar gidan da gudu ta fice ..a soron gidan su ta tsaya tana maida nishi.ga uban kuka da take Yi,ga tsoro ya kamata yau tayi gamo da aljanun Mairo..

Babar su ce taji kukan ta,tuni ta leko tana tambayar me ya faru,Nan tace wa Babar su wai Aljanun Mairo ne suka dake ta da bulala.."

Mamaki ya kama Babar su humaira,tace .."wai daman Mairon nada mahukatan iska shine bamu sani ba?,yanzu da shake ki sukai fa kika mutu fa?"

Ita dai Humaira kuka take Yi,ga jiki yayi rudu rudu,ita kadai tasan yadda ta Sha duka,dan ta mugun dakuwa a gun Mairo,Kuma ta kasa rama wa saboda tsoron Aljanu Daman gare ta.

Haka dai Babar su ta kamata suka shiga ciki,tana ta al'ajabin wannan lamari.

Chan tace .."Humaira amman dai bakin kara komawa wajen mairon ba ko?"

Humaira dai batai magana ba,se hmmmm kawai take cewa,yo ita ko da kudi ma ta koma gidan Mairo,ai ita Sam bata shiri da masu iskokai,Dan haka ba sauran alaka a tsakanin ta da Mairo,ba ita Mairon ba ma,hatta Mainan ma ta hakura dashi in dai abun hakane..

Humaira dai seda aka hada da su gasa jiki,da bacci har seda tasha paracetamol ma..niko nace gobe ma ta sake ..

*******

An samu tsawon lokaci sosai,Wanda a dai dai wannan lokacin Maina ya chanja sana'a kala uku,da yana saida gwanjon shi,ya dawo ya koma zuwa wani gu da yaga ana aikin gini,daga baya ya bar gun lebura,ya koma gun masu gyaran mota..

A wannan lokacin Maina gyaran mota yake koya,sedai tundaga danda ya gane kan gyaran motan,se ya zamana har ya fara janye mutane,kowa yazo da motar shi,se yace Maina ne ze gyara masa,a dole me gidan su Maina me suna Olabo ya sallami Maina..

A halin da ake ciki kuwa ,Abubuwa sun fara wa maina yawa a kansa,rayuwar ta fara juya Mai,ta Kai ta kawo,komai se an tara kudin shi,Sakamakon tashi da Maina yayi daga unguwa uku,ya koma wata unguwa wai ita Sheshe dake tsakiyar badalar cikin garin Kano.

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now