WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Saturday, 26th September. 2020
(24)
***************
Suka fara girkin su da kansu..
Maina ya karbo baaron sa,inda seda akai Masa aikin katako ta sama,inda ze ruga jera raken..
Tuni yaji saukin wannan abu,shi ba Mai zesa ba, ba fetur ba,kawai tura wa ne,Kuma wannan ba wani Abu bane a gunshi..
Kullun ze debo ruwa da dare,Wanda zasu kwana dashi,sannan da asuba da sunyi wanka se ya fita ya debo Mata wani. Yana dawowa ze karya,se ya tafi wani filin kwallo da suke buga kwallon safiya,ya tsaida baaron sa,anan ze tsaya har goma,sannan ya zagaya a gari,se Magariba yake dawowa gida,Yana Sallar isha'i se Kuma ya fito kofar gidan su ya tsaida baaron sa..anan ze ta zama har se gurin goma se ya shigo gida.
In ya shigo kuwa wani zubin ya shigo musu da awara,ko kosai suci kayan su . rayuwar su dai cikin rufin asiri..
______________''
Matsala ta farko da ya fara fuskanta a zaman gidan shine wannan debo ruwan,Kuma gashi ko ya debo bokiti biyu be cika isan su ba,Dan Maina mutum ne me azabar wasan ruwa,Yana son ruwa a rayuwar sa,shidai yayi wanka yaji dadi,haka ne yasa ko shi bokiti biyun ma sun Mai kadan,bare Kuma har su biyu.se Kuma ruwan shansu da yake zuba musu a wani Kofi me murfi,shima kan wani lokaci ya kare.
Na shan su,dole tasa ya samo musu Randa Yar dai dai misali,da wani Dan bokiti me murfi wanda yake cin bokiti hudu na ruwa suka ijiye shi a Dan dakin su.A Nan ya kau da wannan matsalar.
Se matsala ta biyu,shine watan da sukai a Nan gidan ,Zeema ta matsa masa,ta sa Masa ido,ta kafa masa kahon zuga..
Kullun da dare in Yana waje, se taje ta wajen,ta samu gefen shi ta zauna,Haka zatayi ta matsowa kusa dashi,wani lokacin har se ya tashi ya bar Mata gun.dan har se ta ruga gogar masa jiki...
Ya rasa yadda zeyi da zeema,gashi yanayin yadda take kwata kwata Bata cikin tsarin irin Matan da yake so..
Dole haka ya hanawa kanshi zaman waje ,Dan zeema ta hana mishi cinikin sa..
Se Abu na uku,Wanda Duk dai Zeeman ce,bayan ya daina zaman waje,se Kuma ta tsiri zuwa ta kwankwasa masa kofa,wai zata siy rake,in ya fito ta runga Masa kwarkwasa,har in ya Miko Mata raken ko chanjin ta se ta shafo Masa hannun sa.
Haka yake ta daurewa ya share ta ya nuna Mata be ma San me take Yi ba.
Ana Haka ma yayin rake ya fara fita,dole ya ajiye rake,Yana shawarar debo abun yayi,ko dai goba ko yalo.
A karshe ma dole yalo ya debo,Haka ya fara gara yalo,toh da yake shi yalo ba kowa ke son shi ba,se ya zamana baya ciniki dakyau,dole ya watsar da yalon,a lokacin yalo akwai gurjin gidan gona.
Tuni ya debo gurji ya fara gara shi,a karshe ma se ya samu makarantar bokon da yake zuwa ya tsaya in an tashi yara suyi ta siye,gashi a koman shi bayi da tsada hakan yasa yaran suka gane se suke ta rububi a gun shi..
Shidai in ze samu riba ko ya take ala amfana..
A hankali a hankali Kuma, ya koma in an tashi daga makarantar bokon wurin karfe biyu haka, se ya cigaba da yawo,yamma nayi yake zuwa kofar wata islamiyya,Haka zeje chan ma yayi ta ciniki in yaran sun tashi daga islamiyya.daga nan se ya koma gida..
YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomanceLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...