(13)

52 3 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Sunday, 26th July. 2020

(13)

***************

An samu Mako biyu ana ta kokarin ballo ruwa a gidan Wanda ake wa lakabi da "Gidan yawa"
.ruwan kuwa daga bangaren su ladidi ne da Uwani ,se Bintalo da ta lura da cewa su Uwanin suma basa yin Maina,Amman ita a nata haukan ,yadda suke nuna mata,so suke ta laka masa sharrin cewa ya mata ciki ,su ta bangaren su su bata mai suna ,ita kuwa Bintalo dan ya aure ta ne take son yin haka,saboda ba karamin son shi take yi ba ,sedai shi be ma san da ita ba ,balle har ya San da cewa tana son shi.Shi kam in banda randa sukai karo a bandaki be taba ma ganin ta ba,kuma ko a yanzu ba wai ze iya cewa gata bane ba..

Se gashi a tsakar gidan an fara yabadidin cewa Maina na neman Bintalo duk kuwa da cewa har yanzu a matsayin sabon Ango yake..

Isiya yaron Wanda zeyi sa'an Hasina ,shine ya gaya wa innaji abun da yake wakana a tsakar gidan.ko da ma a yadda ya gaya mata ,cewa yayi .."yaji ana cewa wai 'Da guda dan iska ne .."

Dajin wannan magana Wanda Innajin ta tabbatar Isiya baze mata karya ba ,se ta taryi Maina da batun ,tace kuma kar ya kula su,ta tuna masa da cewa daman tun tasowar sa da yawa a cikin gidan Yana da yan bakin ciki ..

Budar bakin Maina yace .."Aiko duk Wanda ya fado wannan maganar se ya kawo yadda farkon ta yake ,ma'ana se yayi bayanin yadda akai har shi ya zama dan iska.da har ake cewa yana neman bintalo."

Innaji ta sake baki,dan tasan ba haka Maina ya saba cewa ba ,kusan kullum in taji husuma na kokarin tashi wadda ta hado da Maina ciki,ita ke kiran shi ta ja mai kunne dan kar ya shiga maganar ma.tana dire wa se yace mata ..."innaji ki kwantar da hankalin ki,ni ba abunda zanyi,kowa da bakin shi ya fadi duk abun da yake so .."

Amman a wannan karon se kallon shi tayi tana bude bakin ta Wanda  goro take tauna wa,tace.."'da guda yaushe ne har ka chanja daga yadda na sanka ?"

Cewa yayi "Ni ban chanja ba Innaji,kawai dai wannan karon sunzo da abunda zan iya cewa sun wuce gona da iri ne,dan mako ukku baya akwai maganganun da naji da kunne na suna yi,radda mukai karo da wata diya a kewaye,kinga ko maganar ban miki ba,a daren sun fadi maganar da ta batan Rai Amman nayi shiru na kyale su a zato na zasu bar maganar tunda dai na dauke kai na,na ga ne kamar sunga ana tsoron su dan sunga ana musu shiru shi yasa ni kuma naga lokaci yayi da zan tsayar da wannan katsalandan din,kina ga dai yanzu nayo maki kishiya,duk da chan basuyi wannan maganar ba se yanzu ,dan kawai a bata mun suna a idon iyali na ?"

Kallon ta yayi yadda ta saki baki,shi kan shi mamakin kanshi yake ,ta yadda yake jin ze iya kai ruwa rana da duk wanda ya tsiro da wannan maganar..dan in yayi wasa har diyan sa se sunji wannan maganar .

Cewa yayi ,.."Rufe bakin mana ta karfen kar kuda ya samu masauki ciki "

Rufe bakin innaji tayi tana fadin.."humm"

Kallon shi tayi tana mamakin shi.gashi tasan shi baya zance da yawa ..kan tayi nisa a tunanin ma ya samu ya sauya salon hirar ,Nan take ta gane cewa fa magana dai ze yita ba fashi. Haka ta kyale shi sukai hirar su wadda Rabin hirar duk magana ce me gugar zana ta ruga mai,rabi Kuma nasiha nasiha a bai bai..

Sati biyu bayan zaman da Innaji tayi da Maina.tun tana sa ran ze yi wani abu har ta hakura ta hau murnar yaji maganar ta Kuma ya fasa yin komi..

Shi kuwa Maina hankali ya maida kan Mairon sa wadda izuwa yanzu in ba rabar shi tayi ba Bata jin dadi,ta Saba da jikin shi sosai sosai,duk da da kunya take yin makale-matan,Amman shi abun Yana bala'in kayatar da shi,a gefe guda Kuma ya bari yaji maganar ne da kunnen sa se yayi maganar yaci uban duk Wanda yake neman shigar mai hanci da kudundune . .

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now