WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Friday,5th September, 2020.
(18)
***************
Maina ne yake cewa .."Nifa yunwa nake ji.."
Tashi kama yayi Yana cewa .."tsaya na dauko Mana,Allah ya taimake ka ban ci ba,da sedai ka kwan da yunwa.."
Cewa Maina yayi .."yunwa biyu ba ,gata Mata ta gata cikina .."
Dariya sukai suna tafawa sannan kama ya fice ya nufi dauko tuwo..
********
Asuban fari Maina ya sake wanka ya sauya Kaya se Masallaci,ko da aka idar Ubale yaga Maina se ya hau washe baki,gashi Daman suturar Maina ta Isa ta nunawa me kallon shi cewa fa jiya ba yau ba,Nan suka hau gaggaisa wa da mutane ana tayi wa Maina son barka.dan dama da baya nan kowa ya tambayi Ubale Ina Maina,se yace "Ah ahaf ai Maina ya nufi gidan sarkin Burum,ai achan ya samu aiki.."
Dan haka dai yanzu da alama ga zahiri nan jama'ar hayin su sun fara gani..
Ubale se cewa yake.."saukar dare Kai kenan daguda?"
Shi Kuma Maina se daga kai yake kawai Dan baya so ya bada Labarin karya,a haka suka rankayo gida tare da sauran mazan gidan kowa se kallon Maina ake Duk da da sauran duhun gari,Amman Kuma da yake akwai hasken farin wata,se ya zamana kowa na ganin kowa ,Kuma shi Maina ana ganin yadda yake sanye da sutura me kyau ..
A cikin gida gun Innaji kawai Maina ya wuce shi Kama kuwa yace Yana zuwa.daman Maina ya saba daga Masallaci se gun Innaji,Yana shiga da ta gan shi se ta saki fara'a ,cikin azama ta fara lalubo magurjin ta da goro .kan ya zauna ta fara Mika Mai,karba yayi Yana zama ,gaisa wa sukai se ta fara tambayar inda ya tafi ya dade,shi da akai dashi ze zo bayan Mako Ukku?
Nan dai yace Mata be samu damar tahowa bane se yanzu..Nan sukai ta hirar su Yana goga Mata goro tana ci,cewa take "Daguda Rabon da naci goro me dadin wannan na mance ,yo shegun yaran Nan ma ko gogawar da kyau basuyi.se a ban goron har Yana niyar kashe mun dasashi .."
Haba me Maina zeyi in ba Dariya ba..cikin wannan yanayi kama ya shigo Yana dariyar maganar da yaji Innaji nayi,Yana zama tace .."Dan nema ,harda Kai ai,munahiki.."
Sudai Dariya suke tayi..daga nan Maina ya tashi , lokacin kusan bakwai na safe,rumfar Inna Mari ya wuce shi kuwa kama ya wuce gunsu..
A tsakar gida ya ganta ,Daman tun da yake da Innar sa,be taba ganin ta batai wanka ba,kullum ka ganta da wankan ta ne,hakan ne yasa zaman su Mairo ma a gun ta da an tashi Sallar asuba se wanka ,Kuma ba'a koma wa bacci.
Daga cikin zaure Mairo taji Inna na cewa .."Ah ah Daguda ne ,saukar yaushe ,lale"
Fit Mairo da Hasi suka fito,Amman se Mairon taja ta tsaya a kofa tana kallon gefe,wannan abunda tayi ya nuna cewa fushi take dashi.yo Amman fushin mi,iya Sanin mu dai ba abunda yayi Mata ,sedai Kuma Allahu a'alam..
Zama yayi a taburmar da take zaune Yana jin wani murna na ganin mutane biyu da yake jin soyayyar su ta tsanani a ran shi..ga Innar sa da suka fara shiru kwanakin baya se Kuma matar shi, Mairon shi masoyiyar zuciyar shi..
Yana gaida Inna Yana satar kallon Mairo da take ta faman zunburo baki,Innar na ganin shi,ta lura Kuma hankalin sa nakan Mairo ..
Hasi ta gaida shi,Yana kallon ta yaga yadda tayi kyau da Dan ciki a jikin ta ,take yaji sha'awar ganin Mairon shi da ciki a jikin ta kamar haka,A ranshi yayi Addu'ar Allah shima ya bashi ikon Yi Mata cikin..
YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomanceLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...