(23)

36 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Saturday, 26th September. 2020

(23)

***************

A gida,a bakin kofar dakin su suka zauna ,Nan suka tsinci shinkafar Nan tas,suka dora,tana dahuwa Maina na daka yaji..

Bayan ta dahu Kuma suka soya Mai..

Nan suka kimtsa kan komai suka gyara gun suka zauna suna cin abincin su a tare abunsu,suna yi suna soyayya..

Tuni mazauna gidan suka fara tsegumi ,Dan a masallaci ma bayan an idar da Sallah,akwai Salisu Wanda shima Dan haya ne a gidan da Maina yake haya,yace Masa "wai wani irin abu take Haka,salon bada maza har wani yaji take daka wa matar sa,wankin da yake Mata be Isa ba"

Salisu ya Kara da cewa.."baka ga ba mu sedai Matan mu suyi mana wankin ma,Kai kuwa ka wani zage kana wa karamar yarinya bauta?"

Kallon shi Maina ya ruga Yi,sake da baki,da hanci da ido,dan Salisu ya bashi mamaki ma'ishi..

A wannan lokacin Maina ya nuna wa Salisu ba bauta bace ba,tunda ba Wanda ya saka sa,yace shi yaga dama ne dakan sa yake Yi.."

A takaice dai,tundaga wannan lokacin Salisu ya dingi zuga Maina ,Yana ce Masa ,ba kaga da mun tashi muke ficewa ba,Kuma in mun dawo mu samu an Mana komi?,Kai baka son irin Haka?,nifa Mata ta tsabar
Biyayya ko kallon ido na Bata iya Yi,tsoro na ma take ji,wallahi ka dai na yin wannan bautar ka zama tsayayyen namiji "

Shi dai Maina a kullun da Koda yaushe se yayi ta yiwa Salisu Dariya,dan a Kauyen su ma cewa aka dingi Yi wai Mairo ta maida shi sullutu,wai ta shanye shi,ta asirce shi,Kuma yayi biris ya banza da maganar ya cigaba da hidimar sa,bare wannan Salisun da shi zuga shi ma yake Yi kai tsaye,toh ya maida abun wasa Dan ma kar ya saka abun a ransa suzo su samu matsala da Salisun wataran..

Gashi Maina ya tsani a ruga mai kutse a rayuwar sa,Amman duba da cewa a kauye ma anyi,yasa ya share ya maida Salisun sakarai,Kuma in batu ne na biyayya ai sedai in be furta ba,Haka ma yasan Mairo na tsoran shi sosai,Amman tsoron nata na gudun bacin ran shi ne,toh shi in be Mata ba,waze yiwa?,yarinyar da ya dauke daga gun iyayen ta,ya kawo ta wani gari,shi se yake ganin Kamar Mairon ta gama Yi masa komai ai,Kuma take ganin cewa ta cancanci ya mutumta ta ya darajta ta..

*********

Kwanshi tashi asarar me rai,se gashi su Maina sunyi wata guda a Kano ,Kuma a gidan haya,Wanda kowa na gidan ya gane cewa Mairo da Maina masoya ne na gasken gaske,hakan ne yasa bakin ciki,kyashi da hassada ya fara shiga cikin zuciyar mazauna gidan,in ka cire Malam Ado da matar sa Aisha,sauran mazan da Matan su, irin salon rayuwar su Mairon ta tsaye musu a Rai..

Su mazan sun San cewa Mairo tanai wa Maina abunda Matan su basa musu,Haka Kuma Matan ma suna gani Kuma sun San cewa abunda Maina yake wa Mairo,ko zasu mutu mazan su baza su musu ba.

Shine abun ya dame su,ya addabi rayuwar su,da yake ana zamani na mutuwar zuciya,se Maina ya lura da wasu daga cikin matan suna masa wasu alamu na nuna so ko Kuma Jan hankali,sunai Masa gwalangwaso da iyayi,Amman se ya share ya fita daga batun su..

Mairo kuwa se ta koma Kamar suna kishi da ita..

Tunda sun samu wata guda a gidan,Mairon ta saki jikin ta,mafi akasari in Maina baya nan se Aisha tace ta fito ta Sha iska tunda ba maza a gidan,se Dan small ne kawai yake ragewa,shima din da ya gama baccin sa yake ficewa daga gidan se Kuma an ganshi..

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now