WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Thursday, 15th October. 2020
(28)
***************
Me karatu ze Yi mamakin yadda akai Maina ya daina sana'ar sa a farko ko?
Toh wannan dalilin be wuce ganin cewa ya samu aiki me biya da kyau,ta yadda Albashin shi na wata guda ze rike su har tsawon wata Ukku ko ma fiye.Wannan dalilin yasa daga shi har Mairon suka tattara suka daina sana'ar,ita ta maida hankalin ta kan karatun ta,shi kuma yake ta fama da biyan kudin makarantar Mairo,hadi da yan siyan littafi,dan kudin mitfife (meat pie) da sauran su..
A yanzu kuwa Kwatsam su Alhaji sun bar kasar Najeriya,inda Maina kuma ya bar aikin babban gida,toh amman da yake Yana da yan sauran tarin sa,ga Kuma yan kudaden da Alhaji ya bashi,se suka dukufa da zaara wadda hausawa kan ce bata taba barin dami ba ..
Ganin abun na neman wuce tunanin Maina ya Sanya shi koma wa sana'a,toh a halin yanzu dai Maina dan bola ya koma..
Wannan kenan.
**********
Tafe Maina yake cikin unguwar su ,Yana ta yawo Yana ihu "za'a Kai shara a kura?"
Da Haka masu shara ke ta fito da bolar su,Maina ko ya amshe ta ya juye a kurar sa sannan ya sake tura wa gaba,da ashirin da talatin zuwa hamsin shine abunda yake samu,Dan akwai ma masu bada goma,Amman Maina be taba rainawa ba,shi dai a kawo ko nawa ne ze karba ..
In ya gama hada bola shi, kurar nan tayi dam da ita,se Kuma ya dau hanyar zuwa inda ake zubarwa Wanda ba karamin tafiya yake Sha ba,haka zaku gan shi kamar wani mahaukaci ,Yana ta tafiya yana zabga gumi,a haka dai ake ta wannan rayuwa ..
Maina ya samu wata kusan biyar yana zubar da shara,sannu a hankali ya fara gajiya da wannan sharar da yake yi,toh da yake Mairo na Saida yan gwanjo na Mata,se kawai shima ya yanke shawarar siyo na maza ya tuga yawo da su,hakan kuwa yayi,yaje ya siyo kayan Nan,seda ya fara dibar wa kansa kala biyu,riga da wando ,sannan ya zauna yayi musu kudi, washegari ya jere kayan sa a kafadar sa ,ya kama hanya Yana ta tafiya Yana ta tafiya,ga Maina kamar Aljani,tafiya Bata taba masa wahala,duk nisan wuri se yaje da kafar sa abunsa.shi wannan ba wani sabon Abu bane..
Ba laifi yayi ciniki,Amman ba wani yawa,Haka yaci yawon shi ya dawo gida,ko da ya dawo ya tadda Mairo tayi kicin kicin ta bata rai..
Ko da ya tambaye ta abunda ya faru,se ta fara kuka,ita wai gida zata,tayi mafarkin Baffan ta,Kuma so take taje ta gano shi..
Nan Maina ya fara, lallashin ta,amman fur Taki shiru,Dan hankalin Mairo ya koma gida.
Shi dai yana ta kallon ta,lokaci guda Kuma tausayin ta ya cika shi,dan kam sun yi shekaru rabon su da gida.
A hankali ya janyo ta ya fara lallashin ta cikin salon da ya wuce wa tunanin ta,tuni tayi luf jikin ta ya mutu,se da ya tabbatar ta nutsu,sannan yace tayi hakuri ta fara kammala secondary din ta tukunna,ya mata alkwarin ze Kai ta gida ,amman se ta maida hankali ta karasa karatu,tunda an kusa ai, befi saura watanni hudu ba suyi WAEC din su..
Nan da nan ta amince,sannan yace toh suje suyo wanka su dawo,dan wannan sabon su ne,kullin cikin wanka suke,se suyi wanka fiye da sau Ukku a rana.
Daga wanka na kauce na Basu guri,Dan Maina yau wasu sabbin salo yazo dasu,Duk Dan ya sake kwantar Mata da hankali,ai kuwa hankalin ta ya kwanta,Dan hatta da batun su Baffa seda Mairo ta mance da shi..

YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomanceLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...