WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
DIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Saturday,6th june. 2020
(5)
***************
Maina ma cikin tarin shi ya sayo zani turmi guda,ya sai gyale,da hoda da yan kunne da takalmi,harda 200 kudin dinki..
Be kasa a gwiwa ba ya tashi Kamalu dan Baba Sale kanin Ubale ya aiko shi gidan su Mairo, da ledar kayan sallah da yayi wa Mairo din.
Kamalu da Maina kusan sa'anni ne duk da a yanzu zasuyi 23 ,dan shima kamalu a rumfar su shine na karshe,duk da baba sale nada yara 6 kuwa..
Dama shi maina bada wuri yazo ba,seda kusan Ubale ya girma sannan ne ya same shi ..
Su kuma su Malam Ubalen su uku ne Inna gaji da Malam sa'idu suka haifa, kawu Ubale ne na fari,se kawu sale
sannan inna Zaliha ..Kawu Ubale dan sa daya jal Maina,
Se kawu Sale me yara shidda ,Habu,bahari,sa'ade,shamsiya,Audu se kamalu.cikin yaran kawu Sale,kamalu ne kawai beyi aure ba.shi da maina kenan .
Inna Zaliha ma me diya 4 ,Rabe,bashari,se Hajara da sakina.yaran inna Zaliha ma duk sun yi aure Kuma duk sun hayyafa.
A gaba dayan wannan zuri'ar ,mazan gidan kowa ya tashi aure guri ake tsaga mishi yayi dabe yayi rufi ya zauna da iyalin sa .
Matan ne suke aure a waje tunda dai suma gidan wasu suke tafiya.
A cikin su kuma harda masu mata biyu,uku,hudu,ga ya'ya nan su tattaba kunnen Malam sa'idu sun cika gida dam abun su.se ya zamana wannan suna shiri da yan nan wanchan basa shiri da yan chan..wato anyi groups kenan tsakanin faccalolin da kishiyoyin.
Shi dai kawu Ubale na shi kallo,dan shi dai dan sa daya,kuma baya shiga shirgin kowa,kullum harkokin sa yake yi ,yaje bakin kasuwa ya tura kurar ruwan sa..
Banda ma yanzu ya rage kuzari tunda ya farga ya gane ya kamu da son Mairon gangare ,so kuma me tsanani.duk da ma ana cikin azumi ya gansu da Talan wata rana,shine daga baya ya sake ganin Talan ita kadai shine har ya bata kudi yace kuma ta gaida Mairon.
Da alama kuwa da gaske yake son ta ,gashi kuwa yayo siyayyar kayan sallah ya aiko mata ..
Ko da yake kamalu ma yana dinki a shagon Masu tela.
Duk suna da abun yin su..sauran kuwa manya ne ,daga me diya hudu ,se me biyar se me diya har tara suna dai nan a gidan gandu abun su ..
(Wannan kadan kenan daga tarihin gidan Malam sa'idu,dan Ku fi fahimta)
Yawwa..shi kamalu shi yaje gidan su Mairo ,ya aika aka mai iso gun Malam iro .
Da yake baya fita ,sedai in yayi baki,su shigo rumfar shi,haka kuwan yau ma akayi ,se ga Kamalu ya rafko sallamar sa ya shigo yana ta sunkui da kai.
Ko da yake su yan hayi ne,su Mallam iro kuma yan gangare,amma duk sun San junan su,tunda ba wani nisa ne tsakanin su ba.
Wani ma kwata ce ta raba unguwa,wani kuwa dalili ne
Gaida Malam iro kamalu yayi,dake ma da yamma yaje.nan suka gaisa ya ke kara tambayar Malam iro kafar sa..
Be tsaya wani kwana ba yace .."Baba...daman Sako ne na zo da shi.."
Ciro ledar yayi ya ajje yace .."Na Mairo ne aka aiko ni in kawo .."
Yana fadar haka Baffa ya gane cewa ,iri ne na gidan shi ake nema..yayi farin ciki duk da ma besan waye me so ba tukunna.kuma ba wai neman auren bane yasa shi farin ciki,Ah ah,kawai dai ko ba komai anyi masa karamci tunda ta hannun shi aka fara biyo wa .wannan shine mutumci.
Ba kamar yanda yanzu abubuwa suka chanja ba,mafi yawancin masu neman aure,yarinya suke fara nema..
Duk da kai tsaye ba laifi bane,daman zamanin ya juya ya koma hakan,Amman a mutumce fara Neman iyayen yarinya yafi akan neman yarinya kai tsaye tun balle yan kankana irin su mairo ..dan daman yaran kauye basu cika girma ba,dan a burni ma Mairo kallon yar shekara 7 za'ai mata..
Nan Malam yai fara'a yace .."Ah ah,haka kau,waye me sakon toh?"
Dan shafa kai kamalu yayi yace .."Daga rumfar Baba Ubale ne ..Maina"
Dan murmusa wa ya sake yi sannan yace .."kakkak Allah sarki,toh kayi wa Malam godiya..Allah ya saka da alheri.."
Daga nan sukai sallama,har Malam yana ta kokarin bawa Kamalu tukuici ,Amman kamalun yaki karba.
Shiko maina yana gida yana jiran kamalu ya dawo.
Isar Kamalu gida ya baiwa Maina labari wanda ya dadawa Maina rai,dan da alama in ya fito nema za'a iya samu a bashi..
A gidan su Mairo kuwa ,ita Inna duduwa dai bata ce komi ba,Amman kam abun yayi mata kusa,a nata ganin duka duka nawa Mairon take ?
Kuma a ra'ayin ta tafi son yaranta su gama ta gaba da firamari sannan suyi auren.
Yo ina amfanin auren da ake yi a kauyuka wanda yawancin sa da "day" ake kiran sa.wato auren jeka ka dawo,kuma dawowar ma harda tsaraba ko ta ciki ko ta goyon ciki?
Gashi nan a nan kauyen nasu, za'a aurar da yara fiye da goma sha a kaka.Amman kan kaka ta zagayo fiye da 6 sun dawo zawarci,kuma duk irin su mairon,wasu kuma za'a kai har a haihu.se a haihuwar ake mutuwa dan akwai high rate of maternal mortality.
Sannan yanzu ace wai Mairo ce har aka fara mata aike me nuni da ana son fara neman auren ta..yar Mairon???
Hmm ..Shi dai Malam iro ya fuskanci innar ba tayi na'am da aiken ba..Haka kuma se shi ne ya bude mata kayan ta gani dan kunya ko kallon kayan ta kasa yi,ba shakka yayi kokarin siyan kayan ta yadda.
Amman dai gaskiya ita bata jin yiwa Mairo aure yanzu,yo salon ma mijin yaje yayi ta cin zalin ta?
Haka dai take ta tunane tunanen ta ,ko da yake shi Malam yasan ra'ayin Innar akan karatun yaran nata ,kuma shima yayi na'am da hakan tunda yasan
Ko ba komai in sukai karatun zasu amfana da shi wata rana .
Kwantar mata da hankali yayi yana tuna mata cewa .." Bafa neman aure suka zo ba,kawai dai suna so asan da su ne .."kuma dai innar mu,naga baka maida hannun kyauta baya".cewar Mallam
Ya Kara da .."in banda abinki ,nima ai nafi son suyi karatun sannan ko dan gaba sabo da hali irin na rayuwa"
Da haka ya samu ta kwantar da hankalin ta sannan suka rufe babin bayan ta sanya wa abun albarka in har da alheri a cikin sa. . .
Toh Bari mu tsaya anan ..kashi na gaba zamu tashi insha Allah,meye ra'ayin ku game da su Mairo din?
TBC.........

YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
Roman d'amourLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...