(10)

63 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Tuesday, 21th July. 2020

(10)

***************

Cewa yayi .."Inna taji shiru ko.."

Daga kai Hasi tai tana juya wa ta shige zauren su.bin bayan ta yayi yana sallama..

Inna ce take amsa sallamar yayin da ta kara sa zura hijabin ta ..

Zama Mato yayi suka gaisa da inna.nan ne inna ta sake cewa .."Ya mai jikin Mato?

Kafar sa ya Dan sa wa hannu ya kade sannan ya gyara tsugunnon sa ya karyar da wuya yana cewa .."Kai ai yaji jiki bawan Allah,be ma San sadda aka kai shi gun me ganye ba.kakki ciwo baddadi..Amman jikin da sauki Alhamdulillah..da yake ma me juriya ne da kan shi ya tafi gida shi da Dan uwan shi Kama.."

Da yake Mato irin mutanen nan ne masu zuzuta lamari,se gashi se wani jirkice kai yake yana kuma jimanta lamarin

Ajiyar zuciya inna ta yi Dan tabbas hankalin ta ya tashi,kawai Dan mutane yazo ya mutu a kor gidan su?

Hamdala tayi a fili tana cewa .."har naji Dan nutsuwa..yo Mato nan Inda wani Abu ya same shi da cewa za'a ruga yi a kor gidan mu ne.."

Cewa yayi .."eh inna,Amman duk da haka ai an San tsautsayi ne hakan,ba Wanda ze kawo fiye da hakan a tunani nai ma.."

Sama ta kalla tana cewa . "Hmmm kai dai Allah ya kiyaye na gaba ..gobe kaje ka gano jikin nashi ko ,tunda dare yayi yanzu .."...

Cewa yayi .." Hakan ne kuwa ,gobe da wuri zani na dubo shi insha Allah.."

Da haka sukai sallama da Mato bayan yar hirar yau da gobe da suka taba..

Ko da yaje washe gari  cikin sa'a ya iske Maina kwance ,se Mato yayi tunanin duk jikin ne .nan kuwa tsabar gajiya ce ke nukurkusar Maina.Dan sun fara Daben su (Gini).
Wanda a al'ada irin ta kauye a gidan gandu daman haka ake yi.duk Wanda ya tashi aure se a shata masa guri yayi dabe ya zauna nan ciki.

Hakan ce ta kasance wa Maina da Kama .haka suke haduwa da abukkan su suna yin Daben tare Wanda dama kuma al'adar samarin kauye ce yin hakan.Ma'ana duk sadda saurayi ya tashi aure,da anzo kan dabe se abokai su hadu suyi aikin Daben tare .Haka kuma ake rama wa kowa in nashi ya taso..

Wala'Allah hakan suka fi son suyi,tayi yu kuma sauki suke nema wa Kansu ne ..sedai kuma Maina ya tsiro da abun da ba'a taba yi ba a tarihin gidan su,wato yin zagaye na dakin ka ,da kuma yin gewaye na daban..Se gashi yanzu Maina ya ce lallai shi se ya zagaye gurin sa sannan yana so yayi musu gewayen su shi da Mairon shi daban..Maganar da taso tada zaune tsaye ,Dan Ubale dai ya yarda da wannan shawarar ta Maina,sedai kuma hausawa na cewa .."in maye yaci 'da ya manta.."
Watakila Ubale ya mance sanda yayi uwa yayi makarbiya ya hana Audu yin wannan zagayen na dakin sa sadda ya tashi auren ,ya kara da fadin .."Ba Wanda ya isa ya tsiro mana da wani Sabon Abu Wanda bamu saba dashi ba ,haka nan muka tashi muka ga ana yi,kuma haka nan zamu dore bame yi mana chanji.."

Audu na ji na gani haka ya fasa yin katangar da yaso yayi.Kawai shi kuma Ubale ya mance da wannan batun,se gashi Maina Na zuwa da batu Ubale ya amince ..nan kuwa yan hamayyar fili da na boye suka runga yada maganganu Wanda har ya isa kunnen Ubale,dole kuwa kanwar naki ,Maina ya hakura badan yaso ba.Dan ba abun da ya tsana irin ya Ruga ganin matan yayyen su suna Shiga wanka ko suna fito wa daga wanka,ko da daman an San mutanen kauye da zama ba Riga ,wasun su ma haka suke sake kirji ragajaajaa suyi zaune tsakar gidan su,ko ma kor gidan..

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now