WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Sunday, 12th june. 2020
(7)
***************
Koda Innaji ta samu Maina da batun karatun Mairo ,abun be mishi dadi ba ,Amman yace indai an bashi ita ze iya jiran ta ,ko kuma ya yadda ta ruga yi daga dakin ta. .
Koda yake ma Malam sa'idu ya shiga maganar ,inda da kan shi ya taka har kofar gidan Malam iro,yayi sallama aka masa iso, Sannan ya roki alfarmar a basu auren yarinya ,kuma karatu zatayi shi a dakin ta ..koda ma ba'a haka aka so ba.Amman duba da yadda Malam sa'idu ya taka da kan shi ,gashi tsoho tukuf dashi,ai dole a karbi kokon barar sa.baya ga haka ma shi Maina ai sha lelen gidan su ne ,kakanni naso iyaye naso ...
Bayan sauraren Malam sa'idu ba yadda Baffan Mairo ya iya haka nan ya furta cewa ya amince ya kuma bada Mairo ga Maina..
Dan ko ba komai Malam iro yasan diyar sa Mairo tayi dace da miji me zafin nema,da jajircewa..
Malam sa'idu be kasa a gwiwa ba ,seda ya San yadda yayi suka zabi lokacin biki ,rana kuma daga baya a tsaida ..lokacin bikin wanda ya kama a Kakar bana .. Hallau kuma yace Maina ze zo ganin Mairo..
Bayan Malam sa'idu ya koma gida da labarin me dadi a kunnen Maina da iyayen sa,da kaka Innaji,se murna ..
Dan Maina ma kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha ..
Haka ya tashi ya fara neman kayan da ze sanya ,ba bata lokaci ya fiddo wata shaddar sa me kyau ya hau wanki ,yana gama wa ya shanya Sannan ya samo dutsin guga na Karfe ya ajje ..kayan na bushewa ya same su da guga ..kayan sunyi kyau dai dai gwargwado ...
Allah Allah yake dare yayi ya samu yaje tadi..ilai kuwa da Daren yayi haka ya feso wanka kai ka ce ze chanza fatar sa,ya fito ya shafa mai ya sanya kayan sa,kana ya kawo hula ya murza. Koda ma hular duk tayi laushi ta kwanta Amman ta mugum karbar shi ..
Turaren shi ya dauko dan duri ya tsiyayo ya mammaka a jikin shi,kan kace me daki ya dume da kamshi, koda ma dai kamshin me bala'in arha ne ,Amman a dai dai level dinsu yayi abun kai..Dan ko cikin samari abokan su ansan Mainan na daban ne
Haka ya rufe yar kwalbar sa Sannan ya jawo wasu takalman sa,su din ma na sallan sa ne ,irin yan kirar hannu dinnan ne masu arhar gaske ..ya zura su a Kafar sa..
Se ga Maina ya fito a Dan kwalisan sa ,yayi kyau sosai ,dan wallahi a hakan shi, shi din miji ne na kera sa'a ,dan da yawan yan Matan hayin su suna nan sun shirya sun lashi takobi,jira suke kaka ta zo Maina ya fidda su su zama taurari..
Wasun su kuma har fura suke dama mai su bishi bakin kasuwa ,da yawa suna son Maina ,Amman kuwa shi duk basu mai ba..
Budurwar sa daya da ya so me suna sha'awa kuwa rasuwa tayi ,tunda ga kanta ne be sake samun wadda ta masa ba ,se Mairo da ya gani bako jima wa,Amman kaunar ta tayi wuf ta Kane masa zuciya ..
Dan Maina irin mutanen nan ne,in zeyi kawai zeyi ,in ba zeyi ba kuwa bazeyi ba,Amman shi ko kadan baya missing opportunity ,baya Barin dama ta wuce shi..
Yo ba gashi ba,har ya aika an nemo mai izini,har ma an bashi?
Hmm Maina kenan ,a gaba zamu kara Sanin waye Maina..
A yanzu kuwa bari mu nufi zance ...
Baya kadan
Bayan tafiyar Malam sa'idu ,Baffa ya kira innar Mairo ,nan ya zaunar da ita .cewa yayi .."wai niko innar mu anya kina ji dani kuwa yanzu ?"
Dan kallon shi tayi kadan saboda kunya ,shima kallon tayi shi ne domin tana son ta fuskanci fuskar da zancen nasa yake dauke da ,gefe ta kalla bayan taga wasa a fuskar tashi .se tace .."yo ni kuma ,wace ni?"
Dan dariya yayi ,yasan daman amsar ta ta bata wuce hakan ,se yace .."Toh iyy man innar mu,wai ni yaushe Rabin da a damo mani dawo a kawo Mani,hallau a ruga bani ana mun kallon soyayya ne ?"
Ai tuni inna ta kwanta jikin sa tana boye fuskar ta ,chakulkuli yayi mata kadan ,ya barta tana dariya ,dan yana tuna tun tana karamar ta bata son chakulkuli ..kallon ta yake cikin so da kauna ,Sannan yayi gyaran murya yace . ....
"Ahp yanzu ana ta dariya,Dana gaya maki wata magana kuma ki hau hawaye ko? "
Dan kallon shi tayi tana dena dariyar tace.. "Wace magana ce ,Allah ya sa dai lafiya .."
Cewa yayi .."Lafiya lau,nadai miki laifi,Na bada Diyar ki bada sanin ki ba, yo ban samu damar yin shawara Dake ba tunda Mahaifin Malam Ubale yayi tattaki yazo da kan shi .."
Kallon ta yayi yaga bata chanja fuska ba ,se ya ci gaba da cewa .."neman alfarma yayi,ni kuma bazan iya kin yi mar wannan alfarma ba ,tunda nima matsayin uba yake gare ni.."
Nan ya kwashe yadda sukai da Malam sa'idu ya gaya mata,da mamakin sa se kawai yaga tayi addu'ar zabin Alherin Allah.
Baffa yaji dadi sosai ba shiri ya rungumeta ,dan ma tana ta nokewa ,nan ya shi mata albarka, dan wallahi ya zata za ta botsare taki,tace ita se diyar ta tayi boko,ya zata zata hura masa wuta saboda daddeden burin ta ,Amman se gashi ba tayi ba,sema Addu'a da tayi. .Nan aka tsunduma fagen kauna.
Bayan Nan kuma inna ta hau maganar yadda zasu iya aurar da diyar ta su bayan suna cikin wani hali na rashi..
Malam kuwa dariya yayi yace .."kar ki daga hankalin ki duduwa, Allah yana nan ,kuma dashi muka dogara ,ze ruhwa mana asiri .."
Cewa tayi "Toh Allah yasa .."
A ranta tana jinjina karhin hali irin na malam din,Amman tunda ya ruga yace Allah ai batu ya kare..
Cigaba
Karfe 7 na Daren ranar tayi wa Maina a kofar gidan su Mairo ,wata yarinya ya gani ya aika ta tace wai ana sallama da Mairo inji Maina ..
Tana fada inna tace jeki ce kin fada,
Tana fita ya bata yar biyar,ai se tsallen murna
Maina na tsaye yana tsumayin Mairo ga farin ciki fall da rayuwar sa
A cikin gidan kuwa inna ce ta rasa ma me zatayi,chan dai tace .."Hasi,Mairo leka kuga ni.."
Baffa na jin su ,yana yar dariyar yadda innar tayi maganar ta ta da irin tune din "ya zatayi" se gata tayo sallama ta fado dakin..
Yana ganin ta ya gumtse dariyar tasa ,nan kuwan tace masa .."wai anzo gun su Mairo .."
Ce mata yayi .."Ah ah ,anzo?,waye yazo kuma?"
Yana sane fa,so yake dai yadan tokare ta,se cewa tayi.."yo yaron wajen Alaji Ubale man .."
Dariya yayi yana cewa .."yo kunyar surukin naki kike ji kuma da bazaki fadi sunan sa ba?"
Ita dai shiru tayi wa Malam tana tunanin me ma Mairon zata ce a wajen hirar ? Dan ma dai tace su tafi da Hasi tunda Daman a al'adar su ba'a tadi saurayi da budurwa se da yar rakiya..
Su kuwa su Hasi tini suka fice wajen ,suna leka wa suka ga Maina ne ,nan suka tsaya wajen, Hasi ce ta fara gaida shi Sannan Mairo ta gaida shi itama
Toh fa ,anzo tadi gurin su Mairo,koya hirar tasu zata kasance ?
Se an biyo mu a ci gaban littafin ..
Kuna ko jin dadin wannan labari?
TBC..............
YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomanceLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...