WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Saturday, 24th October. 2020
(34)
***************
Mairo kuwa tunda ta rufe gidan ta Takoma kan jakunkunan nan ta ruga bude su daya bayan daya.
Ko kafin wani lokaci tunda Maina ya gaya Mata nawa ya siyo musu dilar,se ta musu kudi,ta ware masu kyau,da tskaiya da karshe,ko wanne tai Masa kudi yadda tasan zasu samu ribar su..
A yammacin ta fitar dasu shagon su.da take an kusan Sallah lokacin.nan akayi ta diba,wasu sun bada kudin su a lokacin,wasu kuwa Kamar yadda al'adar Mairo take iya sati daya be kake daukan kayan ta ka kawo Mata kudin ta.
Isar Maina gidan Haidar ba wata wata ya fiddo wannan kudi ya Mika wa Haidar,ko Haidar seda gaban shi ya fadi,Nan Maina yace ma sa..
"Kasan munje kwatano da oga,se make na siyo dilar jakunkunan Mata,a ranar ma aka sauke su,shine fa yau Ina bayan gida Mairo ta Kira ni tace a kasan wata jaka ta tsince su..
Shi yasa nazo Nan na kawo maka,nasan kudi ne ,Amman ban san kansu ba..
Haidar Yana ta mamakin wannan kudira ta Ubangiji..
Se ya tsinci Maina na cewa.."toh yanzu in Zan maida musu harda jakunkunan Zan mayar ko kuwa?"
Wani kallo Haidar yayi wa Maina Yana jin kamar ya mangare shi..yace .."wannan wani irin shirme be,wannan ai mallakin ka ne Kuma,suma tsuntuwa ce sukai in su suka gani,Kuma baza su maida ba,Dan wannan kudin Turai ne,dan Haka tunda Kai ka siyo dilar,Kuma kayi tsuntuwa ciki,sun zama naka..ko once na Mairon ka.."
Jikin Maina har rawa take Yi..
Haidar yace .."Kuma wannan kudin da kake gani.ko wacce dayan su mazaunin Naira Dubu talatin da shidda da dari biyar take..
Suman zaune Maina yayi,tuni kwalla suka zo Masa idon sa. Cewa yayi.."Toh ya akai Haka,toh yanzu ya za'ai.."
Haidar yace .."Yadda za'ai wahala ta kare maka.Allah ya dube Kai Maina,Kuma ka chanchanci fiye da haka.Yanzu Ni shawarar da Zan baka itace ,a Kai wannan kudin banki.dan kasan zaman kudi Haka a waje hadari ne.."
Maina dai se jijjiga Kai kawai yake Yi...Daman da kyar ya siyo wannan dilar ta jaka.Allah dai yasa ze siyo ta kawai.Ashe arzikin da be ciki kwance be sani ba..
Wuraren 3:50 Maina da Haidar suna cikin Banki.an bude wa Maina account .Amman se aka zuba kudin a bankin Haidar tunda shi ya Saba saka makuden kudade a bankin shi,tunda babban likita ne ..a hankali se ya maidawa Maina cikin account din shi..
A mota suke shawarar yadda za'ayi da kudi..Maina yace a Kama Masa shago ya tuga siyo dilolin gwanjo Yana Saida wa.Hakan kuwa akai.dan kafin Sati biyu an samu shago a Chan kasuwar sabon garin Kano.
Tuni ya fara hada Hadar sa.dan Bilal ma ya bar ganin Maina.kuma Haidar be gaya wa kowa ba shima..
Daga Maina,se Mairo se Haidar kawai suka San wannan sirrin..
Maina ma seda ya baiwa Haidar makuden kudade..
Ana nan ana nan.Haidar yace wa Maina ya samu ya samu muhalli..ba musu Maina ya ce ya yarda..A unguwar nan hotoron ya samu ya siyi wani gida.ya rushe shi aka fara zabga gini.inda Bilal ne take ginin Amman ya zata na Haidar ne..Maina ko zuwa baya yi.yana chan Yana fama da shagon shi.
![](https://img.wattpad.com/cover/238861444-288-k943635.jpg)
YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomanceLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...