(2)

161 6 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

5Th April. 2020

(2)

Malam iro dan fillo mutumin Kauyen Burum ne wanda ya kasan ce mutumin arziki, uban kwarai, mijin kwarai, makocin kwarai..

Mutum ne shi wanda ya kasance me zuciyar neman na kai,mutum me wadatar zuci,mutum me zuciyar taimako.

Malam iro kowa yasan shi da taimako a garin na burum, tunda ba laifi yana da dan rufin asiri dai dai gwargwado.Dan ko  akalla yana da sana'oi kamar uku wanda ya dogara dasu.

    Na farko yana faskare sannan yana yin saqar hula kuma yana aikin lebura.

Malam iro yana da mata daya me suna inna duduwa, sannan suna da yaran su mata su hudu ta farkon ita ce Mairo, se Hasina se salame sannan hansai.

kuma duk gaba dayan su mairo ke da 13 years, se hasina me 12 se salame me 11 sannan yar auta hansai ita kuma 9 years.

Kusan hansai ce kawai aka samu tsiran shekaru tsakanin ta da sauran.dan Inna duduwa kan tayi yaye ma ta samu wani cikin.

Iyalan iro dan fillo mazauna Kauyen Burum ne kamar yadda na fada, haka dai suke zaune da dadi ba dadi, suna yin duk abunda ya samu dan rufawa kansu asiri tunda inna duduwa jajircacceyar mace ce,gata kuma tsayyayiyar uwa.

A halin da suke ciki yanxu bara ce kawai basayi dan ganin sun samu abinci na yau da gobe, duk da ma tun daga kan inna har su mairo sunfi damuwa da hansai tunda itace yarinya. Dan gaskiya akwai shakuwa da kaunar juna a wannan gida na Malam iro,ga tsantsar soyayyar dake tsakanin Malam iro da inna duduwa me cike da farin ciki da nishadi,ga tsantsar biyayya da kunya ..Dan daman dukkan su Fulani ne masu kyau da mutumci.

Kullum suna cikin neman aiki, sune wankau, aikatau, surfe, debo ruwa, su shara da wanke-wanke a gidan masu hali a garin, hatta reno yi suke, haka in aka hada kudin bautar da suke yi in ya isa jari sosai inna take kosan yamma, awara, wainar fulawa,yar bagalaji da dai  sauran su .duk dan rufin asirin su kuma ALHAMDULILLAH...

Me karatu zeyi mamakin yadda hakan ya kasance, duba da cewa kun karanta yadda malam iro yake jajircewa kuma me sana'a uku ko?, toh tabbas haka ne.sedai rashin su ya samo asali ne daga sanda tsautsayi ya fada wa Malam iro Wanda diyoyin shi kewa lakabi da "Baffa".

kamar dai yadda bawa baya wuce wa kaddarar sa ,hakan ne ya samu Malam iro, Dan kuwa a sana'ar sa ta faskare ya samu tsautsayi wanda ya sare kafar sa.

Tun daga wannan lokaci ya samu matsala, dan se kafar tayi ta ci,tayi ta ci.duk kuwa da ana ta magani amman abun yaci tura.

A hankali kafar malam iro ta daina aiki kuma tana ta ruwa har kawo yanxu da ya samu kusan shekara a zaune.

Abunda basu sani ba shine,mallam iro yana da ciwon sukari,wanda wannan shine dalilin da yasa kafar taki warke wa.

Tayi yu ko dan saboda maganin gida kawai ake tayi mata,ba tare da an hade da na bature ba?Allah dai Masani.

Bayan ya samu wannan lalurar kuma ne se mutane suka juya mar baya duk irin dawainiyar da yayi dasu a sanda yake da lafiya, abun haushi da mamaki ma shine cikin wanda suka juya mar baya ma harda
Yan uwansa,da wasu daga cikin mokatan sa,da wanda yake bi bashi, kuma sau da dama inna tasha tunkarar su wanda mallam ke bi bashi din ko dan a samu a cigaba da yin musu magani ma , amma sunki bayarwa ku kwace nonon uwarsu suka sha..har malam ya gaji yace wa inna ta kyale su in sun biya bashin dan kansu.in sunki ma Kansu..

Hakan kuwa akayi,Dan tun daga wannan lokacin Inna bata sake ko yin maganar bashishikan da Malam din ke bi ba.

Suma a bangaren su Wanda ake bin bashin,sun samu sa'ida sunci bashi sunyi kwance abun su..

Sedai kamar yadda na Allah baya kare wa,a cikin sauran makotan akwai masu kokarin taimakon iyalen Malam kama daga kan Bushashan kanzo,zuwa kwananen abinci,Dan ragowar koko da sauran su..

Duk da ma bawai su Malam iro bane suka fi kowa talauci a Dan tsukun su,ah ah,a zahiri ma kan Malam ya kwanta jinya,su suka fi kowa wadata..sedai tun daga kwanciyar Mallam iro suka koma abun tausai..

Dan duk da zaman su a talakawa,iro har kayan sallah yanai wa yaran makota in dai Allah ya nufa ya kuma hore,sannan su Mairo har boko da allo suke yi..

Haka kuma in Malam ya shiga birni yana sayo masu alawar birni,sannan kar ku manta da yadda duk makota a gunshi suke rancen kudi.    .

Toh dalilin da yasa yanzu ake taimakon su ,domin yanzu yana kwance ba Sana'a,sannan sanda yana da lafiya shima haka yake yi..kai shi kam ma Malam iro har shinkafa yake sanwa makotan shi indai ya samu sarari,duk sanda suka dafa shinkafa se kaga anbi makota da ko yar yaya su maida mugun yawu..

Bari mu dakata anan, mu hadu a kashi na Uku,Amman kafin haka,ya kuka ji wannan labarin?

TBC..... .......

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now