WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Thursday, 23rd July. 2020
(12)
***************
In ko suka zo suka iske yarinya ta watsar da budurcin ta se ya zama abun magana da gori,haka zakuga innonin amarya sunyi sanyi kalau dasu,su kuwa iyayen Ango se suyi ta shuna su da baki suna yada magana.Abun ka da kauye ,komai da girma ake daukan shi ...
Toh a yau dai shigar inna Salmai dakin Kamalu ta tadda Hasina jikin ta tayi zafi ,ga wani sarawa da kanta yake ,ga idanu sunyi jajur sun haura sama ,katifa kuwa inna salmai na kallo bata bukatar Karin bayani,sannu ta fara wa Hasina sannan ta saki guda..Ayyiri Yiri yiri.....
Nan da nan matan bakin rumfar suka dau guda wadda ta karade gidan baki daya.da wannan ta dire se wannan ta dauka..a haka har kunnen iyayen su Maza da basu riga sun fita masallaci ba,dan daman se sunji sakamako zasu fita..toh da yake wannan amare biyu ne aka kawo.se sun saurara sunji an dauki wata gudar tukun ..
Tun kafin a kawo kan Mairo har wasu matan sun iza icce sun daura ruwan wankan Amaryar Kama an fara kokarin gyare ta..
Tuni Inna salmai ta yo rumfar Maina ,ta shigo ta tarda Mairo tana kwance Amman idanun ta rufe,Asali ma bacci take .hayaniyar wannan ce ta tada ta ,se kawai ta ci gaba da kwanciya ,zuwa Inna salmai tayi ta kai hannu ta taba ta ,jikin ta ba zazzabi,dan haka inna ta sake daga fitilar ta ta haska kan gadon ,jikin Mairo ta fara kallo sannan ta duba kan yar katifar ,nan ta sake zabga wata gudar,tuni gidan ya sake kachame wa.ko da ma wasu irin su Uwani su Ladidi sun so suji Amaryar Maina fanko ce ,se gashi ba haka ba..shi yasa ma suka ki yin gudar dakyau su..
A wannan lokacin kowa ya sauke ajiyar zuciya sannan masu zuwa Masallaci suka fice..
Kan wani lokaci har an gyara amare an tsuma su da ruwan dumi da jike jiken gargajiya ..wannan ruwan dumi shi yasa su bacci ,nan suke ta bacci har innonin su suka zo.Tun daga yadda aka tarbe su ma sun San anyi barka,haka suke ta yiwa juna barka sannan suka tafi gida da murna suma ..
Se wajejen goma su Kama suka dawo,lokacin ne suka tada amaren su zasu yi kalaci..kalacin nasu wanda aka toya musu kwan zabbi ga shayi da burodi..
Nan suka zauna suka ci kayan su tare su hudu,Hasina Allah Allah take suyi magana da Addar ta ,dan ta ma fi damuwa da Addar akan ita kanta..
Su na gama cin abinci suka sake fita su angwayen ..dan makota se zuwa suke da baki ,se kace ba jiya akai bikin ba,ko dama daman gidan cike yake da yan uwa ,Wanda basu kai ga tafiya ba ..dole su Maina suka sake tafiya gun Abukkan su .su kuma zasu tafi gidan iyayen amaren su Gaida su.su yo musu godiya..
Fitar su Maina Hasi ta sake matsowa tana kama Hannun Mairo tace .."Adda .."
Nan da nan se hawaye a fuskar dukkan su su biyu ,kuka Mairo ta fara tana kauce wa tuno yadda ta sha wahala a Daren jiya.tayi imanin cewa bata taba shan wahala me makamanciyar haka ba duk rayuwar ta ..har bata so ta tuno sadda taji wani Abu yace .."tus" Wanda ta tabbatar Abu ne taji karan fashewar shi a cikin jikin ta ..
Kara matse Hasina Mairo tayi tana cewa .."Hasi inna,innar mu .gida,gida nake so Hasi.."
Ita ma Hasin kukan take ,haka nan kuma duk baki irin nata da masifa da karadi ta ji ta karaya..nan tace .."Nima Adda ,gwamma muyi tafiyar mu .."
YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomanceLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...