(30)

43 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Sunday, 18th october, 2020.

(30)

***************

A dai dai wannan lokacin Maina da Mairo sun dade da aure,Amman har a yau dai mairo bata taba koda batan wata ba,a yayin da hakan ke faruwa kuwa,Basu taba maida hankali akan hakan ba,da son ganin dalilin da yasa haka.

A wani lokaci Chan baya,Maina ya dan ruga samun damuwa game da rashin haihuwar su,sedai hakan be sa yayi wa Mairo magana ba,toh abun biyu ne,Dan kuwa Mairo ma ta dan fara gajiya tare da damuwa game da rashin haihuwar ta.tun balle da sukan zauna da Humaira wadda ta kusan aure,a inda suke hirar rayuwar aure tare da samun girbe shukar soyayya inji ita Humaira kenan.Toh abun ka da Dan adam,wannan maganganun sun fara tasiri a zuciyar Mairo,duk da dai Bata taba furtawa ba,Amman tana daf ta yin magana dan tana son itama taga ta haihu..

Wannan kenan..

******

Maina ya samu lafiya ras garas a hannu da goshi,sedai goshin yayi tabo wanda kuma zasu cigaba da rayuwa tare da tabon sa,Koda ma tabon be Masa Muni ba,Amman Kuma kana ganin Maina zaka ga alamun tabon a bisa goshin shi..

An samu akalla wata biyu Maina na komawa asibitin dan tabbatar da lafiyar sa,sedai ana haka Haidar yayi tafiya zuwa umraah.daman Kuma bangaren karaya da ban nrme Hadi da Duk wani abu da ya shafi kashi.saboda haka ya cigaba da zuwa nan asibitin ana duba sa kamar yadda Haidar ya bada umarni.

A gefen Ummi kuwa,tun tana daukar soyayyar Maina a wasa,har ta Kai ta kawo ta gane cewa abun fa bada Wasa bane ba.dan kuwa kullum da tunanin Maina take kwana Kuma da shi take tashi.

Kuma ba wai dan bata da saurayi bane,kawai dai dan dama dukkan samarin nata ba na aure bane,Kuma an kasa gano dalilin haka,gata da farin jinin samari,Amman Duk Wanda yazo akai Mai maganar ya fito se ya tsere,a Sakamakon haka ta dena Sanya kowa a zuciyar ta,Duk Wanda yace Yana son ta Bata kinshi.sefai Kuma Bata wani zafafawa.

Amman Kam a wannan karon ta fada cikin kogin soyayyar Maina,ita ba abunda yafi daukar hankalin ta irin yadda taga kirjin nan nashi Kamar wani zaki,gashi kullun mafarkin ganin kanta take a kirjin shi,sedai Bata San yadda zatai ba,gashi ko da haukanta bata Isa yiwa Ya Haidar magana ba.bata San yadda zatai ba,dole yasa ta samu kawarta da maganar a office..

Zaune suke daga kan table inda suke office dinsu na mutum uku ne,ma'ana kowa da table din shi a cikin office din,na ukun nasu namiji ne me suna Hayatu,Wanda shima Hayatu ba karamin son Ummi yake ba,Duk da ma Yana da mata harda yaran su biyu,amman hakan ai ba aibu bane,sedai dan kawai dai bewa Ummi bane ba.

Kawarta me suna Amal,ita Ummi ta zayyanowa Labarin Maina da yadda ta kamu da soyayyar shi,Kuma tace a halin da ake ciki ma ta fara galabaituwa da tsananin rashin Sanin makama ko Kuma madafa..

Dan hura iska Amal tayi tana juya ido,kallon gefen Hayatu tayi Wanda take zaune Yana sauraren waka a kunnen shi,Wanda har su suna iya jiyo me take ji,hakan ya tabbatar musu da cewa baya sauraren su,kallon Ummi ta sake Yi tace.."Babe,gaskiya wannan abun Kamar fa kin debo da zafi.."

Kallon Amal Ummi take,yayin da idon ta yayi rau rau da hawaye.Dafa ta Amal tayi tace.."calm d,ba kuka zakiyi ba,but come to think of it,kince baki San ma a inda yake da zama ba,sannan ko sunan shi baki sani ba,a karshe ma kuma kince baki Isa tunkarar ya Haidar da maganar ba..toh ya kenan za'ai?"

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now