(4)

102 6 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Sarurday,6th june. 2020

(4)

Bayan an sha ruwa ,dukkanin iyalen Malam iro suna cikin rumfar su,nan ne Hasi tace wa Innar su .."inna Adda Mairo fa Talan ta kawo mata Murtala biyu tace wai Mainan Hayin gwarmai ne ya bata ,Amman taki ansowa .."

Kallon Mairon Inna tayi ta ga tayi narai narai da ido ..tace .."yo akan mi Maina ze aiko mata da har Murtala biyu?"

Hasi ce tace "yo ganin dama yayi man inna,ko rokar shi akayi?,kuma ai Talan ma ya bata nata ita ma .."

Dan shiru innar tayi ta na tunani,zatayi magana kenan Malam iro wanda su Mairo ke kira da Baffa yace .."Toh ba komai ,Allah ya biya shi.."

Kallon Mairo yayi sannan yace .."Mairama,me yasa ke baki gaya wa innar mu ba da kanki?"

Cewa Mairo tayi .."Ai inna bugu na za tayi.."

Kallon innar yayi sannan ya sake maida kallon sa ga Mairo yace . "yanzu ina kudin suke?"

Saurin cewa tayi .."ai ban ansa ba ,Talan na barwa kudin,nasan innar mu ta hana mu ansar kudin kowa shi isa na baro su gun ta .."

Cewa yayi "da kyau Mairama,Ku ringa jin maganar inna da kyau,duk wanda ya sake baku kudi kar Ku anso ,kuma da kunzo gida Ku fada wa innar Ku.."

Yana kallon su duk ya karasa maganar . da "Toh Baffa" suka amsa dukkan su

A haka suka ci gaba da hirar su,Amman dai inna ita a gunta wannan magana bata wuce ba.

Da ace Hasina ce da ta gama maganar haka,dan Hasina ko saurayi ne yace yana sonta ,zata tsaya ta wanke shi tas sannan ta na zuwa gida zata fadi..ita kuwa Mairo uwar miskilanci kenan ,yo sau dubu inna zata aiki Hasi kasuwar Hayin Gabas,Amman ko da wasa bata taba aikan Mairo ba.

Toh inna dai bata yadda magana ta wuce ba,so take se ta kwankwasa da kyau taji gaskiyar zance

Tashi Innar tayi ta fita daga rumfar se tace .."Mairo yaki nan.."

Tashi Mairon tayi tabi innar ta ..

Rumfar su suka shige ..nan ta kama hijabin Mairo tace .."me ya kaiki har Hayin gwarmai Niko Mairo?,Har Maina ya baki Murtala biyu,aikin mi wai to kikai mai har ya baki Murtala biyun?"

Zare ido Mairo tayi har ta fara kwalla,tace .."na rantse innar mu ba Hayin da naje,a hanyar dawowa ne fa Talan ta fadi mun taje Hayin shine fa ya bata Murtala daya,ni kuwa yace ta kawo mun Murtala biyu, Amman Allah inna banje ba.."

Ajiyar zuciya Innar ta sauke,ko dama tasan cewa ta bawa yaran tarbiya kuma sun dauki tarbiyar tata,Amman ai uwa dole ki tsaya sosai ki runga bincikar diyoyin ki,tun daga kan mazan kuma har matan..

Yo ba jimawa aka samu Nanan Barira da ciki anan Kauyen nasu,gashi har yau an kasa samo wanda yayi mata shi..

Nan innar ta sake ja mata kunne akan maza,ba ruwan ta da kowa ,sannan tace daga yau tana fada mata komai da kanta ,base Hasi ba,nan Mairo ta amsa da  "toh "

Sannan ta koma Rumfar Baffa,yana kallon ta ya gane ,dan yasan halin innar su ,nan kuma su Hasi suke ta bata hakuri suna goge mata hawayen ta kar ma dai Hansai auta,dan Adda Mairo ce uwar goyon ta..

Shi dai Baffa na kallon su yana jin sanyi a ranshi,yadda suke kaunar junan su abun ya wuci misali.sedai shi a ranshi yafi jin Mairo, dan duk cikin su itace me rauni,gata shiru shiru

Dan Mairo irin su sedai ka chuce su Amman ba bakin magana,ko cikin su yan uwan ta bata cika surutu ba se lokaci zuwa lokaci.

Amman haka suke zaman su ana hirar da ita da yanayin shirun nata..

Ba Dade wa suka tashi,dan dama sunyi Sallahr Isha'i.

Rumfar su suka nufa ,Inda ita kuma Inna tayo rumfar Baffa ,tana ta nokewa dan tasan yasan tayi wa Mairon sa fada..

Aiko tana zama ya kalle ta ,yace .."Sannu me wayo,wato kin zagaye kin yiwa diyata fada ko,anan kin yi shiru kamar magana ta wuce ,seda kika San yadda kika kira ta kikai mata fada.."

Kasa take kallo tace .."yo ai Baffa abun ne ya ki kwanta mun,aikin mi tayi da za'a bata har Murtala biyu? "

Ya gane  me take nufi,da tsoro Amman se ya share yace .."Yo Mairon ba kanwar shi bace,kuma ai Talan ma ya bata ..ki Riga kokarin kyautata zaton ki akan diyan ki,Allah ya kare su ,kuma muna rokon Allah da ya sake tsare mana su .."

Amsa wa tayi da "Amin"

Sannan yayi shiru yana kallon ta,shi yana mamakin yadda yake jin soyayyar Matar shi a ranshi har tsawon wannan lokacin,duk kuwa da cewa sun haihu har diya hudu..Koda yake ma ,rayuwa ce ba irin ta yanzu ba,rayuwar da me cike da karamci da Kara,Koda dai dama a ko'ina akwai na banza da na kirki,toh rayuwar su Mallam me cike da kawaici da yakana ,dole ya ruga jin matar shi har ransa..

Dan dago ido tayi ta kalle shi,se ta rufe ido tana cewa .." Mene to Baffa?"

Dariya yayi yana cewa .."Ah ah,yau kuma ban isa na kalli me dakina ba se an tuhume ni?"

Ita dai dariya tayi ta girgiza kai,dan Inna duduwa badai kunya ba,gashi har yau ta kasa daina kunyar Baffa ..

Rayuwa suke cikin talaucin su, Amman cikin jin dadi da kwanciyar hankali.

_________________

Azumi ya taho gangara ,wanda anci goman farko wato ta Marmari,hallau an cinye goman wuya wato goma ta biyu ,yanzu haka ana goman dokin sallah wato goman Karshe ..

A hankalce dai iyalai suna ta gabatar da ibadar su a gidajen su,masu zuwa masallaci na zuwa ..

Iyalen Malam iro ma ba'a bar su baya ba,dan hatta da Hansai kullun se an tashe su.

Raka'a biyu suke yi su su Mairo ,se suyi addu'a su kwanta

Iyayen kuwa jajircewa suke iya karfin su ,Baffa ya jasu a zaune inna kuwa tabi daga tsaye ..

An sha ibada Muna fatan  Allah ya amshi ibadun mu ya karbi tuban mu sannan ya amshi addu'oin mu..

Yau a kirge saura Kwana biyar Sallah karama..A yau kuma Inna ta tashi ta fita zuwa kasuwa ,nan ta samo zanin ta kala daya ,turmi daya da falle, kudin kuwa gaba daya naira dubu daya da Dari daya.

Zanin mai kyau dai dai karfin talakka,roba ce zanin,robar ma ta karshen karshe irin ta da me sunan London wax.sannan ta siyo musu irin dinkakkun Hijaban nan shima me arha yan  250 kwaya 4,ta siyo musu yan kune yan Naira 30 su hudu..duka gaba daya siyayyar 3000 tayo musu ta dawo gida..

Kuzo kuga tsallen murna an siyo musu zanin sallah ,se godiya suke suna tsalle..Innar su taji dadi ta gode wa Allah da ya hore musu yiwa diyan su kayan sallah..

Baffa ma yaji dadi sosai yadda Allah ya nufa har anyo musu zanin sallah..

A ranar Innar ta aika da kayan gidan Sauden Auwali ,kan kice mi,an zargo dinki ,kudin dinkin nasu 600 su dukka..

Takalmi kuwa suna da na sallar baara,shi zasu sanya abun su ..

Shirye shiryen Sallah ake kan yi kauyen ya kachame ,masu cin bashi naci,masu dan tari sun tara sun fiddo suna kashe wa,masu kallo ma suna nan suna yin kallon su ,kowa dai da abunda yake yi.

Bari mu dakata anan mu hadu a next page..

TBC..........

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now