WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Sunday, 22nd July. 2020
(11)
***************
Angwayen na gano suna ta sake gyara rigunan su ,Kabe nan kabe chan.cikin abokan su da masu aure har da diyan su ,se marasa aure sune suke zaman jiran yiwa angwayen rakiya..karfe bakwai dai dai suka dungumo daga shagon wani abokin su Mamuda.suka nufo gidan su Maina.a hanya suka tsaya suka siyi tsire kowa tsinka biyu,ma'ana na jikka biyu kenan .suka sake dunguma suka nufi gidan.A dakin innaji Maina da kamalu suka dira ,nan kuwan innaji ta tasa su da shi albarka da Addu'oi kala kala,su kuwa se amshe wa suke yi,daga nan se suka Shiga dakunan iyayen su Maza nan ma nasiha aka musu da Jan kunne ,haka nan iyayen su mata ..
Daga nan se angwayen suka rabu, rabi rumfar Maina.Rabi Rumfar kamalu.Wanda suke guri daya .Dan ga kofa ga kofa ,abun Wanda ya sake yiwa yan uwan biyu dadi.wato Mairo da Hasi..
Da haka angwayen suka runga rada sallama har suka dangana da cikin rumfofin,nan sukai abunda Al'ada ta tanadar sannan suka tafi,Dan a wata al'adar irin tasu innaji,yan kawo amarya dasu ake siyan baki,ta yadda in ango yazo daman ya Riga ya biya ..toh hakan ce ta kasance ,Dan an Riga an siyi bakin amaren ..ba jimawa angwayen sukai sallama suka watse ,se ya rage saura kowa da angon ta a rumfar su. .
Maina be Dade ba ya tafi gun Innaji ya karbo lamurje ya dawo.Lamurjen Wanda musamman innaji ta Sanya su cikin randa ,nan da nan kuwa sukai sanyi tunda a Leda yake,haka Maina ya sake cin wata minti goman sannan ya nufo rumfar su da wata aci bal bal din,ya zamana akwai daya a rumfar se wadda ya zo da ita yanzu..
Da sallama ya shiga ,se ya tsaya yana kiran Kamalu daga kofar rumfar shi.yana fitowa ya mika mai lamurje sannan ya mai Sallama ya shige rumfar shi..
Tana zaune yadda ya barta,kuma kanta na sunkuye ne,Dan haka ya tsaya yana kare mata kallo.Gadai ta yar mitsila amman shi ita ce muradin ran shi ,ita ce ta yi masa duniya ..Dan dogon numfashi yaja yace ..."Mairo tashi muyi sallah ko?"
Tashi tayi tsaye ta tsaya ..
Kallon ta yayi yace " kina da Alwala ne?"
Zanin ta na lullubi ta janyo da yake kokarin ya zame,tace "zanyi.."
Kallon ta yayi kamar ba ita tayi magana ba ,se yace "toh zo muje"
Fita yayi tabi bayan shi suka nufi kor rumfar tasu..ce mata yayi ta tsaya nan.da kanshi ya nufi gun innaji ya dauko buta sannan ya zubo ruwa ya taho mata dashi ..
A Inda ya barta ya iske ta ,tana Rabe a jikin garun nasu na jar kasa Wanda aka yi masa shafen farar kasa,abun yayi kyau..
Ajiye mata butar yayi yace .."toh bismillah .."
Gefe kadan tayi ta tsugunna ta fara alwalar ,tana yi lullubin ta na kokarin faduwa,yo ya mata girma.Falle daya ne fa,ina zata kai shi?,ga Dan kwalin ta shima me santsi hakan ne yasa take ta kokuwa da Dan kwalin da lullubin..
Kusa da ita ya matsa Wanda har se da ta tsorata ,tsaya wa yayi yana karewa yanayin ta kallo,nan ya fuskanci duk a tsorace take ,a hankali ya duka kusa da ita yace .."Mairo dan meko lullubin na ruke maki mana,naga kamar ya hana ki yin Alwalar. .."
Tashi tsaye ta yi ta cire shi daga tukwuikwuye shin da tayi sannan ta mika mai..tana bashi ta tsugunna tayi alwalar ta sannan suka koma ciki..
Sallah sukai sannan yayi musu Addu'a.suna idar wa ya janwo ledar tsiren nan ya ajiye lamurjen daga gefen su..
![](https://img.wattpad.com/cover/238861444-288-k943635.jpg)
YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomanceLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...