(20)

37 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Saturday, 6th September, 2020.

(20)

***************

Take wani annuri ya ruga bayyana a fuskar Maina ..gashi Daman kalar shi ta sake fito wa ,yayi kyau dashi ..Nan ya zauna suka gaisa da Inna .Yana kallon Mairo tana ta kauda kai Kuma Bata gaida shi ba...

Kyale ta yayi seda ya tashi tafiya ya huta sannan ya dungure Mata Kai,ai tuni ta fara kuka,Daman Mairo kuka Bai taba Mata wahala ba,Abu kadan se hawaye,Nan Inna Mari ta lalace tana ta lallashin Mairon ta ,dakyar tayi shiru sannan ta tashi ta samu abinci ta hada wa Mairo ta kaiwa Maina..

Shiko Maina da futar da ma seda ya zagaye gidan ya gaggaisa da kowa ..cikin Haka ne Kamalu ya shigo Yana ta Yi wa Maina irin kirarin da yasan ana Yi Masa .Dariya suka Sha sannan suka wuce gunsu..su yan rakiyan da Daman sun juya tun da Maina ya fito daga gun Innaji..

A kan dakali suka zube Maina Yana ta mita ya cire manyan rigunan nan na sarautar sarkin gida..

A Nan Mairo ta iske su suna ta zuba hira,ajje abincin tayi ta juya zata tafi..se Maina yasha kunu yace .."ana Sallar isha'i ki dawo dakin ki.."

Kallon shi tayi taga ba alamar Wasa a fuskar da,tuni ya koma Mata sak Mainan da ta sani a da..

Haka ta tafi tana tuntube ..tana gama fita suka tuntsire da Dariya harda kashe hannu..

Ita Hasi bata nan dama sun fita da Babar maryan,sunan wata Diya Chan hayin subul,akai akai da Mairo taje tace batta zuwa ..

Tare da Maina suka ci abinci ..Maina ne ya rashe bayan sunyi Sallah sun dawo.kamalu kuwa ya hau kason hatsi da
Maina yazo da shi ta gonar sa..

Haka akabi ko wacce rumfa aka Basu abun da ya samu,masu murna nayi masu bukin ciki ma Haka ..toh shidai Allah ba ruwansa da bakin cikin mutum..in yaso azurta ka ba me hanawa ..in Kuma yaso talautaka ba Wanda ya isa Hana wa...

**

Ana idar da Sallah Maina ya shigo gida,be tsaya ko Ina ba ,Nan ya tadda Mairo taci uban tagumi a zaune ..Yana shigowa yace da ita, ta tashi suje wanka..Haka suka yo yadda suka Saba,sedai wannan karon tun a bandakin ta gane cewa Hamman ta ya dado walakanci,wasu irin Abubuwa ya ruga Mata sannan suka fito suka nufi daki,toh gadai shi yanzu an kusa shekaru biyu ba'a hadu ba,Kuma tayi laifi ,Dan Haka da Maina ya ruga chakuda Mairo seda ta gaji tayi lis lis sannan ya kyale ta.izuwa yanzu Mairo ta gane salon hukuncin Maina,Duk sanda tayi Mai laifi baya fada ko harara ko kallon baza ko zagi,shi nashi salon ya Sha Bam Bam da na mutane ,se anzo kwanciya ne yake wahalar da Mairo ,da kanta ta fuskanci Haka se ya zamana Duk wata hanya da tasan in tabi zata Saba Masa batayi,se a zauna lafiya ,Amman yau kam fushin ta na tafiya ya barta ne,ga tarin bukata wadda ita da kanta se yanzu ta gane neman me take ta Mai,ita da kanta tana ta jin kunya ,Dan Yana ta zolayar ta da abubuwan da da bakin ta ta furta su..

Kallon ta yake cike da so da kauna,Kamar ya hadiye ta.chan se yace . "Wallahi Ina son ka Hammah."

Rufe idon ta tayi tana churo baki gaba,tasan ita ta fada ,Amman meye na tsokanar ta ..Haka yayi ta faman jagwalgwala ta ,a ranar dai haduwar shekara daya da rabi akai sannan suka yo wanka suka kwanta . ..

A washegarin ranar yake tambayar ta harkar sagon ta,Nan ta nuna Mai cewa komai lafiya ..

Yace toh Alhamdulillah ,se yace Mata .."Toh waye yake Tara maki kudin cinikin?

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now