WATA KADDARAR
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAADIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @Divaadoveysdiaries03
OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03Thursday,4th September, 2020
(17)
***************
*BURUM*
A ran da Maina ya kimtsa yan kayayyakin sa a cikin wata yar buhu,be zame ko Ina se garin Burum.ko da isar shi be tsaya neman ruwa ba ko Dan abin kaiwa bakin salati ya nemi Sanin gidan sarkin Burum din.ba wahala kuwa aka ruga tura shi,daga nan zuwa Chan daga Chan zuwa Chan,se ga Maina ya isa gidan sarkin.ba wahala ya shiga ciki, sedai bayan ya shiga ne ,ya rasa Kuma Wanda ze tunkara da maganar da yazo a kanta,yo ya kula kowa Yana ta harkokin sa,kusan shi ko Hira bega anayi ba,kawai kowa aikin gaban sa yake yi,kawai se ya cigaba da yar tafiya Yana kallace kallace,cikin haka yagano wata Yar hanya,kawai se ya yanki shawarar bin wannan hanyar,shi be sani ba,Ashe wannan hanyar Sarki ne kawai yake bin ta,Dan ko diyan sarki Basu binta se Sarkin kawai da fadawan sa,se gashi Maina daga zuwa ya afka hanyar Yana ta tafiya,Kuma ko da ya shiga fa akwai dogaren sarki da suka gan shi sadda ya shiga .Amman se suka kyale shi tsabar mugunta da bakin hali.seda yayi nisa sannan ya Yi tunanin ya fa yayi batan kai,haka ya juyo ya fara dawowa ,Amman kuwa se ga wannan dogaren na sarki,ba tambaya ba neman ba'asi suka hau chakuda shi suna kwada shi,kai kace ma zogale ne aka samu,Maina kau zo kuga ihu,Sega Maina ya zage Yana ta zunduma ihu harda Kiran Innar shi da Mairon shi.gashi ya shawo hanya ko ruwa be tsaya ya nemi Sha ba..
Seda sukai mai lis lis sannan ne suka nufi gidan kaso dashi,gidan Wanda a bayan gidan sarkin yake,Maina dai ba ya iya magana ,haka aka kaishi a wurga wani daki aka zura makulli aka garkame shi,Anan ya samu ya kwanta ya ruga maida nishi Yana mamakin laifin da yayi akayi mai wannan dukan ,ba tare da ya Sami amsa ba ya hakura da tunanin da ya Sanya kanshi yake masa mugun ciwo ga jikin sa da yayi mugu mugun tsami..
Kawai se ya fara sabon kuka ,yo laifin mi yayi?,ace ko a Kauyen su me gari ma be San da shi ba sabida baya shiga shirgin da ze da akai karar shi,se gashi yanzu daga zuwan sa yau an zane shi kamar wani karamin yaro?..hmm Allah me iko ..
Haka Nan dai Maina yayi kwance har kusan Rabin awa sannan bacci ya kwasheshi..
Tashin da yayi ne daga baccin yaga har an kawo wani dan saurayi dakin, Yana tashi da kyar ya Mika wa saurayin hannu Yana fadin.."Salamu alaikum"
Amsawa saurayin nan yayi da Yar fara'a..se Maina ya sake cewa ..."Kaima bakai komi ba aka kawo ka Hala?"
Kallon shi wannan saurayi yayi ,se ya daga mai kai..
Maina ya fara mamakin yadda akai suke haka,Chan Kuma yace .."nifa Nan da ka ganni ma bako ne,sauka ta kenan aka samu wasu kattai sukai man Dan banzan bugun tsiya,hallau suka kawo Ni nan.."
Shiru saurayin nan yayi Yana kallon Maina ,Chan saurayin yace .."Ni kaga fa ba zama nazo yi ba,da na samu hanya kawai Zan gudu,Dan se Kai shekaru a Nan wajen an ma mance da Kai .."
Maina ne ya bude baki cikin mamaki da firgici,ya auno yadda ya baro Mairon sa da Innaji da Inna Mari..Nan yace.."Daman ni aiki ya kawoni Nan,Amman tunda bassu so se a hakura ai,nima din da na samu hanya Zan gudu ..
Cikin haka aka Kira Sallar Maghrib,Nan Maina yayi taimama yayi Sallah sannan ya kwanta wani baccin ya kwasheshi..
Wannan saurayi dai Koda Maina ya farka baya nan,da Maina yaga be ganshi ba se ya Dan damu,Dan da ko ba komai ya samu abokin zama,se gashi har an dauke shi..
YOU ARE READING
WATA KADDARAR ✅
RomanceLabari akan rayuwar soyayyar talakawa masu wadatar zuci da kaunar junan su..Labari da ya kunshi tarin fadakarwa da nishadantar wa,Labarin da ya kunshi yadda talakawa ke rayuwa ta jin dadi a dai dai karfin su.Labarin Wanda yake nuna asalin al'ada iri...