(33)

38 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Saturday, 24th October. 2020

(33)

***************

Jama'ar Burum suna nan lafiya..

Bari mu fara jin dalilin da yasa Maina be koma garin su ba a wannan lokacin da suka shafe suna zaune a garin Kano..

Wato Maina be mance da batun Yi masa aure ba da  Ubale yayi ba,na biyu kuwa yafi so se yayi Dan arziki sannan ya koma musu,yadda zasu fi jin dadin ganin shi,Kuma Koda ace be haihu ba har lokacin,in Yana da yan kudaden sa,bane masa dole,se Kuma batun tsangwamar Mairo da ake tayi da ita akan Bata haihu ba,yasan in sunje ma za'a cigaba ne,sannan Yana son ya dauko iyayen sa yazo dasu Birnin Kano,suma suga rayuwa wadda Basu taba zaton tana wakana ba,suji dadi.toh shima fama yake Yi a kanon,har yaushe ya Isa yaje ya dauko wasu ya kawo?,dole tasa ya hakura da komawa se yaga yadda hali ya yiyu tukunna..wannan shine dalilan Maina na kin zuwa Burum..

A garin na Burum kuwa,na fara sauka a gidan su Mairon,inda na ga abun Al'ajabi,Dan kuwa Baffa na gani Yana dogara sanda ya shigo gidan sa da kafafun sa,abun ya bani mamaki,Wanda har na gano cewa mijin salame me ya tafi da Baffa chan jihar katsina,akai ta magani,se gashi kafa ta warke Amman Kuma ga tsufa,dole tasa take hada wa da Sanda..Toh Alhamdulillah.gadai shi suruki yayi wa Baffa iro rana..

Inna kuwa naga ta tsufa itan ma ,Amman Kuma in ka ganta zaka ga ta kwantar hankalin ta ya kwanta,sedai tunanin diyar ta da take kwana dashi tana tashi,tana son ma Sanin halin da suke ciki,wannan irin shiru haka .toh da take Baffa na kokarin kwantar Mata da hankali, dole tasa itan ma take kokarin ganin cewa ta kwantar da hankalin ta game da tunanin Mairo da Maina.

Dan ko Kamalu da Hasina sun dade da dawowa Burum,Hasina nada yaran ta shidda,se Salame me uku,se Hansai auta me uku Amman ita haihuwa biyu tayi,ta samu tagwaye a haihuwar fari,se Wanda take shayar wa yanzu..

Na bar gidan Baffa iro na nufi gidan Gandu,wato babban gida,a Chan dai na ga cewa jiya iyau,se zawarawa a gidan Kamar Kamar me, diyoyin su Mata sun ki zaman aure,Dan Daman bayan gidan ya watse Ubale ya fidda kofar sa,Haka ma Sale.se ya zamana yaran gidan suna yin Abubuwa ba kwaba,a haka har ciki seda akayo wa wata Diya larai,Haka akai ta Kai ruwa rana ,su Ubale sun Hana Dora wa yara talla,su kuwa su Uwani since in basuyi tallan ba ta yaya zasu na cin abinci?, dole Ubale ya cire ido ya bar su da halin su,Dan har takai ta kawo ana Masa gori kan cewa Maina ya gudu da matar sa ya barsu a nan din,gashi wai ance bama a San inda Mainan take ba.doke fa Ubale ya zuba musu ido.daga karshe ma se ya debi Matan sa suka bar gidan Kuma a Birnin Burum suka zauna abunsu ..

Toh wannan kenan..

******

Kano ta dabo,tumbin toron giwa ko same kazo kuwa an fika..

A halin da ake ciki Maina ya zama babban magini,domin kuwa Haidar wan Ummi a wani ziyara da Maina ya Kai masa yake fada Masa cewa ya Yi ta neman shi ance ya tashi daga inda yake,gashi shi ba waya ba,besan inda ze same shi ba,dole ya hakura.se da Maina yabushi iska se ya Kai wa Haidar ziyara,Haidar kuwa yaji dadin ganin Maina,ya Kuma ga ya sauya,Dan in banda kayan jikin shi masu arha ne,kawai sedai a Kira shi da babban matashi,ba babban yaro ba.

A nan Haidar yaje tambayar Maina Ina ya koma,Nan ya gaya masa yayi gini ne a Chan kwanar ganduje ya koma,sannan ya gaya masa sana'ar sa ta gini.

Haidar yace toh suje yaga gida,Koda suka zo yaga gigan,se ya lura fanka daya ce dasu,Kuma ba kafet,se Kuma suna amfani da gawayi ko icce ,tuni ya bawa Maina kudi yace tashi gudunmuwar kenan,ya siya fankoki,Kuma ya siya abun girki,subar gawayi haka.bayan Nan ya tafi Yana tunanin kwazo irin na Maina,lallai Yana so ya taimake shi,Amman ta Ina?"

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now