💞 PRINCESS JAWAHHIR 2⃣💞
Wattpad
Mk_ princess✍6⃣➖🔟
Washe gari hajiya zakiyya na zaune taji karan door bell taanii tasa taje ta bude hajiya uwani ce ta shigo ay kuwa da sauri meerah da ake ma kitson attach tana kwance ta tashi zaune...
Zama uwani tayi hajiya zakiya tace ay da baki zauna ba tashi muyi sama zaifi sirri da sauri meerah ta mike tacema me kiton excuse me ta bisu sama...
Suna zuwa sama uwani ta zauna ta fito da wani abu a leda tace wannan garin shi za'a fesa mata kanta zai juye zata bata ta shiga gari kuma bazata sake tunawa da komai ba hatta sunanta sai ta manta kuma zata dena magana kuma zatayi nisa da shi sosai...
tsalle meerah tayi tace aunty uwani na gode...
Wata kwalba ta dakko tace wannan kuma a gidan za'a binne idan aka binne ta, to kamar an rufe babin rayuwar yarinyar ne a gidan du wani wanda ya santa a garin soyaki bazai lura da batanta ba bakuma zai damu da hakan ba bakuma zaiyi maganarta ba balle ya damu da ita na tsawon kwana 2..
... . Sai kuma suyi ta nemanta hankalinsu zai tashi matuka da batanta amma banda sultan saboda zuwa lokacin meerah ta kammala aykinta na kwanciya da shi, kuma daga lokacin da suka kwanta to ta gama malakarsa bazai dinga jin maganar kowa ba sai ta meerah bazai gane zancen kowaba saina meerah bazai damu da kowa ba sai meerah.... ..Wani ihu meerah tayi tace i love u aunty uwani shiyasa nake sanki amma aunty meyasa bazasu manta da ita gaba daya ba sai na kwana 2....
Eh meerah nima nama boka wannan tambayar cewa yayi sarki da matarsa (ummah) a tsaye suke a kan yayansu da masarautar gaba daya bazaiyu su manta da yarinyar nan ba dan yace ya gano tana da karfin jini a masarautar kuma a hakan ma ba lallai su manta dinba amma yasan bazasu taba ganinta ba dan aljani zai sa ya sace ta ya kaita chan inda bazasu ganta ba...
ga wannan turaren shikuma shafawa zakiyi ranar da zaki tare wannan kuma kiyi tsarki shine cikon aykinki na mallaka
yawwa aunty uwani nagode yarinya du tazo kamar mayya ta kara rikita lissafi da muna fama da iyayensa da shikansa tazo ta karu gwara mu kauda ita mu huta muji da su masu zafin yawun...
Wai ni zakiyya wannan mutane da wuyar sha'ani suke komai nasu sai kaji ance a tsaye suke? aunty uwani ta tambayi mommy(🤔ni kuwa nace bazasu tsaya ba bayan sunsan sunada makiya irinku dole su dage da addu'a allah ka nisanta mu daga sharrin makiyi😏Ameen)
Kedai bari uwani du inda mukaje sai angaya mana haka akan wannan mutanen amma nasan yanzu sun hadu da daidai su zai mana maganinsu ita kuma wannan yarinya karamar alhaki gata har mun gama da ita dan nasan du neman da zasu mata bazasu ganta ba tsinanniya me kalar aljanu...
Wlh mommy na tsani yarinyar nan allah yasa bazasu nemota ba allah yasa ma ni ta mutu a hanya....
Dariya uwani tayi tace daughter na kenan barta banda mutuwa, a dai barta da batanma da rashin maganar ma kinga ay bazata iya bayani ma a gane me take bukata ba watakil ma yunwa ta kashe ta dama ance yar hutu ce kinga wahala da yinwa da bata saba jiba su zasu karasa tsinannaiya... ..
Allah yasa aunty inji meerah mommy ce tace meerah tace kyakyawace watakil wani ya gani ya samu rabonsa...
Tab mommy ay wlh ko wani ya ganta cewa zaiyi aljana ce kinga kyanta kuwa ay ko maza suka ganta guduwa zasuyi suce sunyi gamo ba me taimakonta ta fada tana dariya....
(Humm duniya kenan ka shuka sharri har ka rinka dariya bayan sun manta akwai allah)
Wannan kenan📝
Jirgin su sadiya yana sauka suka fito suna zauwa parking space suka ganshi a range rover dinshi da mamaki sadiya tace tab gaske ne ko mafarki yaya kaine kazo daukarmu kodai kazo ganin wanine a airport dan murmushi yayi yace to in bazaku shigaba nayi tafiyata da sauri salma ta shiga yaran sai murna suke arif yace yau uncle ne yazo daukarmu ba sarkin mota ba muhd yace kuma fa be taba zuwa ya daukemu ba , dariya sadiya tayi tace a toh yarama sun gani wlh... ita dai tana tsaye y sadiya ce tace shiga mana jawahhir salma tace shiga gaba dan wlh danke yaya yazo daukarmu ta mirror din gaba ya harareta dan yasan tanan zata gani bakinta ta rufe y sadiya dai sai murmushi take kayansu akasa a booth ya ja motar yayi gaba kallon gefanta yayi yace babu gaisuwa...