💞PRINCESS JAWAHHIR 💞Wattpad
Mk_princess✍3⃣6️⃣➖4️⃣0️⃣
Tana zuwa kara gyarawa tayi ta dakko kwallin nan ta saka tana yarfa hannu sbd zafin da take ji dan ita ko kwalin ma ba iya sawa tayi wayyo mum zaku kashe min ido ta fada tana turo baki wlh kai kadai ne za'a sa insa wannan abun a idona nasa ta fada kamar zatayi kuka Doll bell ta danna....
Yana zaune yana waya magana yake dr sulaiman akana asibitinsu da suke so a fara ayki.....
Jin ana ta danna doll bell din ne ya kalli kofar yamutsa fuska yayi a ransa yana cewa waye yake mishi wannan haukan zai ta danna doll bell kamar yana binsa bashi....
Ta danna kusan sau 4 har ta fara bubbuga kafa na rashin bude mata da yayi.....
Jin an danyi shiru ya tashi yaje ya bude ciki da mamaki yake kallonta ta sunkuyar da kai hada rai yayi ya juya zama yayi ya cigaba da wayar da yake yi...
Shigowa tayi ta zauna tana jira ya gama ko kallon inda take beyi ba har saida ya gama system dinsa ya cigaba da dannawa ko kallon wajan da take beyi ba....
Tana zaune ta fara magana a zuciyarta wlh prince din nan ya fiya ji da kai ji yadda yamin banza kamar be san dani a wajan ba ko ma dai menene saidai kayi wlh sai ka soni dole tunda ina sanka....
Kamar a fili tayi maganar ya dago ya kalle ta ita kuma idonta na kan abin rigarta da ya makale a jikin center table din da ke tsakiyar parlon da ya matso dashi kusa da kujerar da yake zaune ya dora system dinshi....
maida idonsa yayi kan aykinsa kamar me ciwon baki yace.. ke... lfy....
Kamar ta kifa mai mari sbd haushi amma idan ta tuna waye shi a wajanta sai ta danne zuciyarta sbd ita bata taba haduwa da wanda yake wukanta ta ba irinsa....
Dan murmushi ta kakalo tace haba prince haka ma zaka ce laifi nawa kamin baka gayamin ka dawo ba sai ni na gano nakira kuma baka picking sannan na maka text ba reply kuma nazo har gidanku amma ko ka nemini ji abinda ka min dazu da saf.....
Kasa karasawa tayi sbd wata tsawa da ya daka mata ke dallah ya isa yace baki da.... dagowa tayi ay kuwa suka hada ido kasa karasawa yayi jin da yayi kamar an sokeshi a ido kauda kansa yayi yana huce ya dafe kansa ya mamakin abinda yake ji a kansa da kyar ya daga kansa ya kalle ta yace pls naji nagode zaki iya tafiya.....
Ganin yadda yayi sanyi sai ta fara murna tace haba my SULTAN na maka laifi....
Ji yayi maganarta na masa wani iri a kunne yadda yake ji yasan idan ya cigaba da zama da ita wani abun zai iya faruwa.....
Dagowa yayi da idanunnan nasa me ban tsoro da sukayi jaaa yace pls ki tafi na gode am not in the mood I some rest please....
Ehhyah my prince am sorry I don't know ay bara Na hada ma coffe kafin na wuce....
Bai ce mata komai ba shidai kawai ya rufe idonsa tashi tayi taje ta hada masa coffe din da kwatakwata ba wani iya hadawa tayi ba kawai ta cika coffe din ne da sugar sai ruwa da ta zuba mishi ta hada da maganin bayan ya gama zafi ta juye ta kawo mai ajiyewa tayi tace am sorry tashi sai kaje ka kawanta ko dagowa baiyi ba bai kuma bude idonsa ba ji yayi kamar wani abu na bin jikinshi tsigar jikinsa na tashi kamar an tilasta zuciyarshi ya fara addu'a a hankali yanayi yana kara runtse idonsa....
Sunkai wajan 5 minute a haka sannan ya dago ya bude idonsa da yayi wani irin jaaa ba karamin tsorata tayi ba nan jikinta ya fara rawa....
Kallon coffe din yayi ya kalleta ya kauda kai kawai sai ya mike ya fara tafiya hanyar bedroom dinsa yayi cike da tsoro ta mike sai kawai wata zuciyar tace bishi binsa ta fara yi yana zuwa daidai kofar ya juyo kawai sai ji tayi an shaki wuyan ta kakari ta fara yi tana yarfa hannu idanuwanta sun firfita a haka ya jata har bakin kofa sannan ya cikata da hannu ya nuna mata hanyar kofa tana nishi ta bude ta fita .....