💞 PRINCESS JAWAHHIR2⃣💞
Wattpad
Mk_ princess✍1⃣1⃣➖1⃣5⃣
Affuwan amin mutuwane ta kusa shiyasa kuka jini shiru Ina neman mata addu'a Allah ya jikanta yasa aljannar fiddausi ce makomarta... 😭
A yaune za'a fara biki gida ya dau harami ko Ina ya sha gyara da fenti kunsan gidan sarauta da ado bangaran Ummah an turare shi da turare kamshi sai tashi yake du ya hada wajan yan uwan su Ummah ne suka zo sadiya da Salma sai kaikawo suke suna tarbar yan uwa da abokan arziki wata cousin din umma ce tace sadiya wannan turare naku da kamshi yake wata kawar ummah a kusa da ita tace hajiya lailah kin rigani ne Ashe har yan Yemen ma sunji dadin turaren nan sadiya a Ina kuka siyo murmushi y sadiya tayi tace wlh wata ce (the skin studio tana yin turaruka na jiki da na wuta da kayan Gyaran jiki, kwaliya da mayuka ay Matan nan karshe ce wajan sirin kamshi aunt's ta iya hada turare, turarenta daban ne tana nan a kano ga number ta📲 08038259320 Instagram page dinta 👉Perfume_plug_kn 👈xaku iya Kira dan neman Karin bayani)
Nan take wajan mutum shida suka kirata dan samun nasu kayan kamshin....
Wannan kenan📝
Jawahhir tana dakinsu ita kadai tana kwance a daki ta rufe ido kamar me bacci amma ba bacci take ba , taki shiga cikin gidan ne saboda ita bata saba ganin mutane da yawa haka ba gashi kwana biyu abubawa da yawa suna damunta tuanain iyayenta da ya zame mata jiki faduwar gaba da take yawanyi ga ya sultan kwana 2 baya shigowa cikin gidan sosai sannan kuma tana mamkin yanda take jin haushin auren da zaiyi a zuciyarta tace ko dan shima baya so ne tana cikin wannan tunanin wayarta tayi Kara tasan dai masu kiran basuda yawa ko y sadiya ko Salma ko Ummah ko ya sultan tana kallon wayar shine kuwa dagawa tayi cikin wata irin murya me sanyi da taushi tayi sallama....
Shiru yayi yana lumshe ido ya Kara Dora kafarsa a kan table din office dinsa ...
Jin yayi shiru tace hello yaya....
Ajiyar zuciya yayi yace baby kina lafiya...
Lumshe ido tayi jin muryarsa ta Kara dadi kasa amsamai tayi kawai tace ummmm.
Me kikeyi yanzu is like kamar ke kadaice....
A hankali tace eh ni kadaice...
Meyasa kike zama ke kadai kina tunanin koh ya fada cike da tausayin ta...
Umm dama na dan gaji ne shine na dawo na dan kwanta amma yanzu zan koma cikin gidan...
Ya kamata dai please baby kinsan bana son kina zama ke kadai ki tashi kije wajan su Salma kinji...
Ok yaya dama ni mutane ne sunyi yawa a gidan ko Ina mutane kuma kowa yaita kallona kamar wani sabon Abu ta fada cikin shagwaba...
Dan murmushi yayi😊 kamar bazaiyi magana ba sai yace dan baki saba bane kuma kallonki da sukeyi.... Shiru yayi...
Tace meyasa....
Murmushi yayi yace kina musu kyau ne shiyasa suke kallonki...
Murmushi itama tayi tace ay suma yaya suna da kyau sosai especially cousin din su ummah..
Yh amma kin fisu kyau ay Saida ya fada kuma sai yaji dama be fada ba kar fa yariyar nan ta raina ni Gyaran murya yayi yace ni bana son surutu tashi kije kar na sake Kira naji ki ke kadai kawai ya kashe wayar yana ajiyar zuciya kawai sai yaji damuwar da tai masa yawa tana raguwa.... Knocking kofa a kai yes.... Khalil ne shigowa yayi yace haba ango kai ba aykin ba kai kuma ba shirin bikin ba komai kaki yi du ka Dora min wahala komai ni ake sawa to bashi, ... nima nawa dole a yimin komai...
Kallonsa kawai yake Saida ya gama yace kai kacika suruatu wlh kuma aykin da kakeyi wayasaka ya fada yana Wani mazewa...
Dariya khalil yayi yace yanzu fa naji kana Waya kana kashe murya amma ji yadda ka Wani hade rai...
YOU ARE READING
JAWAHIR
Roman d'amourIts all about love and Royal family life.... Read and find out ❤❤❤