💞PRINCESS JAWAHHIR 💞Wattpad
Mk.. princess✍4⃣
Yana shiga yaga du suna bacci JAWAHHIR tana kwance sosai take bacci sister ummi kuma tana zaune a kujera tana bacci.....
karasawa yayi a hankali karya tashe ta wajan gadonta yayi tsayawa yayi akanta kamar me tunani hannu ya sa ya dauki pillow da yake gefanta ya kara mata a gefan kafarta da ta karye kallon ta yayi ganin yadda take bacci kamar ta mutu murmushi yayi yace sleeping beauty kusa da sister ummi ya je Dan gefan kujeran ya Dan bubbuga farkawa tayi....
Yace sister ummi ki kwanta mana sai wuyanki yayi ciwo ay.....
A Dan kunya ce tace sorry sir ehmmm dama ban san bacci ya dauke ni ba nima....
Murmushi 😊yayi yace bakomai ay ya kamata dama kiji bacci ay dare yayi ki kwanta ki huta Bawani matsala dai ko....
Eh babu sai dai tunda muka dawo take cewa kanta na ciwo Amma da na bata dinner tasa drugs din ta naga ta rage complain Amma sir kamar dai har yanzu tana da damuwa....
Ok tom bakomai da safe zan zo kafin na fita sai naji meye matsalan good night...
Good night sir tace dashi ta rufe musu kofa.... Asuba ta gari😴✴✴✴✴✴✴✴✴
Juma'at babbar rana wayansa da ke ringing kansa dake kasan pillow ya fito dashi tsaki yayi mtiwsss😏 daga wayar yayi ba tare da ya duba ba yace meye jin Wandda ta bashi amsa ne yasa yai saurin tashi....
Mama barka da Asuba....
Barka kadai wai kaikam babana yaushe zaka girma ne haryanzu baka iya tashi sallar Asuba...
No ba haka bane mama tuba nake gajiya ce wlh kinsan na gaji.....
Kajiya ko yayi kyau idan na maka aure ka haihu danka yazo Yana tashinka sallar Asuba sai kace mai gajiya bani Dana haife ka ba.....
Dan sosa keya yayi kamar Yana gabanta murmushi yayi ....
Sanin ba amsa zai bata ba ta dora da cewa takawa yace kuzo kaida khalil kafin ya fita fada yana son ganin ku bata jira amsar sa ba ta Kashe wayar ....
Ajiye wayar yayi ya dafe kansa idan da sabo ya saba Dan kullum sai sunyi wannan dramar shi kanshi abin Yana damunshi yau shekara uku kenan shida baya wasa da sallah musamman ma Asuba Amma yanzu KO ya kwana Yana ayki lokacin Asuba na gabatowa zaiyi bacci tunawa yayi da abinda ya same shi last week da daddare ya kwana yana ayki baya jin bacci har theater yayi a ranar Amma Asuba nayi ya rinka jin wani bacci dole saida ya nemi excuse ya je office yayi bacci kuma sai banyan Asuba ya farka....
Ajiyar zuciya yayi yace Allah ka yaye min bathroom ya shiga wanka yayi yai alwala yayi sallah gari du ya Waye tashi yayi ya fito parlor zama yayi kallon agogo yayi yaga 7:15 kamar me bacci ya lumshe idon sa 8:00 yaji shigowar mutum bude ido yayi .....
Zube wa yayi ya gaishe shi da mishi ya gajiyar hanya....
kauda kai yayi yace nasara kana lfy....
Lfy lau Allah shi tai make ka dama nazo hada coffee ne naga lokaci yayi....
Maida kansa yayi ya lumshe bai bashi amsa ba ya Dora kafarsa kan center table....
Ganin haka nasara ya tashi yaje ya hado coffee ya kawo karba yayi tv ya kallah ganin haka nasara yaje ya kunna ya dakko remote din ya dawo dash kusa dashi zube wa yayi kasa yace Allah ya tai make babu wani abun....
Da kai ya bashi amsa...
Mikewa tayi yace Allah ya fansheka lfy ranka yayde....
A hankali ya dago ya kalleshi yace Ameen....
Fita nasara yayi be dade da fita ba khalil ya shigo salama yayi ya amsa....
Yana shiga ya ganshi a zaune murmushi yayi yace ran PRINCE SULTAN ya dade an tashi kenan Ana kallo Ana shan coffee kaga basaraken doctor....
Harara ya bishi da shi kawai yaki kula...
Abin dariya ya bama khalil yace Tofa ni karka tsoratani da wannan idanuwan naka ka tashi mu shiga cikin gida bakaji sakon takawa bane....
Kamar ba dashi yake ba kawai ya mike ya shige Daki kaya ya sauya cikin wani yadi sky blue mara nauyi yasa zanna bukar dinsa me kyau da touch din blue ajiki fitowa yayi ya a sa agogo a hannunsa..
Khalil dake kallonsa ya kauda kai yayi kamar be ganshi ba ya maida hankalinsa kan TV...
Kallonsa yayi yace muje ko.. Gani yayi yamai Banza.... Kallonsa yayi yace wai meye haka ina maganar kamar ba dakai nake ba...
Sai a sannan khalil ya juyo yace Ashe ba dadi ni zakaiwa mulki an gayama nima ban iya shariyar bane....
Murmushi yayi sosai ganin khalil sai kumfar Baki yake wai shi yaji haushi tabe Baki yayi yace yaci ace ka saba man ya fada Yana dafa kafadar sa murmushi sukai gaba daya suka fita basu zarce ko ina ba sai cikin gida sashen mai martaba......