8️⃣1️⃣➖8️⃣5️⃣

177 26 0
                                    


💞PRINCESS JAWAHHIR 💞

Wattpad
Mk_princess✍

8️⃣1️⃣➖8️⃣5️⃣

Asubar fari mom tasa meerah a gaba suka shirya sukatafi sai da suka biya suka dakko kawarta hajiya uwani chan wani kauye ne a cikin garin na nasarawa gaba daya yare ne ma a kauyen kuma ga alama ma babu wani musulunci a garin a kofar wani gida sukai packing tun daga kofar gidan suke ganin wasu tarkace a jikin bangon gidan wasu gashi gashi da jan fenti ga wani zane da akai kamar na ido sosai meerah ta tsorata ba dan mamanta ta kama hannunta ba da babu abinda zaisa ta shiga wannan gidan....

Yana zaune a tsakar gidan bashida ko riga a jikinsa ya fente jikinsa da farin fenti fuskarsa kuwa ba kyan gani daga shi sai wani zane na jan yadi a kugunsa an shimfida mai bakin yadi a gabansa da kayan tsafinsa yanata wani yare....

Da baya suka karasa wajansa nan suka zauna daga mom har meerah yanzu babu wanda be tsorata ba jin ya kira sunan meerah da mom yace sannunku kuma abinda yakara tsorata su hausar da sukaji yayi dan yanayin sa gani suke zo in kasheka da hausa be sani ba.. 

Katse musu tunani yayi yace meke tafe daku .....

A tsorace mom ta kalli hajiya uwani tace yi bayani hajiya uwani ce tace to mudai  boka (tuturi tutu)  ka kara karko a koda yaushe wannan kawata ce hajiya zakiyya to yar tace zata auri dan sarkin soyaki me suna SULTAN to inda matsalar take shifa baya so kuma  tana so ya sota ta juyashi daga shi har iyayensa.....

Dariya yasa me karfi yace an gama fadi wata matsalar....

Yanzu mom ce tace to dama akwai wata yarinya da take so ta bamu matsala Ga alama yana son ta Dan akanta har sabani suka samu shida meerah to so nake a rabasu tafice ta bar gidan kuma kar Wanda ya tunata balle ya damu da barinta daga gidan..  

Wata dariyar yayi sai kuma ya sha kunu wani mai ya dakko a yar kwalba ya ajiye a gaban su yace to ke uwani kinsan yanayin aykin mu shi wannan na mallaka sai mun hadu yanzu zamu shiga daki bakin aljani zai karasa aykin    .....

Da Dan mamaki mom ta kalli hajiya uwani alama ta mata akan ta kwantar da hankalin ta...

Mikawa meerah kwalbar nan yayi ta karba tana karba ya mike ba tare da yace ta bishi ba kawai ta Tashi ta bishi wani daki suka shiga...  

Mom har zata kamo ta hajiya uwani tai saurin hanata tace haba hajiya zaki bata mana ayki...

Cike da tsoro tace uwani kar ya mata wani abu fa....

Wani abu kamar me bawani abu aykinsa kawai zai yi...

Suna shiga dakin yasa ta cire kaya ta shafa wannnan  abun cikin kwalbar a jikinta jiki na rawa ya kwata da ita saida ya gama abun da zaiyi sannan ya tasheta yace ta sa kaya ta sa du wannan abun da ya mata ya maidata kamar wata gunki shi yake controlling dinta ....

Gaskiya ni uwani ina tsoro naga sun dade karfa yaje ya mata wani abu ni zuciyata tana ta bugawa...

Haba kekuwa zakiyya sai kace bake inda amana be kamata kiji tsoron boka ba ina ne baki shiga ba akan dadyn meerah   .....

Dan murmushi tayi tace ay naga sun dade ne bata karasa rufe bakinta ba sai ga meerah ta fito zuwatayi ta zauna mom ce tayi saurin tabata tace yaya me ya faru kawai kallon mom din tayi tace bakomai da mamaki mom din ta kalli yar tata ganin tawani maze....

Fitowa yayi yana wata dariya ya tsaya a gaban su ya kalli uwani yace an gama wannan SULTAN yazama na ta wani kullin garin magani ya bawa mom ta karba yace a sa mai a madara ko ruwa yasha bayan aurensu da kwana daya sai denajin maganar kowa sai tata zai manta da kowa ruwa idan bata ce ya sha ba haka zai shekara da ishirwa be sha ba hahahhha ya sa dariya..

JAWAHIRWhere stories live. Discover now