💞PRINCESS JAWAHHIR 💞Wattpad
Mk_princess✍
1⃣6️⃣➖2️⃣0️⃣
Sunana Maryam Youssouf Tafeeda.... Babana Youssouf Tafeeda Oumarou dan kasar Niger ne cikin damagaram..... mamahna Ayishah Abraham Hakim ita yar Ethiopia ce Addis Ababa city dake garin Ethiopia Ni kuma na tashi a abuja gidan mu dake gwarinfa nan nayi rayuwa tundaga yarinta ta har na kai time din da na fara zuwa schl daga ni sai mamah na da daddy sai nanny na me suna baba jummai tunda na tashi nake ganinta a gidan mu ita take yin shara da goge goge mamah na kuma tayi girki ta kula dani komai mama na ce ke min mamah na ba karamin sona take ba ko ciwo nake tare mukeyi idan naki cin abinci haka zatai ta damuwa kuma ta kasa cin itama bata son ganin bacin raina daddy na kuwa babu abinda ke bata mai rai irin jin kuka na iyayena na sona matuka kawayena biyu kachal khausar da hidaya wanda suke neigbours din mu kuma tundaga nursery school har secondy da na gama NTIC dake nan abuja mun zama family friends dasu...
Sai Aminin daddy Alhaji Mahmoud da matarsa hajiya hadiza da yayanta ummi da khalifa daga hajiya hadiza har yayanta basu da dabi'a me kyau masamman ma khalifa danta da yake mara tarbiya ga shaye shaye shiyasa mamahna bata sakar musu ganin haka yasa suma basa zuwa gidan mu amma alhaji Mahmoud kullum yana gidan mu dashi muke dinner kullum....
ina rayuwa cikin farinciki da hutu abu daya ne ya fara damuna daga lokacin danayi wayo friends dina suna yawan zuwa garinsu kausar yar kano ce Hidaya kuma yar bauchi ce lokacin zuwa lokacin suna tafiya garinsu hutu su da family su amma ni daga daddy har mamah babu wanda ya taba cewa zai kaini Niger ko Ethiopia sai dai muyi ta yawo kasashe ni kuma idan su hidaya sun dawo sunzo gidan mu suyi ta bani labrin family dinsu da kakaninsu abin na burgeni idan suka tambayeni me yasa bana zuwa wajan kakanni na sai nace musu daddy yaki kaimu a haka har muka gama secondary school na samu first class dama kuma daddy yamun alkawarin zai kaini UK na yi karatun medicine dina a chan inata jin dadi ban taba tunanin daddy zai bar business dinsa da mutanensa mu koma UK ba kawai dan nayi karatu wannan abin ya karasamin san iyayena matuka haka mukai sallama da kowa muka tafi UK a nan muka hadu da Yaya SULTAN wanda ya Zane min kamar blood brother duda dai ina ganin yana takura min amma yadda yake kula dani ina jin dadi kuma yadda yake ma iyayena yasa na kara ganin kimarsa a idona sosai ....