2️⃣1️⃣➖2️⃣5️⃣

231 22 0
                                    


            💞PRINCESS JAWAHHIR 💞

      Wattpad
  Mk_princess✍

                        2️⃣1️⃣➖2️⃣5️⃣

Zaune take akan sofa ta Dora kafa daya kan daya cikin English wear jeans and T-shirt  tana waya sai turo Baki take kamar tana fushi....

wata hamshakiyar mata ce ta ke sakkowa daga stairs karasowa tayi tana cewa yayane meerah turo Baki tayi tace mom Allah abinda prince yake min baya kyautawa yanzu ace yana Nigeria ban sani ba ina ta neman number sa na UK yaki shiga sai yanzu da nakira number sa na 9ja naji ta shiga Kuma tun dazu nake kira yaki picking ta fada tana kokarin kuka rungume ta tayi tace haba my princess you're the only princess in Soyaki haba ta fari Kuma auta bana so ki rinka bata ranki yaushe SULTAN din ya dawo ni bana son kina daga hankalinki akan namiji kullum ina gayamiki idai namiji ne saidai ke ki juyashi ba dai shi ya juyaki ba....

Dagowa tayi ta kalli mom dariya sukayi suka tafa tace shiyasa nake sonki mom I love you ....

Juyawa tayi tace yanzu to ya za'a yi mom ina son ganinsa ....

Nace ki kwantar da hankalinki shiryawa zakiyi tunda kinyi hutu kawai ki tafi soyakin...

Mom amma fa kin san Abba bazai barni ba...

Zai bari mana bani Nace ki shirya ba zan ce mar kaduna kika tafi gidan aunty yanzu zanyi  ma hajiya fulani waya na Gaya mata zaki zo hutu wajanta Kuma Nace wannan kanwar tasa da kuke school daya zaki jaa ajiki meerah tun yaushe nake miki Wannan karatun amma kinki ji wani lokaci kinada taurin kai ta fada tana hararar ta...

Matsowa tayi ta Kama hannunta tace mom wlh kinsan ni duda tana sister prince gani nake bata kai matsayin da zan kula ta ba Kuma mom kisan ba irina bace ta cika kauyanci ne taita wani irin dressing kamar wata matar Aure da mayafi fa take sawa wata rana ma da hijab zaki ganta kamar matar liman ni kuwa kinsan ba class dina bace shiyasa ko a school nake share ta I don't like irin Wannan mutanen mom ta fada tana turo Baki...

JAWAHIRWhere stories live. Discover now