💞 PRINCESS JAWAHHIR2⃣💞
Wattpad
Mk_ princess✍2️⃣6️⃣➖3️⃣0️⃣
🌟Me sultan zai ce ma su khalil game da jawahhir ❓
🌟zai yarda yana son jawahhir ❓
🌟 kuma zai gaya mata yana sonta❓
🌟 ya shirin su meerah akan jawahhir ❓
🌟ya dinner zata kasance ❓
🌟ya maganar alhaji barau❓
Shiru dakin yayi kowa so yake yaji me zai ce .........
Sukuyar da kai yayi lokacin da ya dago abun ba karamin daga hankalinsu abin yayi ba dansu a wajan su sabon abune da basu taba gani ba Wanda idan da Wanda ya taba ganin hawayen sultan ma saidai khalil kuma koshi yasan ba karamin abune zai sashi kukan ba
Kallonsu yayi yace guys ina son jawahhir sonda banta ta tunanin zanyishi ba har na koma ga Mahalicci na gani nake ko iyayenta a yanzu bazau kaini sonta bana kauna ko yaya naga damuwa a tare da ita idan ina tare da ita ina samun relief sbd gani nake kamar ranta zai iya baci ko zata shiga damuwa idan bana tare da ita ina mata son da bazan iya bawa kowa jawahhir ba ina tsoron ranar da zan rabuda ita wlh idan yau na auri jawahhir nasan bazan taba yin adalci a tsakaninsu ba sbd meerah ban taba sonta ba jawahhir kuma tun ranar da na fara ganinta sonta yake wahalar dani tun ban gane ba har nagane amma gani nake kamar ita bazata soni ba kuma ina tsoron kar nace ina sonta nauyina da matsayina yasa ta karbi soyayya ta nafiso jawahhir ta soni kamar yadda nake sonta ta kuma yadda son da nake mata ba wai Dan ta rasa iyayenta vane bawai Dan ina tausayinta bane son dake mata asalin sone danake mata tun bata San kanta ba kuna ganin jawahhir zata fahimce ni kuna ganin jawahhir irin wannan son take mun ba sona take Dan nazamar mata jigo bane a rayuwar ta ....
Gaba dayansu sun tausaya masa sun kuma kara tambatar da abokinsu ya kamu har wuya tissue ya dauka ya goge idan sa yace muje khalil ne ya dafa shi yace ina so gobe kafin a kai ma amaryar ka kazauna da jawahhir ka gayamata abinda yake zuciyarka ni kuma na tabbata itama tana ma irin son da kake mata ....
Kamar Wanda akace an yafe mai du laifinsa haka ya ke kallon khalil kawai sai ya rungume shi yana wata irin dariya da su kansu sun dade rabon da suga yana wannan dariyar wani murmushi yake kamar an mai bushara haka suka fita su kb nata tsokanarsa yana musu murmushi har zasu je waja mota ya kamo khalil yace zomuje mu cika umarni kamanta tace idan na shirya muje nan sukayi side din umma suka bar su kb na jiransu a cikin mota...
Suna shiga umma na zaune suma gaishita nan ta dafasu tana yaba kwamiyarsu yanayi n sultan din ne ya dan bata mamaki ta dade bata ganshi haka ba kamar yana cikin farinciki kamar ta tambayeshi sai tace bari dai ta barshi tasan idan abinda ya kamata ta sani ne da kansa zai sanar mata haka mata nata guda abbu tayiwa ango addu'a nan umma ta ce zo na ma addu'a kayi kyau da yawa murmushi yayi ya durkusa ya cire hular ta masa addu'a ta gama yayi godiya suka tashi suka fita .....
Suna fita su jawahhir suka shigo suma sun gama shiryawa anzo a nunawa umma kwaliya ...
Umma ta yaba da kwaliyar da yayan nata sukayi nan suka mata salama suka fita a wajan da ake ajiye motocin gidan suka nufa inda motocin suka karu sbd Dana daukar amarya Dana abokan ango sai kuma motocin masu gidan wajan a cikin gidan yake amma yanada nisan da dole a hau mota musamman su da suke yayan manya basa je a kafa ba salma ce zata tuka su a motarta jawahhir tace Dan Allah bani na kaimu sai ki rinka nuna min sbd na dade banyi tuki ba sadiya ce tace dama kina driving ne tace eh yaya ya koyamin a UK fadin UK din datayi sai taje tana missing iyayenta lura da hakan yasa salma tayi saurin bata keys din tace yau zamu hau tukin yan UK yaya sadiya tace ay bazamu gane komai ba tunda wajan ba nisa ne dashi ba ko yar koya zata iya kaimu....