3️⃣6️⃣➖4️⃣0️⃣

249 20 5
                                    


💞PRINCESS JAWAHHIR 💞

Wattpad
Mk_princess✍

3⃣6⃣➖4⃣0⃣

Tunda ya koma yake bacci kamar a mafarki yake jin karan doo bell tsaki yayi ya bude ido a hankali juyawa yayi ya kalli agogon dake kan bedside kara bude idanu yayi ganin har lokacin azahar ya wuce da dan sauri ya tashi jallabiyar sa da ya cire ya dauka ya sa parlo ya je ya bude khalil ne da dr sulaiman...

Be musu magana ba ya juya ya koma bedroom alwala yayi yai sallah sannan ya shiga wanka....

Zama suakai dr sulaiman yace wato me hali baya fasa halinsa kaga guy din nan ko inda muke bai kallah ba sai kace ba dashi mukai zamu hadu yauba....

Khalil ne yace tab kai ma dai ka manta halin SULTAN ne ay basaraken doctor idan mutum bai san halinsa ba sai yasa maka high Bp dariya sukayi suna zaune ya fito cikin wani yadi nevy blue da hularsa a hannu yana sawa zama yayi cikin daya daga cikin kujerun dr sulaiman ya kallah yace S I. Ya kk....

Da kamar bazai amsa ba sanin halin SULTAN din kuma sai yace lfy ya halinka na wulakaci ka barmu munta tsaye a kofa kazo ka bude mana kuma ko kallo ba mu ishe ka ba koh...

Kamar ba da shi yake ba yanata latsa wayar sa saida ya gama yace am sorry banyi sallah bane shine nayi sauri nayi ya fada yana kallon khalil da tunda suka shigo yake waya tabe baki yayi yace bari na sha coffe sai mu je dan yau ko breakfast banyi ba....

Kahalil ne da ya gama waya yace waya hanaka toh malam dan Allah kayi sauri munada abubuwa fa nida na dawo daga tafiya ma nafika abin arziki....

Harararsa yayi yana mike wa sallama sukaji ana kwadawa dr sulaiman ne ya amsa nasara ne ya shigo nan ya zube yana kwasar gaisuwa ya juya wajan uban gidan nasa yace Allah ya taimake barka da rana inada kewayowa ba'a tashi ba gashi breakfast har ya huce amma hajiya azumi tace me za'a dafa Allah ya taimake ka ✊

Dan tabe baki yayi ya cigaba da tafiya Kamar ba dashi ake magana ba cike da isa ya karasa wajan coffee marker har zai zuba ya fara hadawa sai ya kalli nasara yace dauki ka wanko min ka hada min wani ya juya ya koma wajan zamansa...

Nasara ya dauka ya wanko ya hada wani yazo ya durkusa ya mika mai ya zauna yana jiran amsar abinda ya kawo shi saida ya kusan shanyewa ya dago ya kalli nasara yace ace bana bukatar lunch ya fada yana ajiye cup din ya kalle su yace muje.....

Tashi sukai a bakin kofa Dan liti ya zube ya gaishe shi nan ya shiga Dan yayi aykinsa Na shara....

Sabon asibitin su suka nufa nan sukaje sukaga du abinda ya rage a karasa sun dade suna planing yadda abin zai kasance su uku zasu rike asibitin kowa da nasa bangaren nan suka yanke shawarar Saturday za'a bude asibitin saboda komai an gama a hanyarsu ta dawowa ne khalil yace wlh guys ya kamata muyi aure bai kamata ace munda asibiti kamar wannan ba ace bamuda aure du abinda muke bukata yanzu dai mun samu babu abinda zamu ce sai godiyar Allah....

S I. Ne yace wlh kam ni dai na kusa dan an kusa a kai kudin aure ma nikam na kusa zama complete ya fada yana dariya....

Khalil ne yace oh mu ba complete bane kenan to sai ka gayama wanda basu da niyar zama complete din nima inada tawa tana nan a gida...

Yana jinsu ya lumshe idonsa tabe baki yayi yace toh gwara kai S I farida tana da dan girma shi kuwa wannan da ya kwaso yara yana so ya jamana raini ya rinka bin wata yar ficiciyar yarinya.....

Dariya khalil yayi yace gwara ni inada yarinyar ay wani ma yayi mana kaida kake tsoron matan...

Kallonsa yayi yace Allah ya kiyaye naji tsoron mace har yanzu ni banga class dina bace ni kasan bana san raini....

JAWAHIRWhere stories live. Discover now