3️⃣1️⃣➖3️⃣5️⃣

259 19 5
                                    


            💞PRINCESS JAWAHHIR 💞

      Wattpad
  Mk_princess✍

                          3️⃣1️⃣➖3⃣5️⃣

Fitowarshi a wanka kenan yaji an danna door bell din side din shi cigaba yayi da shiryawar shi sai da ya gama a nutse ya dauki wayarsa ya fita parlor ajiye phone din shi yayi kan center table yaje ya bude kofa ganin Wanda ke bakin kofar ne yasa ya juya ya zauna a kujera yana daukan remote....

Zubewa yayi gaban sa ranka ya dade Allah ya biyama bukata barka Da asuba Da fatan an wayi gari lafiya ✊Allah ya taimake ka....

Ameen nasarah ya fada yana kauda kai....

Dama ranka ya dade hajiya azumi ce (mai dafa mai abinci ita kadai take bashi abinci yaci itace kamar uwar rain on sa tun yana karami  sai kuma Salma)  tace nazo na tambaya me za'a yi breakfast dashi ✊Allah ya biyama bukata.....

Wayarshi yake dannawa kamar ba dashi ake ba sai Bayan wani lokaci yace... Kunun gyada Da pepper soup din kayan ciki....

Angama ranka ya dade Allah biyama bukata ✊ na iya tafiya ko kuma na dakko kayan hada coffee din naga kamar ba'a sha ba....

No bana buka yace yana mikewa...

Tashi yayi yace tuba nake dan sarki magajin sarki ya nufi kofa ya fita....

Tsaki yayi yace sarauta ko wahala ya fada yana tabe Baki karasawa yayi wajan Da kayan tea dinsa suke coffee ya hada as usual ya dawo ya zauna yana kallo wayar sa ce tayi ringing dauka yayi yace ya maza wai yaushe zaka dawo ne kawani makale a abuja daga 2 days kayi one week....

Daga chan bangaren khalil yace wlh basaraken doctor ayki ne ya dan tsayar dani kuma kaima ay kasani ay dan rainin hakali kana wani cewa na dade bakai kasani nayi ma bincike ba....

Murmushi yayi dan ya san kome khalil ya gayamai shi ya jawo dan ya fishi Baki... Toh naji ya ake ciki any information....

Eh toh gsky babu dan na binciki hospital Da yawa ko zamu samu labarin su babu kuma nasa amin binci ke sosai Naje Sheraton hotel din sun duba min na gaya musu date din sunce eh dama suna neman wanda suka san su ma dan sun sauka amma kwanan su daya suka bar hotel din kuma bill din Da sukayi na wajan 2 weeks ne kuma sun ma bar kayansu a nan Da zasu bani kayan ma sai kuma suka ce na basu wata shedar Da zai nuna nasan su ni kuma kaga banida Kawai Nace musu zan dawo sai kuma shi commissioner of police Naje wajansa kamar yadda mai martaba ya umarce ni suna ta kokari wajan binci ke amma gasky SULTAN wannan abun dole fa sai kazo abuja cuz kaine kake Da duwani information Da ake nema akan case din nan....

Ajiyar zuciya yayi yace insha Allah zanzo munyi magana da commissioner din yamin bayani yanzu so nake na samu number su tace Zata duba a mail dinta yanzu zanje mu duba,....  kuma Ina so ka dawo sai ni kuma na tafi sbd yarinyar nan kazo ka duba kafarta you're a dermatologist so nake naga tana takawa Da kanta  amma sai wani yanga kake min kasan da bangare na ne da tuni an wuce wajan please  ina so su zo abuja ita da salma may be zai taimaka wajan samun lafiyarta....

Toh yallabai tuba muke naga dai wlh kanwar nan tamu ana bata kulawa harda extra ya fada yana dariya....

Kai fa matsalar ka kenan komai sai ka kawo wasa khalil you know JAWAHHIR is my responsibility dole na tsaya mata ta samu lafiya Bata da kowa a yanzu sai ni please kayi abinda nace...

Eh gskyne my man karka damu kuma nima nayi tunanin hakan dama ina shirin  gayama ko zamu dawo da ita wajan sadiya zai taimaka.....

Eh hakan za'a yi yanzu dai please ka dawo....

Angama basaraken doctor....

Smile yayi ya kashe wayar ya cigaba da shan coffee dinsa laptop din sa ya bude yana dan aikace aikacen sa wayarsa ya dauka yai Kira hello.... Dr  Sulaiman kana lafiya....

JAWAHIRWhere stories live. Discover now