💞PRINCESS JAWAHHIR 💞Wattpad
Mk_princess✍4⃣6️⃣➖5⃣0️⃣
Wata Kara sukaji da gaba dayansu suka tsorata JAWAHHIR kuwa gaba daya rikicewa tayi jikinta na rawa ta rufe idonta karar wani Marin ne yasa ta bude idonta.....
Meerah ta gani a durkushe da shatin hannun sultan a fuskarta hagu da dama kamar an zana....
Kama hannunta yayi ya murda ta sa Kara ya Kara murdawa cikin azaba muryarta na rawa tace please... Prince live me am sorry....
Kamar ba hannun mutum ya murde ba kallon JAWAHHIR yayi yace baby ku shiga ciki salma kamata ina zuwa JAWAHHIR da jikinta ke rawa dan ji take kamar ita akaima wannan rikon da kai kawai ta amsa salma ta kamata sukayi hanyar side dinsu...
Saida yaga sunyi nisa ya juyo ya kalli meerah da a yanzu ta hada wani uban gumi a tsugune wani kallo ya mata sai kuma yayi wani killer smile lips dinsa yayi beating kadan kara hade rai yayi kamar bai taba dariya ba ya cika ta jiki na rawa tana yarfa hanuwanta da takejin wata azaba...
Kamar me kallon kazanta yake kallonta yace wlh meerah ki kiyaye ni kinaso ki koma abuja babu kafafu ki nutsu ki san me kike yana gama fadan haka yayi gaba....
Amma da yake me hali kunsan ko me aka mai sai yayi halinsa tashi tayi tana hawaye kallonsa tayi tace akan wachan banzar yarinyar zaka min haka prince...
Juyowa yayi kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya dan dawo ya tsare ta da ido yace da ki taba JAWAHHIR gwara ki taba kowa a gidan nan dan JAWAHHIR "Amana ta ce"
Mai maitawa tayi "amanarka "Kamar me tunanin..... gaba yayi ya barta nan tana tunani da fuska a kunbure...
Kuka ta tafi tanayi kamar wanda ake kwakulewa ido haka ta shiga sashen mama fulani tana shiga mama fulani tace tofa ni wannan yarinya gsky bakida hal..... Kasa karasawa tayi ganin meerah da kuburarriyar fuska...
Zuwa tayi ta fada jikinta ta kara sa kuka lallashinta mama fulani ta fara yi saida tayi kukanta ta koshe sannan tace bazaki tambayeni me ya faru ba....
Mama fulani da gaba daya ranta ya gama baci tace to jira nake kukan ya miki magani idan yanayi...
Goge idonta tayi ta kalli mama fulani tace wlh sultan ya taboni yau ba so ba ko menene zan iya ajeshi gefe na yi masa rashin mutunci akan wata banzar yar tsakuwar yarinya zai daga hannu ya mare ni ya murdi min hannu har yana min Wronging akanta wai amanar sa ce....... Ta fada tana Kara sa kuka...
Gyara zama mama fulani tayi tace ban gane ba wacecec kike fada akan wace yarinyar ya mare ki....
Nan meerah ta bawa mama fulani labarin abinda ya faru shiru mama tayi kamar me tunani kallon meerah tai tace kira min abu.... (Abu amintacciyar baiwar Mama fulani ce du wani kitimurmurah da ita ake hadata)
Abu na zuwa ta zube tana kwasar gaisuwa Allah ya taimaki uwar dakina maganain kuka na me babban daki gani me ake bukata....
Cikin izza da kasaita tace abu ina son sanin wacece bakuwar SULTAN da kuma alakar dake tsakanin su....
An gama uwar daki na ki bani awa guda kadai ya isheni na kawo miki bayanin uwar dakina Allah biya miki bukata uwar dakina mike wa tayi ta fice...
Mama fulani kallon meerah tayi tace to ya isa haka kinsan dai ni bana san kukan nan ko tashi ki je dakin ki kwanta...
Tashi tayi tana shiga daki ta dakko waya ta kira mom ta bata labari tana kuka sun dan dade mom tana tsara mata abinda zatayi ma SULTAN cike da murna tace thanks so much love nagode da wannan advice din to mom ita kuma wannan yarinyar fa me za'a mata....