💞PRINCESS JAWAHHIR 💞Wattpad
Mk_princess✍5⃣6️⃣➖6️⃣0️⃣
Bangaran takawa kuwa mama fulani ce a zaune daga gefan ta ita da umar dake zaune kansa a kasa.
Kana kallon fuskar mai martaba kasan ransa a bace yake kallonta yayi yace ke nake saurare...
Murya na rawa alamar rashin gaskiya ta fara bayani tace ran sarki ya dade dama ina yawan magana akan yaron nan akan a rinka samai ido abubuwan da yakeyi sai aga kamar dan ba ni na haifeshi bane....
Dakatar da ita yayi cikin kakkausar murya yace ba wannan bayanin nake so ba abinda umar ya gayamin gaskiya ne...
Umar dake zaune hantar cikinsa ta kada lallai yau mai martaba ransa ya baci ji yadda yake kiran sunansa karara.
Cikin ina ina tace to gaskiya ne amma ni ban so umar yazo ya gayama ba sultan da meerah du nawane kuma nasan sharrin shaidan ne du fitinar sultan nasan bazai yi a gida ba ta fada tana kara sunkuyar da kai..
Takawa ne yace fulani har yanzu ba'a bamu amsar tambayar mu ba ko sai mun maimaita miki....
Tuba nake ranka ya dade Allah ya huci zuciyar ka abinda ya faru shine jiya da yamma meerah ta shigo fuskarta a kun bure kuma ta rike ciki tana kuka da na tambayeta tace sultan ne to dayake du nasan halin su shi bashida hakuri ita kuma rashin kunya to shiyasa ban ko tambayeta me ya mata ba haka ta karaci kukanta wajan magriba kuma sai na je dakinta na sameta tana murkususu tana ciwon ciki tana kuka aka bata magani amma sai ciwon ya karu bayan magariba sai abun yayi tsanani sai na ayki abuu nace ta je ta kirawoshi ya dubata ta je ta dawo tace ta gayamai amma be bata amsa ba kuma me makon ya biyo ta a baya sai ya komawarsa dakin sa Na jinjina maganar saboda mamaki irin na dan yau muka sa ta a gaba tanata murkususu sai abuu tace a bata xuma da ruwan dumi shine ta hado ta bata sai kuwa mukai sa'a ciwon ya lafa har ta samu bacci na ce abuu ta zauna da ita na tafi daki zanyi sallah nayi sallah na gama komai sultan be xo ba da kamar na kirashi sai kuma na fasa tunda naga ta samu sauki gashi kuma dare yayi har 10:00 na koma dakin meerah na tarar har lokacin bacci take dan haka nace abuu taje ta kwanta tunda baccin yayi nauyi kuma ganin ina kusa da ita na rinka lekawa ina dubata abuu ta tafi ta kwanta nima sai na tafi ina kwance sai naji na kasa bacci wajan sha biyu sai na tashi nace bara ba dubo ta ina dosar daikin kuwa sai naji ihun ta kawai ina shiga....
Sai ta fara sharar hawaye kamar gaske ( kai Allah ka rabamu da makiyi) tace kawai naga sultan a kan gadon meerah ba riga a jikinsa suna kokawa yana kokarin rabata da kayanta ta fada tana share hawaye...
Shiru takawa yayi kawai yana kallonta idonsa yayi jaaa shi kadai yasan me yake sakawa a zuciyar sa ajiyar zuciya yayi sai ya kalli umar yace jeka ka kiramin ummahn ku da sultan idan khalil be fita ba shima kace yazo..
Har umar ya tashi da sauri sai kuma yace dawo ka zauna kira min Aminar a wayarka kace tazo wayar sa dake gefansa ya dauka ya kira ummah yace Maryam ki zo keda yayanki maza...
✴✴✴✴✴✴✴✴✴
Yana kashe wayar ajiyewa tayi ta kalli sultan dake durkushe dafa kansa tayi tace babana ina umartarka da ka karbi du hukuncin da mahaifinka xai maka kuma ina so kusa a ranku dukkan mai hakuri shi yake da riba kuma ku rinka tunawa akwai Allah kuma yana sane damu sannan ina so kayi shiru ka saurari abinda ta fada idan ya tambayeka ka fadi abinda ya faru sai ka gayamai abinda ya faru ku tashi kuje nima ina nan yafe...
Haka suka tashi sultan da fuskarsa tayi jaaa idonsa ma haka manyan idanun nan nasa Kamar zasu fito kowa ya ganshi yasan yau an tabo namiji sallama sukayi takawa ne ya amsa suka zube sukai gaisuwa ya amsa musu sai kuma suka koma gefe suka zauna sauna zama ummah ta shigo da sallama ta nemi guri itama ta zauna.