💞 PRINCESS JAWAHHIR2⃣💞
Wattpad
Mk_ princess✍3️⃣6️⃣➖4️⃣0️⃣
🌟Ga jawahhir kuma a riga ko suwaye suka tsinceta❓
🌟zata farfado idan ta farka ta gansu ya zatayi❓
🌟me yasa baffa yake mata kallon sani❓
🌟waima a wani gari aka tsinci jawahhir ❓
🌟su waye su baffa meye asalinsu da labarin su❓
🌟me meerah zatayi ma sultan ya manta da jawahhir ❓
🌟kuna ganin za'a iya gano inda aka tsinci jawahhir kafin kwana uku abinne asirin da za'a manta da ita ❓
🌟Ana binne wannan asirin ko ba'a binnewa❓
🌟 yaya sultan zai tsinci kansa cikin wannan halin na batan jawahhir ❓
Nan ya kara jingida da bango dan du ya galabaita ya fita hayyacinsa ganin Wanda aka shigo da su ne hankalin alh barau yayi mummunan tashi iyalinsa ne hanunsu du da handcuff suka zube a gabansa cikin tashin hankali yace wlh yallabai du abinda kake so zan gayama amma Dan Allah kar a cutar min da iyali....
Sultan da ke zaune yana huci tun shigowarsu cikin kunar rai yace kai kana son naka iyalin amma ka hallaka wasu iyalin sbd burinka kasa magana yayi sbd wani daci da yake ji a zuciyarsa DPO ne yace bamu cikaken amsoshin da muke bukata.
Alh barau ya dago yace na hadu da alh yousuf tafeeda a jirgi inada muka zauna waje guda shida iyalinsa da jaririyar yarsu hira muka Dan fara anan nagane alh yousuf be San kowa a Nigeria ba Dan na fara tambayarsa a wani gari yake a Nigeria kallo na yayi yace ni ba Dan Nigeria bane ni Dan Niger ne amma dai na taba zuwa Nigeria sau daya munzo abuja yanzu ma kuma abujan zani nan na nuna masa nima abuujan zani nima nage Niger ne sbd wani ayke da ogana ya sani ni dillalin gidaje ne ogana yana yin estate a nan abuja to ni nake kula dasu to akwai wani abokinsa a nan Niger sai yayi sha'awar irin sana ar shine ogana yake turani dan na nuna mai yadda sana'ar da yadda aake bawa masu San haya ko siyan Estate din ....
Jin haka yousuf tafeeda yace yanzu zaka iya sama min haya a cikin Estate din ogan naka nan yace ba matsala dama ni ay sana'ata keanan nemo masu San gidan ko na haya ko na malaka ....haka maukaita hira Wanda saidai maman jawahhir ta kallemu kawai har muka sauka a nan na lura da yousuf fa be San ko ina a abuja ba kallonsa nayi yayinda motar ogana tazo daukata nace ko zan taimaka muku da wani Abu kafin intafi ajiyar zuciya yousuf yayi yace yanzu dai da hotel nake so na samu me dan sauki kafin ka samo min hayar gidan murmushi nayi nace idan bazaka damu ba muje gidana mana ku zauna da iyali na mana zuwa gobe sai muje kaga Estate din ka ga wanne zaka iya zama...nan yousuf yayi min godiya muka shiga mota aka loda kayansu a booths na shiga gaban motar ina jin maman jawahhir nayi masa magana kasa kasa tace kana ganin ya kamata mu yarda da Wanda bamu sani ba har mu bishi gidan sa karfa muje ya cutar damu kafin ya bata amsa na juyo nace maman Baaby ki kwantar da hankalinki insha Allah kuna cikin aminci yousuf ma inaji yana kara tausarta haka mukaje gidana nasa matata ta musu tarba me kyau satin su daya a gida na nan naga maman jawahhir ta sake sosai da iyali na a lokacin muka je ya zabi wani irin ready-made din Estate da muke saka komai na gida mu siyar ganin haka na tabbatar da zargin danake a zuciyata na wannan mutanen masu kudi ne kwana biyu suka kara suka koma daya daga cikin Estate din ogana dake gwarinfa Wanda gida hudu ne kawai a ciki tun daga nan muka kulla zumunci da yousuf bayan kamar wata daya ya nemi yana son gani na naji yace min alh barau ina son na nemi shawarar ka ne game da business din da nake so nayi Wanda dole sai na samu dan gari Wanda yasan gari shiyasa na meka nan na nemi jin wani business din yake so ya fara yace yana so ya fara saida kayan asibiti ne yana shigowa da machines din da ake bukata a hospital da gadaje....
Jin irin business din ne yasa nasan wannan yazo da dukiya nan na gyra zama nace zan hadashi da ogana Wanda dama shine minister lafiya ...
Yaji dadin haka sosai nan muka sa rana mukaje muka samo ogana nan ogana yace zai sama masa hanyoyin da yadda za'a rinka shigo da kayan asibitin expecially na gamnati nan mukayi godiya muka taso ...
Harga Allah a lokacin banji ina son cutar da yousuf ba hasalima na daukeshi aboki kuma amini sbd a lokacin haka ya dauke ni du abunda zaiyi sai ya nemi shawarata duda ina ganin kamar na samu Wanda zan karu dashi ganin daga lokacin da muka hadu zuwa yanzu ya min alheri da yawa nida iyalina hakan kuma ya kara min kafin gwiwar na rikeshi gam ....
A haka dai baban jawahhir ya fara business dinshi da taimakon ogana minister da kuma ni wata rana yace min zai je Niger ya dawo yaje beyi sati ba ya dawo bayan ya dawo ne ya kara neman shawarar zai bude comperny babba yana so ya samu fili ya fara gini jin wannan abun ya girgizani har na fara jin ina so nasan shi waye ne wannan mutumin sbd na lura kamar zuwa Niger din da yaje ya dawo da maku dan dukiya....
Nan na nuna jin dadi na na nuna masa ay wannan ba karamin ciga bane nan na bashi shawara nace ko mister zamu samuu mu gayamasa wannan maganar nan yace to babu laifi nan muka nemi appointment muka hadu da minister nan ya nuna jin dadinsa sannan yace shi kuma zai bada godun mawar hadashi da masu ilimin business din sosai da mutanen da ya kamata ya dauka na company nan suka masa godiya a nan ne minister ya karbi number yousuf sukayi exchange number nan muka taso ba'ayi 2 years ba company M.A.Y health services Ltd ya zama cikaken company da Nigeria take matukar morar sa dan babu kalar machines din da baya shigowa da shi masu foundation da dama suna zauwa company yana taimaka musu da abubuwa da dama da marasa lafiya suke bukata....
Ganin idan yousuf zai ga minister baya bi ta kaina waya kawai suke su hadu sai yasa na fara jin wani iri saboda naga ya rage gayamin abubawa da yake ciki...
Wata rana naje gidansa bayan munci abincin dare na nemi mu yi magana yace yana jina nace yousuf yanzu mun zama yan uwa yakamata mu San juna mu San asalin juna ina taso na ma wata tambaya amma sai naji kamar be shafeni ba ...
Baban jawahhir ya juyo yace hakane barau na dade ina jiran wannan tambayar dan ita zata sa na kara yadda dakai dan du mutumin kwai zai so yasan Wanda yake mu'amulla naji dadin haka sosai zan baka labarina da dalilin da yasa na bar kasa ta na zo Nigeria nake kuma neman kudi a Nigeria.
🌟Ga jawahhir kuma a riga ko suwaye suka tsinceta❓
🌟zata farfado idan ta farka ta gansu ya zatayi❓
🌟me yasa baffa yake mata kallon sani❓
🌟waima a wani gari aka tsinci jawahhir ❓
🌟su waye su baffa meye asalinsu da labarin su❓
🌟me meerah zatayi ma sultan ya manta da jawahhir ❓
🌟kuna ganin za'a iya gano inda aka tsinci jawahhir kafin kwana uku abinne asirin da za'a manta da ita ❓
🌟Ana binne wannan asirin ko ba'a binnewa❓
🌟 yaya sultan zai tsinci kansa cikin wannan halin na batan jawahhir ❓
🌟menene asalin baban jawahhir kuma me ya rabashi da kasarsu ya dawo Nigeria ❓
Mu hadu a next page more comments & vote more typing
YOU ARE READING
JAWAHIR
Storie d'amoreIts all about love and Royal family life.... Read and find out ❤❤❤