💞 PRINCESS JAWAHHIR2⃣💞
Wattpad
Mk_ princess✍2️⃣1⃣➖2️⃣5️⃣
me ango zaiyi da ya ga amarya da jawahhir da suka hada ido❓
🌟 me su aunty uwani suke planing ne game da dinner za'a yi ko baza'a yi ba❓
🌟 ya maganar abinda za'a yima jawahhir na kurciya zasuyi ko sun fasa❓
🌟 ya case din Alh barau an kamashi ko ba'a kamashi ba ❓
🌟ya maganar S I meye a zuciyarsa game da jawahhir Musamman yanzo da yake ganin sultan yayi aure❓
Jawahhir da ta kare musu kallo salma ce ta taba ta tace ma twins gasu nan sun tawo daga kai tayi ay kuwa yayi dai dai da karasowa dai dai inda suke kamar ance ya daga ido ay kuwa suka hada ido abinda yayi shi ya bama mutane........
Wani murmushi da wani irin kallo yake ma jawahhir Wanda yake da fassara daban daban meerah kuwa kallon sa take sai ta kalli inda yake kallo ....
Sadiya dake gefe itama yau dai taga abinda salma take gani shikuwa gogan ga alama ma shifa be lura da wata amarya ba Dan jawahhir kawai yake kallo yana wani murmushi itama shi dake kallo da mamakin mutane sai suka ga ya daga hannu memakon yayi gingina ✊️ alamar kabar gaisuwa sai suka ga yayi mata alamar 👌 da dazu sadiya tamata alamar tayi kyau kunya taji tayi murmushi ta rufe fuska wannan murmushi da tayi ji yayi kamar ta cire mishi du wani damuwar shi, ..haka yayi gaba yana murmushi ko kallon inda amarya da kawayenta suke biyi ba ..
Meerah ji tayi kamar tayi hauka kawayenta sai magana suke suna tambayarta wecece wachan din wasu na cewa ko favourite sister sa ce ...
Zee ce tace amma yana son sister nan tashi kodayke gaskiya kyakyawa ce kuma tayi kyau beyi karya ba Samantha ce tace gaskiya meerah na yadda mijinki nada kyau ga sisters dinsa du masu kyau expecially wachan favourite sister nashi ....
Meerah da take jin kamar ta Harbe su ta daka musu tsawa ya isa ban San hauka baku ga abinda prince yamin bane kun zauna sai wani maganar banza kuke kawai tayi gaba ta shiga cikin gida Wanda su jawahhir sun dade da shiga ango na shigewa suma suka shige.....
Meerah na shiga side din mama ta tuje Dan kwalin ta fara kuka kamar wata mara hankali kawayenta da su mommy kowa tsayawa yayi yana kallonta mommy ce ta kamota meerah menene kuma ...
Kuka take tace mommy wannan yarinya itace matsala prince yana wulakantani a kanta ta kara sa kuka ta kalli mommy tace wlh ko a kashe yarinyar nan ko na kashe kaina kowa ya huta kawayenta da suka tsaya suna kallonta dansu fa fast gane me take nufi ba aunty uwani ce taja hanunta da na mommy suka shiga ciki ita kuwa mama fulani dake zaune haushi meerah kamata yake kamar ta mata duka Dan wannan asirin da sukayiwa meerah na son sultan ya fara haukata musu ita....
Aunty uwani ce tace haba meerah meyasa ke baki da wayo ne ance ki dena nuna kishin ki a fili ki rinka controlling fushinki kina so ki tona mana asiri me yarinyar ta miki da har zakice zaki kashe kanki....
Cikin kuka tace aunty a gaban kawayena sultan ya wulakantani ko kallon inda muke beyi ba amma sai gashi yana kallon shegiyar yarinyar nan har yana daga mata hannu mutane sai magana suke su kuma dakikan friends dina suna cewa wai favourite sister sa ce tana da kyau bama su ga wulakantani da yayi ba ta kara fashewa da kuka ..
Mommy dake tsaye ta zura mata ido jin zuciyata take kamar ta fito Dan takaici ta kalli meerah tace princess kwantar da hankalin ki yau ba sai gobe ba zamuyi maganin yarinyar nan kuma kallon da yamata daga yau bazai sake mata shi ba ki kwantar da hankalin ki kije kiyi celebrating dinki keda kawayenki karki kara nunawa kowa kin tsani yarinyar nan ko sun tamayeki kice kawai kishi kike amma kema kina santa tunda yana ji da ita karki kuskura sugane jawahhir ba sister dinsa bace Dan idan suka San haka kome ya sameta zasu zarge ki ina miki albishirin gobe za'a nemi jawahhir a rasa ta fada tana wani murmushin mugunta...