💞PRINCESS JAWAHHIR 💞Wattpad
Mk_princess✍6️⃣1️⃣➖6⃣5️⃣
Sallama tayi suka amsa du sunyi jugum jugum ta durkusa tace ranki ya dade gwaggon ta shigo sashenta amma ta hau sama shine nace bara nazo na sanar miki gyada kai kawai salma tayi JAWAHHIR kuwa da ta hada gwiwa ko dagowa batayi ba bare ta san da shigowarta salma ce ta zo ta dafata ta dago taso muje Ummah ta dawo daga wajan takawa..
Girgiza mata kai tayi tace salma I can't baki san me nake feeling ba cabana ba karamin faduwa yake ba kawai ki je bana so naje naji wani abun da zaisa na shiga tashin hankali dan wlh zuciyata Zata iya bugawa.
Insha Allah ma bakomai amma tunda kince ba zaki ba bari ni naje naji menene yake faruwa amma please ki kwantar da hankalin ki kinsan fa ba lfy ne dake ba.
Dan murmushi tayi wanda kana gani kasan iya fuskarta ne Ok Allah ya sa muji Alheri..
Ameen salma tace ta fita bangaren ummah ta shiga akace ta hau sama tayi mamaki dan ummah kwanciyar bacci kawai take hauda ita sama idan ta sakko komai a dakunan kasa take yi kauda tuna nin tayi ta hau sama ta samu ummah a zaune a kan sallaya tana sallah ba ta dade da zama ba ...
Sai yayi sallama idonsa yayi jaaa kamar garwashi ba karamin tsorata salma yayi ba muryar ta na rawa ta amsa sallamarsa zama yayi kawai yayi tagumi...
Ummah ce tace yaya ka dawo gaba daya suka juya dan du basusan ta idar ba kowa da tunanin da ya addabi zuciyar sa kauda musu da tunanin tayi tace yaya.
Cikin damuwa da tashin hankali muryar sa na rawa yace ummah munzo da gawar suna chan bangaren takawa za'a musu sutura ya dago kansa ya dubi ummah yace ummah bansan ya zanyi da jawahhir ba ban san ya zan gayamata an kashe mata iyaye ba an musu yankan rago ya fada yana runtse ido...
Ummah kuma tace innalillahi wainna ilaihi raji'un.
Salma da ta daskare a wajan ta kasa koda motsi kawai sai jin karar jawahhir a kofa da sauri ya tashi ya bude kofa suma suka biyo shi a baya..
Baya baya take yi tana girgiza kai ta toshe kunnen ta tana kallonsa tace karya ne nace karya ne bata san ta kai karshen step din ba ta ay kuwa ta fadi ta fara gangarawa aguje ya bita amma bai iya kamota ba saida ta je karshen stairs din kanta yayi da sauri ya dagata amma me har ta suma kallon wata hadima yayi a rikice yace bani ruwa Dan kwalinta ya cire ya tare wajan da kanta ya bugu har ya fashe ..
Salma ce ta karbi ruwan ta mika mai ya zuba mata a fuskarta du ya rude kamar ba dr ba ganin bata farfado ba..
Ummah tace kutafi asibiti kawai ay bai tsaya jin karashen maganar ba kuwa ya dauketa ya fita da ita salma ce ta bishi tundaga nesa yake kwadawa sarkin mota kira a rude ya fito ganin abinda yake faruwa shima yayi sauri ya shiga mota salma ce ta bude mai baya ya sata a ciki shima ya shiga gaba ta shiga suka ja suka tafi asibiti dake nan kusa da su...
Suna shiga kuwa sai ga dr S I da sauri SULTAN yayi kansa yana nuna masa jawahhir dake rungumeta a kirjinsa gaban rigarsa du ya baci da jini nurse's ne suka zo suka karbeta sukai emergency room sukai da ita aka fara bata taimakon gaggawa..
Dr S I ne ya fito ya kalli sultan da du ya fita a hayyacin sa dafashi yayi da sauri yace how's she .. Comedown mana dr ya kake Abu Kamar ba likita ba ana dubata kuma insha Allah babu komai dan buguwane kawai da tayi a ka kuma zata iya farfado wa a koda yaushe....
Ajiyar zuciya yayi yace bazaka gane bane s i damuwar da take kaina ba kowanne kaine zai dauka ba mikewa yayi yace muje na ganta nan suka shiga dakin har an mata dressing din gurin daya fashi tana kwance ansa mata drip ana allura a ciki dr da yake dubatan ya kallah yace yaya meye condition din ta...