💞PRINCESS JAWAHHIR 💞Wattpad
Mk_princess✍
1️⃣0️⃣➖1⃣5⃣
( ➡Note karku manta nace muku na kirkiri sonan garin ne sbd bana so labari na ya nuna kama kowacce masarauta)✴✴✴ Soyaki✴✴✴
Babban gari ne dake nan kasarmu Nigeria gari ne dayake da ruwa biyu hausa da kuma fulani, musamman masarautar garin asalin fulani ne wannan suna na masaurantar soyaki ya samo asili ne ta wani sarki da yake shine na 13 kafin kakan me martaba na yanzu saka makon a da ana yin yaki tsakanin wannan masarautar da wasu garuruwa sarki soyaki shine sarki na farko da ya kawo karshen yake yaken da ake a wancan lokacin ya cisu da yaki kuma shi ya tabbatar da samuwar kwanciyar hankali da addini a wannan lokacin shine aka maida sunan sa ya koma so yaki kinji asalin sunan so yaki....
***
Bari na takai ta miki sarki Abdussalam Abubakar soyaki shine sarki na yanzu yana da mata uku kafin ya zama sarki yana mata daya ne me suna ummusalma itace matar da ya fiso a duniya saboda auren so sukayi ita ba yar Nigeria bace yar yemen ce karatu da maimartaba yaje suka hadu da ita har sukai aure bayan gama karatunsa suka dawo nan ita da kanwarta mai suna maryam.... bayan dawowarsu da shekaru 5 Allah yayiwa sarki Abubakar rasuwa wato baban me martaba nan aka nada sarki Abdussalam ba ayi shekara daya ba mahaifiyar sa ma tabi mijinta sai abokiyar zamanta me suna gwagwan katsina me suna mariya nan tasa sarki ya dole ya kara aure acewar wai matarsa bata haihuwa duda baya so haka yai biyayya ya auro mama fulani Wadda gwagon katsina ce ta hada Dan yar Dan uwanta ce da take riko tunda akai auren su ummah ta dena samun kwanciyar hankali ita da kanwar ta Maryam kullum cikin takura tana matar sarki amma kullum hankalinta a tashe saboda masifar gwagon katsina da na mama fulani maryam kuwa bata sakewa a gidan kanwar sarki hajiya zainab da ta auri waziri ita kadai suke jin dadin ta wadda umma ta girmeta Dan ta bata kusan shekara 3 zuwa hudu ba a dade kuma da aurenta ba suka zama kawaye ita da umma haka ta zama kamar yar Uwa a wajan ummah ba a dade ba umma da hajiya Zainab suka samu ciki wannan cikin ya daga ma su mama fulani hankali ba irin abinda ba ayi ba Dan a raba ta dashi ansha bata magani ta sha tai ta wahala amma baya zubewa wata ranar juma'a da asuba ta haifi Dan ta Abubakar Abdussalam Abubakar soyaki shine ya yaya SULTAN Wannan ranar ta zamewa su mama fulani bakar rana dan ba haka suka so ba gashi ita mama fulani ko batan wata bata taba yi ba a daren ranar hajiya zainab ma ta haifi nata dan Ibrahim Abdullahi waziri shine yaya khalil Dr da yake dubaki Ba karamin farin ciki sarki yayi ba dan kullum burinsa kenan umma ta riga mama fulani haihuwa dan yasan du rashin haihuwar ne yake sawa ake mata du abinda ake mata dan yana sane da komai amma ba yadda zaiyyi tunda gwagon katsina uwa ce a wajanshi saida umma tayi shekara biyar mama fulani ta haifi da daya umar wanda basu da nisa da sadiya da hajiya zainab ta kuma haifa.... Shekara biyu tsakani mama kilyshi ta kuma haifar Mustapha tunda ga nan bata kara haihuwa ba....