3️⃣6️⃣➖4️⃣0️⃣

22 2 0
                                    


💞 PRINCESS JAWAHHIR2⃣💞

Wattpad
Mk_ princess✍

3️⃣6️⃣➖4️⃣0️⃣

🌟Wane hali jawahhir take ciki❓

🌟 ina jawahhir take❓

🌟 me meerah zatayi ma sultan ya manta da jawahhir ❓

🌟kuna ganin za'a iya gano jawahhir kafin kwana uku abinne asirin da za'a manta da ita ❓

🌟Ana binne wannan asirin ko ba'a binnewa❓

🌟 yaya sultan zai tsinci kansa cikin wannan halin na batan jawahhir ❓

A ranar dai gidan nan babu Wanda ya runtsa ko ina security's ne suna bincike du giraman gidan nan da yake gari guda an dubashi ba jawahhir babu alamarta sultan tun yana dakewa har zuciyarsa ta fara karaya Dan ya fara hawaye wanda baisan ma yana yinsa ba su salma kuwa kuka suke suna addu'a kamar yand umma takeyi kowa yana cikin tashin hankali na wannan masifa da ta samesu ....

Bagaren su mama fulani ganin zaman jimamin yaki karewa nan sukayiwa mai martaba sallama suka tashi suka koma bangarensu sukayi kwanciayrsu dama abun ba damunsu yayi ba....

Haka gari ya wayewa su sultan babu Wanda ya runtsa kowa abun na damunsa haka sukayi sallah nan mai martaba yasa malamai suyi ta addu'a da rokon Allah...

🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Farkawa tayi ta ganta a wani daji ba gida gaba ba gida baya kamar mahaukaciya haka ta miki cikin tsanin tsoro ihu takeso tayi amma ta kasa idan ta Bude baki sai taji sautin muryarta ya dauke a cikin irin tashin hankalin da take ta rasa me zatayi kawai sai ta fara gudu ga dare gashi bata gane komai kawai gudu take cikin tashin hankali har taji tagaji da gudun Dan Jeff kafarta kawai take bata gane komai ji tayi kanta ya bugu da wani Abu da bata San menane ba nan ta fadi sumammiya......

Bayan ya idar da sallah asuba ne ya fito yana Kiran ta hauwa hauwa wata yarinya yar kyakyawa ta fito wadda shikarunta be wuce 14 zuwa 15 ba tana turo baki wata mata tace anya hauwa bazaki dena sakalci ba ace a rayuwanki kullum sai ayi miki magana kizo kuwuce ga furar nan na gama ki dauka ko tafi baffa dake kwance ga alama baya jin dadi yace kai mamman tafiyarka kiwonka nashe ka dena jiran uwata tunda kullum sai tasa ka makara kayi sauri kasan yau zamu shiga cikin gari ....

Mamman Wanda shi yake Kiran hauwa ya dau sandarsa zai tafi hawwa tayi sauri tace ayya yaya gidado jirani mana ta fito tana sauri inna dake tankade tayi dariya ganin yadda hawwa take sauri kar yayanta mamman ya tafi ya barta yanda sukeyi kullum yauma haka mamman ya raka hauwa har bakin shiga garin dake kusa da rugarsu ya dawo ya kada shanunsa Dan ya kaiso kiwo hanyar dajin yayi yana cikin tafiya ya hango kamar mutum a kwance sandarsa ya dakko daga jikin jakin da yake hawa idan zaiyi nisan kiwo da ya daure sadar a jikinsa saida ya dan karasa wajan sai yaga kamar mace da dan sauri ya karasa ganin wata kyakyawar aljana yayi me kyau ga gashi ga sutura ta alfarma nan jikinsa ya fara rawa abunka da dan malami kuma shima yanda nasa ilimin nan ya fara karato addu'o in neman tsari daga shedanu ganin bata bace ba yadan kara matsowa da sandarsa ya dan taba ta sai yaga kamar kafarta ta motsa ajiyar zuciya yayi a fili yace wannan mutum ce amma me ya kawo ta nan dan tunani yayi sai ya dakko yar karamar wayarsa a aljihunsa ya kira baffa baffa dake nan inda suka barshi shima wayarsa tayi kara da sauri ya dauka jin muryar mamman ya gane shine dan baffa bai iya karatun boko ba daga bangaren manman yace baffa kamar nayi gamo wata yarinya na gani a daji me kama da aljanu saida nayi addu'a sai naga ay mutum ce amma inata tunain ya zanyi shine na kiraka da sauri baffa ya tashi zaune yace haba maman ka dakkota kawai ka yadda da Allah kasa a zuciyarka dan Allah zakayi ka kawo ta nan mu dubata nan mamman yace to ya kashe wayar kallonta ya tsaya yi bai taba yiwa mace irin wannan kallon ba wani Abu yaji yana fusgarsa addu'a ya kara yi nan ya dauketa jin bata da wani nauyi yace ace ma ba nauyi nan ya dorata a kan jakinsa ya sashi a gaba ya kada shanunsa ya nufi rugarsu. Suna zuwa gida ya shiga da ita inna ta karbe ta nan suka kwantar da ita bakin bokkar su baffa da ya fito daga wata burka da allo da kwarya a hanunsa sai yaga jawahhir ya kura mata ido taunin yake kamar ya taba ganin fuskarta kamar kuma kama take masa da wata wadda ya taba gani nan dai ta  zauna yana cewa inna kawo ruwa na wake mata rubutun a fara bata mugani ga alma ba yar masu shice ko ma menene mu kyautata wa Allah zato Allah ka  bamu ikon cin jarabawa ameen inna tace shi kuwa mamman in banda kallon jawahhir dake kwance babu abinda yake yakasa cewa komai dan shi be taba ganin mace me kyanta ba duda fuskarta ta nuna alamun wahala amma kyawunta bazai taba bata ba kyakyawa ce sosai Dan har yanzu wani sashi yana tantama na ganin jawahhir kamar ba mutum ba .....

Safiya nayi sultan police station din da aka tsare alh barau sukaje nan aka fito dashi DPO ne da kansa ya fara yiwa alh barau tambayoyi yace muna so ka bamu labarin rayuwarka da yadda akayi ka hadu da baban maryam kuma ka gaya mana dalilinka na kashe su me suka maka kuma ka gayamana ina ka kai maryam.

Cikin firgici ya dago kai yace wlh yallabai ban San inda maryam take ba kuma  wlh ba hanuna a batanta ya fada yana maida numfashi dan Alh barau ya chanza kala saboda azabar da yasha ba kadan bace Dan a yanzu ji yake ko tamabayar yadda uwarsa ta haifesa aka masa zai yi kokarin bada amsa (😅 nace alh barau yaji wuta)

Nan ya kara jingida da bango dan du ya galabaita ya fita hayyacinsa ganin Wanda aka shigo da su ne hankalin alh barau yayi mummunan tashi iyalinsa ne hanunsu du da handcuff suka zube a gabansa cikin tashin hankali yace wlh yallabai du abinda kake zan gayama amma Dan Allah kar a cutar min da iyali....

Tofa yau dai rubutun ba yawa nima dai zan so naji yadda zaa kare da alh barau .

🌟Ga jawahhir kuma a riga ko suwaye suka tsinceta❓

🌟zata farfado idan ta farka ta gansu ya zatayi❓

🌟me yasa baffa yake mata kallon sani❓

🌟waima a wani gari aka tsinci jawahhir ❓

🌟su waye su baffa meye asalinsu da labarin su❓

🌟me meerah zatayi ma sultan ya manta da jawahhir ❓

🌟kuna ganin za'a iya gano inda aka tsinci jawahhir kafin kwana uku abinne asirin da za'a manta da ita ❓

🌟Ana binne wannan asirin ko ba'a binnewa❓

🌟 yaya sultan zai tsinci kansa cikin wannan halin na batan jawahhir ❓

Toh amsoshi  da yawa sai Mu hadu a next page more comments more typing 🤝

No edit

JAWAHIRWhere stories live. Discover now