Ba abinda yake tashi a club din sai kida, rawa da hayaniyar mutanan wajan, nan aka fara gabatar da party, farko dance computation ne sai pick and obey sannan cutting the cake , nan Mc ya fara gabatar da abinda ya tarasu, Amrah da firdausi ne suka fito sannan wani saurayi da Jackson suma suka fito, Mc yace yanzu zasu fara but under one condition duk Wanda sune loser toh za'aci taransu, nan kowa suka dage Lalle su zasuyi winning, ahaka har akaci su Amrah, akazo pick and obey, firdausi ta dauka kiss and hug aikuwa nan taje tayiwa friend dinta kowa sai tafa mata akeyi, akazo kan Amrah kawai taje tadauki kiss and sip atake kirjin ta tafara duka uku uku, ita harga Allah bataji zata iyaba but people around her fah?, gashi all ears on her, Jackson yamata signa da ido nan tadan hada courage sannan tayi kissing Jackson nan aka ringa shewa aka kawo mata Alcohol akan tayi sipping, duk jinta take wani iri saboda wannan shine karonta na farko data fara kissing wani gashi kuma wai zatayi sipping alcohol, amma data tuna cewa duk 'ya'yan manya ne kuma za'a mata kallan bakauyiya kawai tasamu wani courage, takarba barasan sannan tayi sipping, tun kafin azo yanka cake Amrah tafara jinta somehow different, lokacin da zasu yanka cake kawai tayi isolating kanta tayi gefe tazauna chan saiga wani yazo yace "Hey beauty!" Ta dago tana kallon sa amma takasa cewa komai, da yaga she's not in her normal self sai yace "let me show you something" yakama hannunta ita kuma tana kokarin turgewa kawae yajata suka fita,
Jackson dabe ganta ba yazo dubata Kenan kawai yaga wani na shirin fita da ita, da gudu shi yaje yasha gaban sa yace "lafiya malam Ina zaka kaita?" Amrah kawai tamika wa Jackson hannu akan ya kamata, yakamata yayi mota da ita yana tambayarta lafian ta kuwa? Nan tace masa she's not in her normal self yaringa dariya yace "karde kice dan sipping dinnan ne ya maidaki haka?" tace "take me home" yace "your wish is my command baby" yatada motan nan Amrah taga pass 10 to 11pm take taji wani tsoro ya shigeta tace "har 10 yayi wayyo ni" Jackson yayi dariya yace "danma bakiga 2 ba" tace "this is my first time so bansan ya za'ace min agidan ba" kawai saiga hawaye yana saukowa, suka Kama hanyar gidansu Amrah.Sultan sai baccinsa yake hankali kwance dan agajiye ya kwanta, 15 minutes to 11 wayansa yayi ringing ya bude ido yaga Ashe wata girlfriend dinsa ce data tafi karatun India, nan yatashi yadau wayan yana mussuka ido, yace "Hey don't tell me har kunyi landing?" Cikin shagoba tace "yanzu ne fah" nan suka dan fara hira sai yaji kamar bacci zai kwashe sa kawai yayi deciding yafita environment din gidan wata kil in fresh air na dukansa bazaiyi baccinsa ba, yafita waje suka cigaba da hiransu chan yaji sayuwar mota still be kawo komai a mind dinsa ba shidai wayansa yakeyi hankali kwance, yaji Ana knocking gate din gate man ya bude bayan ya sake jin anrufe gate din sannan yaji anja mota antafi, juyawan da zaiyi kawai yaga Amrah tashigo daga ganinta zakasan she's not normal, kawai yasake baki yana kallon ta aransa yana cewa Amrah? What is she doing outside by this time?, tazo zata wuce shi kawai tagansa take zuciyarta ya sinke, ta fisge kawai tawuce ciki,.
Ummi (Abidah) tasaba shan coffee every blessing night, Yau dukda gajjiyarta hartayi bacci amma sai data farka, kawai taji tasauko kasa tahada da kanta tunda tasan kowa yayi bacci and she don't want to disturb anyone, bayan tagama hadawa tafito daga kitchen kawai tasaya a parlour tana sha kawai taji anbude kofar parlourn juyawan da zatayi kawai taga Amrah ce tashigo atake dukkan su biyu sukaji sinkewan zuciya, Amrah tayi upstairs da gudunta, Abidah tayi shiru for some seconds sannan tayi dakinta, saiga sultan shima yashigo amma shima tunanin yakeyi,
Amrah nashiga dakinsu Dua tajiyo tana kallonta ba wadda yace da wani komai, har Amrah tayi wanka tafito still tanajin ta wani irin tasa sleeping dress ta kwanta kawai saitaji Dua tace "Amrah from where mummy ma tazo bata sameki ba?" Amrah tayi saki sannan tace "inda naje is none of your business okay?" Dua bata sake cewa komai ba kawai tayi Addu'o'in bacci takwanta.
Yau agidan antashi da wuri saboda Yau su daddy zasu meeting, as usual Dua da house maid dinsu Fatima suka fara aikinsu, mommy ce ta sauko ta fada musu breakfast dinda zasuyi sannan ta koma, sultan da Aryan sunfito zasu fita jogging nan sukaga Dua sai uban aiki takeyi ta dan kallesu tace "good morning ya Aryan, good morning ya sultan" suka ansa mata fuska asake sannan suka mata sannu da aiki suka fita, sultan aransa yace why all those work Dua only, Ina Amrah fah?
Ummi tafito daga dakin da tasauka zataje ta gaishe da mijinta, nan tahadu da fatima da Dua sai aiki sukeyi, suka gaisheta ta amsa sannan tawuce zuwa gun Abba suka gaisa sannan suka dan taba hira tace masa tana zuwa, dazata koma dakin da ta sauka still Dua da fatima aiki sukeyi tace "wai Ina Amrah ce ita bazata tayaku bane naga aikin yamuku yawa?" Dua tace "tagama aikinta yanzu tawuce sama" ummi tace "aiho" Fatima tace "Ummi karya fa Dua take miki" tajuyo tace "okay fadamin gaskiyan?" Fatima tace "Ai Amrah bata taba daukan sinke da niyar aiki ba koda kuwa kan gadonta ne, Dua keyin komai na dakinsu sannan tasoko kasa nuyi na nanma tare" Ummi tajinjina maganar sannan ta girgiza kanta tayi hanyar hawa sama, aikuwa da gudu fatima taje tana cewa "Ummi dan Allah karki fadawa kowa wollah nashiga uku idan kika fada, halanma akoreni" Ummi tace "you have no problem with me karki damu" tace "okay ma thank you"
Before 10 daddy sunfita agidan sunkama hanyar wajan meeting dinsu, sauran yan gidan da basuyi breakfast ba sune suka fitoyi, mummy taga Amrah har yanzu bata fito ba kawai tayi deciding taje ta dubata,
Tana zuwa taga Amrah kwance tana kallon ceiling, Amrah kuma tayi nisane atunani, What if ya sultan ya tambaye ta Ina taje, what if in Ummi tace baza a hadasu ba, sai kuma tace zan fadawa mummy before surigani nasan No matter what mummy will surely be with me especially when it comes to backing, kawai taji an tabata ta kalla wanda ya tabata taga Ashe mummy ne, nan tayi murmushi ta tashi ta zauna sannan tace "Good morning mummy" mummy tace "morning darling" why the sudden change?, you haven't take your breakfast kuma yana yinki yanuna kamar kina da damuwa?, Nan ta fada mata duk abinda ya faru but bata bata labarin pick and obey ba, mummy tace Kinga irinsa ai you should've told me da duk hakan bai faru ba but anyway ai wannan its just a tiny thing ne so karki damu, and I guess zan turaku hutu kaduna, tace "kince mu kardai harda Dua?" Mummy tace sure saboda naga sultan da uwarsa suna yawan kallon ta so I have to send you both Kinga daganan saiku karasa hutunku, nan Amrah taringa jin dadi zata gun kakanin ta da very own antyn dinta..