CHAPTER 29

61 11 0
                                    


Yana komawa gida direct dakin shi yashiga ya kulle kofan yafada kan gado yana rufe ido ita yagani da sauri ya bude idon shi down inside him yana kara tabbatarwa kanshi itace yajawo wayanshi yayi dialing numbern Jidda kawai yayi tsaki ya jefar da wayan ya kifa kanshi ahaka har bacci ya dauki shi agun,

Dua tana karfawa a barci ta kalli agogo taga karfe Uku Saura ta tuna yau akwai islamiya kuma tun tafiyan ta kaduna bata sake bitan karatunta ba ta kalli Ayrah sai game takeyi, ta wuce toilet ta wanke fuskanta sannan tawuce dakin anty hibbah ta kwankwasa sannan tayi sallama, Anty hibbah tace "yes come in" tabude tashiga ta zauna kusa da kafan anty tace "Anty daman nace tun tafiya na kaduna na daina zuwa islamiya kuma kince zan biki so inason kafin mutafi naci gaba da zuwa ne, inje?" tace "Dua ai bazan hanaki ba but kinsan bakida lafiya kuma ai komai saida lafiya akeyi tafiyan namu kuma ai next tomorrow ne kafin nan kin gama warware wa ko?" Ta gyada mata kai anty takuma cewa "a can dinma akwai mai koyawa Ayrah karatu kinga tare zai namuku duk litattafan da kikeso shi zai miki just relax and recover okay?" Tace "toh nagode" har ranta take son zuwa amma anty tace Aa yazatayi dole ta hakura,

Tana shiga daki taga fatima ta ajiye mata abincin ta tace "Dua have your favorite" tayi murmushi takarasa gunta tayi hugging dinta tace "you're the best sister Fatima" tace "I just want you to recover kikoma Dua din dana sani" tayi murmushi kawai ta zauna akan gadon taja plate din ta daura akan cinyanta Ayrah tace "bazaki kirani ba toh sai naci" murmushi kawai ta mata Ayrah ta karaso sannan sukaci tare Dua tace "you know sometimes yadda kike magana da best friend dina nake tunawa the way you people act always" tace "yenyen you and your friend" ta harare ta ta koma gadon Amrah ta kwanta sai can tace "I must change you wollah, I'm always saying you're my best friend ashe ke kina dashi" Dua tayi dariya tace "ashe haushi kikaji toh dalla aike favorite ce" tace "ohon ki kuma yanzu" Dua tayi dariya sannan taje tafara duba kayanta wanne ne ma zata zaba,

Ya dawo daga sallahn la'asar parlour direct yayi yana shiga yaga Ammi a zaune yaje ya zauna kusa da ita yadaura kansa a shoulder dinta murya chan kasa yace "Ammi barka da warhaka" tace "amma yau lafiyan ka?" Yace "lafiya na kalau fa me kika gani?" Tace "toh ba gashi Duk kazama wani iri ba kamar bakada lafiya" yace "Ammi am fine" tace "ya jikin jiddan?" "Dasauki" tace "yaushe ne zuwan ka kadunan?" "Ammi please not now let me recover amma I promise you zanje din soon" tace "why the sudden change? Duk daukinka na zuwa ganin Dada ya ruguje is there anything I have to know?" Yace "No Ammi I have no change zuwa kuma kamar nayi I just need some break ne" yana gama fada yatashi yayi dakinsa Ammi tabisa da kallo,

Yana shiga daki yasamu wayansa na ringing yana dubawa yaga friend dinsa Ahmad ne ya daga call din yace "Hello dude" Ahmad yace "ka kyauta ai dan rainin wayo" yace "dude bazaka gane bane joke apart wollah namanta ne totally ko randa zanbar German ajikina inajin is like akwai abunda na manta amma ban tuna ba sai after flight dinmu yayi landing sannan natuna but am sorry" yace "apologize accepted" yayi dariya yace "son girmanka is getting over" yace "that's how a strong man is" yace "koba strong man ba" sukayi dariya dukkan su suna gama wayan ya kwanta trying so hard not to think,

Is like daddy is still upset with me but what I did is the right thing I guess, Ayrah da gudunta tashigo tafada jikin anty hibbah hakan yasa she broke the trail of thoughts that hibbah was having in her mind tace "Ayrah why sometimes you're behaving like teenager" tace "ummi just wanna ask you, is that so we're going with Dua?" Tace "no doubt" tayi hugging dinta tace "I love that ummi zan daina zama ciki boredom, nasamu sister ohh what a happiest day" anty hibbah tace "Ayrah go" "yanzu korata kikeyi toh shikenan natafi" Ayrah's replied tafita with frowning face , tagama making decision she will meet him tonight,

Tun daga fitowan ta daga flight zaka gane she's so excited tafara dube dube ta'ina zataga 'yan gidan su luckily sai ta hango mami da Abie da gudu taje tayi hugging mami sannan ta saketa tayi hugging Abie duk ka kallesu zakaga they're all happy suka shiga mota sai labari take basu mami tace "ohh wayaga mutanan Germany yau mun shiga uku kuma" Abie yace "tunda ma ya balle yanzu talkative tasamu topic of discussion" duk sukayi dariya Abie yace "Laaa kinga munbiye ta yarinya munyi abun kunya ko tsayawa mugaisa da teachers dinta bamuyi ba" mami tace "wollah fah gashi munyi nisa, gobe Kawai sai kaje school dinsu shikenan" Ayesha tace "mami wollah sun iya lesson kinga yadda muke pronouncing wasu abubuwan ko toh wollah ba daidai mukeyi ba" Abie yace "Allah sa duk an dauka sannan ayi amfani dasu" tace "ai Abie daga yadda nake magana ma yanzu ai nachanza" duk sukayi dariya sai can tace "Allah sarki" Mami da Abie har hada baki sukayi wajan cewa "meya faru?" Tace "Kullum sai na tuna da Dua, wlh family mummy basu sonta kuma ankaita hutu can sun hanata zuwa german" Abie yace "waye ita?" Mami tace "wannan friend dinta gifted dinnan aikasan Yarinyar she lost her mother tana tare da stepmother dinta saida tasa kowa ya daina kaunar Yarinyar" saiga Ayesha na kuka Abie yace "wasu bansan ina suke sa imanin su ba" Ayesha was obsessed to see Dua,

Da yamma Dua na dakinsu ta ciro duk litattafan da sukeyi tana dubawa tunda tayi kwana biyu bata karanta su ba tana zaune taga anbude kofar dakinsu all her thought is Ayrah amma sae taji muryan su da sauri ta daga kanta it's Mariya and Farida da gudu ta sauka tayi hugging dinsu sam ajikita sai ga hawaye yana zuba a fuskanta tace "you're welcome mum's, am happy to see you" suka karasa suka zauna akan bed dinta mariya tace "subhanallah Dua yaushe kika zama haka?, kodai ido nane farida?" Sai ga hawaye a idon Farida tace "Mariya ji yadda Dua ta koma ta lalace kamar ba'ita ba" Dua tace "sorry mum's nayi rashin lafiya ne shiyasa" Farida tace "Dua don't pretend kinsan munsan everything so don't lie to us you're not enjoying here" da sauri tace "am enjoying it fah" Kawai kallonta sukeyi yadda take son tayi pretend Mariya tace "sorry bamuzo mun dubaki ba for long" tace "gashi yanzu kunzo, I don't even expect so saboda mummy tace karku kara zuwa" sai kuma takuma cewa "am coming" kasa tayi taje ta fadawa fatima, ta tayata hada musu ruwa sannan takoma sama ta ajiye a gabansu tace "kusha ruwa please" tace barin Kira sistern daddynmu Farida tace "hibbah" kai ta gyada musu sannan tasake sauka da gudu,

Tayi knocking kofan sannan tayi sallama anty hibbah taso share mai knocking din amma tanajin muryan Dua tace "yes daughter come in" tashiga ta zauna Sannan tace "Anty ina wannan friends din Ammi na toh sune sukazo, dama time to time suna zuwa da sukayi fada ta mummy ne shine suka daina zuwa, nace ko zakizo ku gaisa suna dakin mu" anty hibbah tace "Ayyah natuna su mutanan arziki kai sunada amana wollah let's go dear" tare suka shiga dakin suka gaisa anty hibbah tace "gaskiya kun rike amana Allah saka muku da Alkhairin sa" duk suka ce "Amin" Farida tace "ai Dua yar muce muma" can Mariya tace "yanzu dan Allah kalli yadda Yarinyar nan ta koma bazaki dauke ta ba kinga bamu da right mu a kanta" tace "wancan lokacin rasuwan nan kunsan agabanku aka hanamin ita but this time around da'ita zan koma London" duk sunji dadin hakan sukayi exchanging contact da hibbah, hibbah tace "yar takuma yanzu tana da waya, wai Dua ina wayan naki nema?" Tace "yana wajan Ayrah" hibbah tace "ikon Allah" Dua ta dauki  littafin gabanta ta rubuta number su aciki sukace zasu tafi Mariya tace "yaushe ne tafiyan naku? Inyaso sai muzo sallama ko" hibbah tayi dariya tace "Ai tafiya yazo jibi ne fa" Farida tace "ashe munyi sa'an samun Dua knn, toh Allah kaimu lafiya" suka rakasu har gate sannan suka juyo,

Tana komawa daki ana kiran magrib hakan yasa tawuce toilet tayi alwala tafara sallah datazo last sujud dinta saida tayi jimawan da bata tabayi ba zuwan su mariya yakuma tuno mata da memories din da sun tuna mata lokacin da sukazo suka raka Ammi asibity lokacin da bata da wanda zai taimaka mata tayiwa Ammi addu'a sannan tayiwa Muslim ummah kafin ta idar,

Hello darln's do hit the star at the corner, follow, comment and share pls

DU'A (THE HATED GIRL) Where stories live. Discover now