CHAPTER 27

46 12 0
                                    

Tace "Anty waya ne toh nikuma mai zanyi dashi" tace "tambaya ta kikeyi ai rikewa zakiyi zai miki amfani" tace "toh" ta bude kwalin ta ciro wayan ta kunna tana kallo kawai taga picture dinta ne a wallpaper din tace "Laaa Anty kalli hoto nane fa a wallpaper" anty tace "mugani?"ta mika mata ta kalla kawai tayi murmushi tace "gashi kinyi kyau sosae a hoton" Dua tafara tunanin yaushe tayi wannan Hoton dama yana da hotonta ta tuna background din hoton rannan da suka tafi dinner party dinsu daddy ne a event center amma batasan yaushe ya mata hoton ba kawai ta sinci kanta da jin dadin hakan,

Anty hibbah ta nema abata sallaman Dua kuma ba musu aka bata sauran alluran da za'a mata ta karba ta koma dakin ta tattare gun tace wa Dua "zaki iya tafiya kuwa ko har yanzu kinajin jiri?" Tace "zan'iya nadan samu sauki ai kawae inajin jiki na so weak ne" tace "zaki daina ji shima soon" ta kamata suka fita ta tare musu mai taxi suka shiga gidan hajiya suka wuce daga asibityn,

Mai taxi yayi dropping dinsu a kofar gidan hibbah har tayi gate taga Dua still na tsaye agun tace "Ki karaso mana" taje tarike hannun ta tace "please anty mutafi karki maidani gun granny" hibbah taji tausayin ta har ranta tace  " Dua ba maidaki zanyi ba kafarki kafata dan kar yazama magana in bamu zo ba yasa zamu shiga okay?" ta gyada mata kai suka shiga cikin gidan da sallama amma sukaji shiru Dua tace "mostly ta baya ake zuwa sannan suka zagaya ta backyard din gidan sukayi sallama,

Amrah tafito da gudun ta tace "Laaa Anty kishigo mana" suka shiga har parlourn Amrah tashiga takira musu hajiya, hajiya tafito tana shan kamshi anty tace "sannu hajiya mun same ku lafiya?" Tace "lafiya" anty tace "ai jikin yarinyar ne yadanyi tsanani shiyasa baki ganni ba, yanzun ma ba sallaman ta akayi ba, nama dauka jiyan zaku lekomu" hajiya tace "banason yawan surutu please yanzu saiki sa hawan jini na ya tashi" anty "Allah baki lafiya" tace "Amin, akwai tsauran magana ne ko ko?" Tace "Aa babu" tayi mikewar ta tashige daki tabarsu agun ko kallon inda Dua take bata kalla ba balle suyi sammanin zatace mata ya jiki,

Amrah tace "Anty yaushe kikazo?" Tace "just 4 days ago" tace "Allah sarki inasu yaya da Ayrah?" Tace "Ayrah na gidan ku a abuja ai" tace "Allah sarki naso muna abuja kukazo" hibbah tace "Amrah" tace "naam anty" tace "banji kinma 'yar uwarki ya jiki ba in fact ma ko kallo bata isheki ba" tace "toh nikam bansan batada lafiya ba" tace "karya zakimin banason wannan dabi'un naki, ita kadai kike da shi amasayin 'yar uwa" tace "Nifa anty am just saying the truth" tace "naji amma ai yanzu kinsan batada lafiya ko?" Tadan juya ta galla ma Dua harara sannan tace "ya jikin?" Dua tace "da sauki thank you" Anty tace "Amrah an riga an cusa miki kiyayyan 'yar uwar ki a zuciyanki while bakusan me gobe zai haifar ba wadda ka raina Allah shi zai daga" tace "Anty I did nothing fa" tace "naji Allah kyauta mukam zamu yafi" suka tashi Amrah ma ta tashi ta rakasu har gate sannan ta juyo ta koma cikin gidan,

Anty tace wa Dua "kinga ba lafiya gareki ba zauna a kan kujeran gateman dinnan kafin taxi ya karaso tunda kakarku tamana kora da hali" tana gama magana sai sukaga mota yayi parking irfan ne yafito ya karaso yace "Anty ai daga asibityn nake naje naga bakunan nasan kuma flight dinku da yamma zai tashi nace may be kunanan" tace "Eh wollah" yana kallon Dua yace "Anty baku shiga bane?" Tace "ka ganmu anan yanzu taxi muke nema zamuje airport din mujira har lokacin tafiyan mu tayi tunda nan dai sun mana kora da hali" yace "I know za'a rina" yace kushigo nakaiku gidan mu kafin la'asar yayi" anty tace "zaki iya tashi?" Tace "Eh" ya dauke su ya biya ta joint dinda ranan yasa yawa Dua shaka sannan yasakeyi mata ordern wasu anty Maganin ya saya a ranta tace tasan za'a rina yafito yace "Anty am sorry for keeping you" tace "bakomai" ya mikawa Dua yace "your promise!" Ta karba tace "thank you",

Mama ta karbe su with two hands Zainab kuma tana ta jin dadi ankawo mata kawarta, Zainab cheers Dua up dan har tana feeling cewa at least akwai masu sonta Dua har ta sake suna ta hirar school anty hibbah tace "ikon Allah dama Dua na magana haka?" Irfan yace "I wonder too" duk maganar da'akeyi sukam hankalinsu baya kansu, tare duk gidan sukayi lunch, anty tace "yanzu zamu tafi idan mukayi sallah" irfan ya fita waje yakira Zainab a waya yace "I just need you two at garden" tace "Alright" sukaje suka samesa yace "how far Dua bazamuyi hoto bane" tayi shiru Zainab tace yea just a memories picture,

Tun a hanyarsu na zuwa airport Anty takira Aryan tace suna anjima zasu tashi tanason yazo ya dauke su idan sun iso, irfan bai barsu ba har saida yaga sun shiga sannan ya koma gida, anty suna isa tace "Allah sa yaron nan yana hanya banason zaman nan wollah" Dua tace "ai kuwa gashi chan yana tahowa" yana karasowa ya saya turus yana kallon Dua yace "Subhanallah anty kingan abinda nagani kuwa" Dua kawai tasaya kallonsa maye yayi appearing a fuskanta da har yake wannan maganan anty tace "rashin lafiya tayi shiyasa bamu zo on time ba in fact ma naje nasameta a tsume" yace "ya ilahi sorry Dua wollah bansani ba ai danazo" tace "worry not" suka shiga mota suka Kama hanyar gida ba wadda yake magana sai chan yace "wollah Dua ta chanza da yawa anty tayi baki, ta rame, kuma kana ganinta Kasan she's not on her normal self" anty tace "toh ya zamuyi Aryan Kasan halin grannyn ka ai" yace "am so much sorry Dua duk laifinane but I couldn't stopped mummy, danayi duk iyawata ganin bakije kaduna ba but now Alhamdulillah tunda Anty ta taho dake" tace ba laifinka bane",

Ayman yafito a dakinsa yace  "kai Ammi maimakon ki barni nasha bacci na wollah akwai stress sosai ajiki na" tace "toh ai saikayi kana namiji sai son jiki" yace "toh yanzu har can gidan Anty Rakiya zani dama driver kika aika" tace "kace dai bakason haduwa dasu jidda ko kuma rakiyan ba tunda kaki 'yarta" yace "kai Ammi bafa kinta nayi bafa she's still my sister kuma ina sonta, but Ammi kinsan banyi settling na aure yanzu ba" tace "wannan kuma kai kasani" yace "toh Ammi ki aiki driver mana wollah kunyarta nakeji" tace "bazan aika dinba Kasan ba masala take dashi ba and she's your supporter bata bi bayan auren hadi ba, in bazakaje ba just say" yace "na'isa Ammi never and ever zuwa gidan anty rakiya kuma it's done" yayi pecking dinta yafita,

yaje gidan Anty rakiya suka danyi hira sai yace "Anty am sorry fah akan maganar" tace "mtsww kadaina damun kanka kaji, we're all understandable so please worry not" yace "Thank you Anty" tace "ranan nafito anguwa naga abokin ka irfan  shi ya kawo ni gida wollah yaron yana da hankali" yace "haka yake ai shi" sukayi sallama ya wuce,

Sun hallara a dinning as usual suna dinner dinsu kawai sallaman hibbah sukaji duk suka juyo Ayrah da gudu tazo ta rungume Dua a jikinta suka karasa shiga parlourn anty hibbah na cewa "ke Ayrah saketa batada karfi karta fadi" kowa ya tsaya kallon yadda Dua ta change just in few days fatima housemaid dinsu har hawaye taji ya zubo na tausayin Dua, suka samu guri suka zauna Abbah yace "hibbah yanaga ta rame, batada lafiya ne?" Hibbah tace "Eh wollah" sultan yace "Dua sai kace wadda aka kaiki prison irin wannan ramewa ga baki" mummy ta hararesa, daddy yace "hibbah da izinin wa kika daukota?" Tace "kai baka gani yadda ta koma ne?, ko so kake su karasa kasheta tunda ba sonta kake ba ai" Ummi tace "Sannu Dua, Ayrah ku wuce sama ko?" Mummy saboda idon mutane tace "Ai daddy bakaga bata da lafiya ba" yayi shiru kawai, kowa yayi shiru hibbah ta wuce dakinta, ummi ma ta bita, mummy bata taba tsanar hibbah irin na yau ba kuma ta dau alwashi bashi taci,

Bayan su Ayrah sun koma daki for like some minutes sai aka bude kofar fatima ce tashigo hannun ta rike da plate takaraso gun Dua tayi hugging dinta Dua tace "I really missed you" tace "me too dear amma kin zama wani iri not as Dua I know before" tayi dariya kawai, fatima tace "surprise!, I just make this purposely for you, its your favorite" Tafada tana mika mata plate din,  ta karba tabude taga pancake ne ta aje agefe tayi hugging fatima tace "that's my sister I love you!" Tace "Allah Kara sauki good night" tana fita Ayrah ta matso tace "wollah tare zamuci whether you like it or not" tace "balle ma I like it dinba" sukayi dariya suka fara ci tare Dua duk sanda take tare da wani sai taji inama Amrah haka suke rayuwa har ranta taji tanason Zainab and now ka cousin dinta da bawani sanin juna sukayi ba amma they're like suntaso a gida daya,

After sun gama cine Ayrah tace sai Dua tabata labari Dua tace "Ayrah please kibari gobe Allah bacci nakeji" tace "Noo I just want now" suna cikin magana sukaji waya na ringing, to be sincere Dua tama manta da wani abu wai shi waya ta bude kayanta tafito da wayan taga numbern da ake Kira anyi saving da jaan Ayrah tace pick up ta daga tasa a kunnan ta tana jiran ayi magana,  duk su biyun sunyi shiru sunajin numfashin junan su Dua har tayi tunanin ko ba'ita ake nema ba tayi niyyar kashewa sai taji muryan irfan na cewa "How was your body" tace "ya irfan ina wuni" yace "nace how was your body?" tace "I'm okay now" yace "how was the trip?" Tace "Alhamdulillah" yace "okay take your medicine please ki kwanta ki huta bye" sai ya kashe wayar, Dua kuma tunda ta dau wayan kirjinta ke Duka Uku Uku bata na farko bata sababa secondly tana tsoron mummy tashigo ta kamata, Ayrah tafara dariya wai Ashe Dua nada saurayi Dua was trying to explain her out amma Ayrah sam taki sai dariya takeyi, Dua har tafara kuluwa kawai ta kwanta ta kyaleta.

Sorry for keeping you waiting

DU'A (THE HATED GIRL) Where stories live. Discover now